Gani tayi hawayen sun ida gangarowa, cikin kuka yace "so nake ki warke", hannu tasa tana share mashi hawayen fuskar shi cikin ƙarfin hali tace "to bari kuka babyna na warke kaji imaza ka daina kukan".




Haka suka riƙa cin abincin yana bata tana bashi har suka ƙoshi, ƙara taba jikinta yayi yaji zafi yace "beauty ina zuwa", ya fita da ido ta bishi tana jingina bayanta jikin gado, sallamar Dr. Aisha taji da Ammie suka shigo cikin ɗakin nan Dr. aisha ta shiga dubata wata allura tai mata sannan ta rubuta wasu magunguna Ammie ta ɗauki takadar dan taba da a siyo ta fita bayan Dr. Aisha ta gama mata bayanin ciwon Asmah.



Dr. Aisha ta kalla Asmah tace "kar ki damu zazzaɓin zai sauka ciwon kan ma zai tafi in kika samu hutu kuma kika sha magungunan da za a kawo maki sai dai if possible kar ki bari mai gidanki ya kusance ki nan kusa saboda kinji raunuka sosai a ƙalla kwana biyar in zai yu ma sati dan kisamu ki warware kafin lokacin insha Allah wannan allurar da na maki da magungunan zasu sa raunukan su warke da wuri in har ba'a fama su ba".





"To na gode Doctor insha Allah za'a kiyaye".






Abdallah ne ya shigo riƙe da roba a hanunshi, kallon shi Doctor tayi dan dama tasan shi tace "Abdallah me zakai da wannan ruwan?".





Sai da ya aje robar a ƙasa sannan yace "wanka zan ma beauty ita ma haka ta mun da banda lafiya ai".




"wanka?" gani tayi yasa ƙaramin towel a ciki ya matse yana ƙoƙarin goge ma Asmah goshi nan ta gane me yake nufi da wankan da yace murmushi tayi dan taga ana samun improvrment sosai a wajenshi fiye da yadda ta san shi a da cewa tai "to hakan na da kyau sosai ka cigaba, to Asmah Allah ya ƙara sauƙi ni zan wuce" ta faɗa maganar ta ta ƙarshe tana kallon Asmah.




"To mun gode Doctor" shima Abdallah ya maimaita abunda Asmah tace.





Doctor Aisha na fita Uwar talle ta shigo sai da tayi ma Asmah ya jiki kana ta miƙa mata magungunan da Ammie tace ta bata sannan ta fita, Asmah tasha maganain kamar yadda aka rubuta, nan Abdallah ya cigaba da matso tsumman yana goge mata fuska gani tayi yana ƙoƙarin cire mata riga da sauri ta riƙe tana faɗin,




"Ka barshi kaji zan samu sauƙi" turo baki yayi ya maƙe kafaɗa yana faɗin "a'a ya bazan bari ba ɗin nima ba haka kike mun ba inbanda lafiya".






Haka ya zare rigarta ya goge mata wuya zuwa ƙirjinta sai da ya taɓa yaji zafin ya ragu sai yazo ya mata wani tofin add'ua kamar yadda take mashi sannan ya zare rigar shi ya kwanta ya rungumeta yana faɗin "beauty kiyi bacci kinji kina tashi zazzaɓin zai sauka".




Dariya tai tana tuna duk yadda take mashi ne, haka sukai bacci, Asmah daɗinta ɗaƴa Auntyn yara bata nan ake wannan dramar ta tafi asibiti.


Sai da aka kira la'asar suka tashi, ba laifi Asmah ta ɗan ji ƙarfin jikinta sosai, tasa Abdallah tayi bayi ta koya mashi yadda zai yi wankan tsarki bayan ya tsabtace jikinshi suka ɗauro alwallah suka fito suka tada sallah Asmah taja sallar kamar yadda suka saba.






🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚





*BAYAN KWANA BIYU*





Abbah yayo kiran Asmah tana isa falon shi ta tarar da Lawyern Abbah da archtect da waenda zata ba kwangila haka suka zauna suna tattaunawa inda Abbah yaji Asmah ba tayi dai dai ba sai ya gyara mata yanzu an riga an samo waenda zasu yi aikin a gonar har sun fara gyara gona kasancewar damina ta matso, iri kuma duk an siya an aje duk yadda abun zai tafi da kuma yadda za'a shigo da engines ɗin duk ba abunda basu tattauna ba sai dai fatan alkhairi a sana'ar Asmah.





ZAN SOKA A HAKANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ