Yadda yai maganar yasa mata mugun tausayinsa a zuciya, "kar ka damu ya Abdallah kaji, lokaci kaɗan ya rage sai ka gaji da kallo na ma".


Ba duka abunda ta faɗa ya gane ba, dan haka ya amsa ma wanda ya gane "bazan taɓa gajiya da kallonki ba".

"Nima".

"To yanzu dai kar ki tafi har sai na gama shan cofee ɗin".

"To" haka ya ɗauki cofeen yana sha yana kallonta tare da shaƙar ƙamshinta da ya baɗe ɗakin yana murmushi.





☘  ☘  ☘  ☘  ☘  ☘


*BAYAN KWANA BIYU* 

Ammie ta dawo lafiya sai dai ita kaɗai ta dawo, Aunty Nana ko da ƙawarta suna can kayan za su biyo, Ammie ta dawo dan ta cigaba da hidima, gida duk ya ƙara cika kasancewar gobe ne za'a fara biki (event), Aunty Nafi tazo ta kwashe Amarya da ƴan matanta ta kaisu gidanta, dan da Ammie tace a barta a nan amman Aunty nafy ta nuna tana so ace ita ta bada hannun Asmah dan haka Ammie tai mata uzuri.


Yau talata tun da safe Ammie ta turo wata mata mai Beauty Saloon wacce take masu Ammie gyaran kai, ita tazo dan tayi ma Amaren gyaran kai da ƙunshi amman Ammie ta tabbatar mata Amarya na musan man zatayi mata, sadda matar ta iso gidan Aunty Nafy dai dai Shuwa ta gama aikinta ta tattara ta koma can gidan Ammie sai kuma da yanma ta kuma dawowa dan tayi mata na yanma dama haka take yi.



Bayan tafiyar shuwa matar ta fara da Asmah aka gyara mata kai sosai sai dai ba'asa mata relaxer ba saboda tace bata so Ammie ma tace kar tasa ma kanta relaxer tunda bata taɓa sawa ba kuma gashinta nada kyau, an gyarashi gwanin ban sha'awa ya sha mai ya kwanta baya sai fitar da wani fitinan nan ƙamshi yake, dan dama can shuwa na gyara mata shi da sinadarai na kai masu ƙamshi wanda basa cutarwa, kowa sai maganar gashin yake, sannan aka fara tsara mata ƙunshinta wanda aka shafa mata muhallabiya kafin a fara, tun anayi su Zarah ke ta yaba kyanshi har aka gama, (kai ni kaina nace gaskiya ƙunshin nan ya fitunu, yanzu ta fara fitowa amarya).


An yi masu Zarah suma sai dai bai kai na uwar gayya ba, tuni sukai wanka suka fara shirin ƙauywa day da za suyi karfe 4:00pm.

Mimi ce ta ɗauki wayar ta, ta buga ma Ammie waya sai dai ta kira yafi sau uku bata ɗauka ba, tace "Nasan yanzu tana can ta saki wayar tana ta hidimar gabanta, dama haka Ammie take akwaita da ruɗu in tana hidima" sai ta kira Aunty Shaila bayan ta ɗauka tace "Hello Aunty shaila tun ɗazun fa muna jiran make up artist ɗin nan amman bata iso ba".


Aunty shaila tace "kinga Mimi yanzu ma ta iso zamu taho tare dan Ammi tace nizan shiryama Amarya, da Aunty Nana zata shirya mata to yanzu kuma ta shiga busy nan wajen, dan haka zan taho da ita yanzu, sannan maganar inda za kuyi naji kamar Ammie na cewa hall za'a kama maku, dan wedding planners ɗin sunzo decouratung ɗin garden sai dai suka ce ba zaiyi ba saboda gyaran da ake a ɓangaren ya Abdallah har ya shiga garden ɗin sabida suna ƙara ma part ɗin girma kama daga garden ɗin suke ɗauka, Uhmmmm Mimi bari dai na kai maki Ammie kuyi magana dan bansan ya ake ciki ba an samu ko a'a".

"To Aunty Shaila".

Jim kaɗan Mimi ta juyo muryar Ammie, bayan sun gaisa ta tambaye ta maganar hall ɗin fa, nan Ammie ta mata bayanin wai weeding planners ɗin sun samu inda za'ai har sun fara decourating ɗin wajen, su dai su shirya zasu zo nan in sun gama su ɗauke su.

Mimi tace "to Ammie za dai kuzo ko?".

Ammie tai dariya tace "lallai Mimi abun ƴan matan za muje da girman mu rufa mana asiri, su Hauwa'u da Shaila dai na nan zuwa dan a sa maku manya dan abun ya tai da kyau".

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now