"Baby na dan Allah kayi haƙuri ni na jamaka wannan wahalar bansan haka abun zai kasance ba, ka gafarce ni nan da kwana uku zan zama mai tsarki sai in faranta maka rai dan Allah kai shiru ka daina kuka".

Can cikin wata rikitacciyar murya taji yana faɗin "Asmah ki taimaka mun in kika hana ni wannan wasan da nake dake zan iya mutuwa, ki buɗe mun ƙofa dan Allah" yana ƙara fashewa da kuka.

Itama kukan ta ƙara saki tace "kayi haƙuri bazan iya buɗe maka ƙofa ba har sai ka dawo hayyacinka".

Wata ƙara taji yana saki da ƙarfi, ta saƙon ƙofa ta leƙa taganshi ya nata birgima, da sauri taje ta buɗa wadrove ɗinshi wata jallabiya tashi ta zura da sauri, ta buɗa ƙofar ganinshi tayi kwance yana mirgina yana riƙe marar shi, tsugunnawa tayi gefen kanshi tace "yayana mai ya faru nice ko, ka yafe mun" da sauri ta isa ta ɗauko mashi maganinshi tazo ta bashi, sannan ta tallafo kanshi tana tofa mashi addu'oi, ƙanƙameta yayi sosai yana fitar da lumfashi sama sama, a haka ta cigaba da mai addu'a har yayi bacci.

A hankali take kallonshi yana bata tausayi, kwance yake lamo a kan
ƙirjinta yana bacci yana sakin ajiyar zuciya, ya ƙanƙameta kamar ana shirin ƙwace mashi ita, duk yadda Asmah tayi dan ta zare jikinta ta kasa, kuma ba yadda za'ai ta iya kaishi gado dole suka shingiɗa anan a haka har bacci ya kwasheta itama.


Can cikin bacci ta rinƙa jin kamar surutu ta buɗa idonta ji tai Abdallah na faɗin "babyna dan Allah ki buɗe mun ƙofar muyi wasa", fuskarshi ta haska da wayarta taga yayi zufa sharkaf sai ƙare matseta yake a jikin shi, yana cigaba da sumbatunshi, hular kanta ta cire tana goge mashi zufar da yayi, kissing ɗinshi tayi a goshi tana ƙara riƙe shi tace "ya haƙuri babyna kaji kar kayi fushi dani dan Allah".

Tun kiran fari na asuba Asmah ta buɗe idonta ta sauke su tar a kan fuskar Abdallah, domin haske ya fara shigowa falon, ji tayi bayanta da wuyanta sun riƙe saboda yadda ta kwanta ga Abdallah duk ya sauke mata nauyinshi a jikinta, da ƙyar ta fara motsa jikinta dan ta zame Abdallah daga kanta, gani tayi ya buɗa idanunshi a hankali kanta tsayawa sukai suna kallon ƙuda can kuma Abdallah ya janye idon shi yana tsaki ya tashi zaune yana juya mata baya, hankalin Asmah a tashe dan tasan ba ƙaramin abu bane yake sa Abdallah tsaki tasan yau ya kai ƙololuwa, da sauri ta dafa kafaɗar shi cikin sanyin murya tace,

"Babyna mai ya faru?".

Bai jiyo ya kalleta ba ya ƙara tsaki yana ƙara juya kai yau Asmah kam tasan ta taro match ɗin da ba gola, tasowa tayi ta dawo ta gabanshi, sai dai tun kafin ta tsugunna taga yayi wuf ya tashi ya koma kan kujera ya kwanta rigingine yana kallon silin yana ta ƙwafa shi ka ɗai.

Bakin kujerar tasa gwiwowinta a ƙasa tace "dan Allah ka faɗa mun laifina gare ka domin nayi saurin roƙar yafiya da gyarawa tare da saka farin ciki rabin rai na", ta faɗa cike da mamkin me ta mashi dan basu taɓa samun saɓani ba tunda suka yi aure sai yau.

Sai da ta daɗe tana mai magiyar ya faɗa mata laifinta har sai da ta fashe da kuka, Abdallah ko bai jurar kukanta da sauri ya jawota jikinshi, itako ta kwanta luf a jikinshi tana shesheƙar kuka shi kuma yana shafa mata baya alamar rarrashi.

Ji tayi yace "me yasa kika hana ni wasa dake?" mamaki ne ya kama Asmah dan Abdallah bai cika tuna abubuwa ba amman ya akai wannan bai manta ba.

Ɗago jajayan idanunta tayi tace "babyna yau baza ka sharemun hawaye ba, ba kai kace baka son ganin......" bata ƙarasa ba saboda jin harshen Abdallah yana share mata hawaye yana ajiyar zuciya, wani yanayi ta tsinci kanta wanda ta kasa tantance a wacce duniyar take domin yadda Abdallah ke wasa da harshensa a dukkan fuskarta zuwa bakinta sai dai bata bari ya shiga cikin bakinta ba saboda bacci ta tashi, sun shagala sosai can ganin sallar asuba zata wuce bai ba Asmah tai saurin cewa,

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now