Mimi tace "to da Allah yanzu dai a bar maganar nan aside naga tana so ta kawo tashin tashina abun ya wuce wasa tunda har da iyaye, a canza magana plz".


"Hmmm Mimi kenan na san baki san inda maganata ta dosa ba shi yasa kika ce haka, to yanzu magana shine Asmah ki daina kuka kamar yadda Mimi ta faɗa taimakon da za muyi mashi muyi mai addu'a dan ita yafi buƙata, nasan dole abun yai ta baki mamaki, kamar yadda nima zai zame mun babban abun mamaki a zuciyata a duk duniyar nan, ba yadda za'ai mu canza abunda ya faru sai dai wanda bai faru ba, dama kince kinyi istihara kinga kin saka Allah a lamarinki, to duk abunda ya tafi ba dai dai ba dama can ba alkhairi bane a gare ki, dan haka sai ki gode ma Allah da yasa kika gano cutuwarki ta nan gaba tun wuri kinga sai kiyi maganinta".



Asmaga ta rungume Zarah tana faɗin "Zarah kinyi a rayuwa ba kowa bane zai iya samun ki a matsayin ƙawa ba, duk kuma wanda ya sameki kuma ya more, Allah na gode maka daka haɗa ni da wannan baiwar taka, Allah na gode, banda kamarku ƙawaye na" ta faɗa tare da jawo Mimi itama ta haɗa su duka ta rungume su, sun daɗe a haka suna ma Allah godiyar haɗa su da yayi.




Zarah ta fara zare jiki tare da faɗin "to kun manta muna kan mission ne, tunda ya Aliyu ya faɗi ai sai mu cigaba dan gano winner ko?".


Duka suka bita da idanu sun san kawai tana maganar ne badan tana so ba, tare da jinjina mata.


Zarah ta kalle su duka tace "common gals stop being pity, am all right".

"Allah sa haka" suka faɗa.

Jin tace "ameen" yasa suka son ba wai ta faɗa gaskiya bane she's not alright.

Zarah tai masu yaƙe tare da miƙa ma Asmah waya tace "ki kira ya Marwan"

Asmah ta amsa wayar tace bari dai na tura mashi test, suka ce to, ta tura test kar haka:


_Asalam_
_Barka da warhaka ya Marwan, ya kake ya karatunka fatan komai lafiya, kayi haƙurin rashin amsa ma da banyi ba da wuri, kayi haƙuri kuma dajin amsar da zan baka domin nasan ba ita ka so jiba, banda yadda zanyi ne ya Marwan ina da wani a zuciyata kuma bazan iya yaudara ko saɓa alƙawari ba ya marwan kayi nauyin baki a abunda bai kamata kayi ba, kayi haƙuri in maganga nu na sun ɓata maka rai, ka huta lafiya._
Daga ƙanwarka
ASMA'U.



Tayi sending sun jira amman ba reply suka ce ila bai kusa ne ya gani daga baya, Zarah ta tashi tare da cewa

"To ni dai bari nazo na wuce gida nasan za ku iya handling sauran, za muyi waya kunji".

Duk yadda suka so ta tsaya a ci abincin rana taƙi, dole suka haƙura suka barta ta tafin, har gaban mota suka rakata suna ƙara tausarta akan lamarin, sai da tayi masu alƙawarin ba zata gaya ma su Mami akan batun ya Aliyu ba sannan suka barta ta tafi.



*6:30pm*

Asmah ta tashi daga sallaya bayan ta gama sallar isha'i, Mimi bayan ta gama ta kalli Asmah tace saura ya Abdallah kije yanzu ki mai, karo na farko da Asmah ta tsinci kanta cikin farin ciki marar misaltuwa dajin sunan ya Abdallah ko me yasa, ɗaga ma Mimi kai kawai tai ta nufi kitchen ta haɗa mai cofee ta yanka mashi fruits sannan ta ɗauki farfesun kayan cikin da suka dafa ita da Mimi ta wuce ɓangarensa.


Sai data bari ya kammala cin abincinsa bayan ta kwashe kwanukan ta dawo ta mashi kallo cikin ido shima ya mayar mata, sun ɗauki tsawon mintuna goma suna aika wa juna saƙonni ta ido, Asmah ta yanke kallon sai da ta gyara murya sannan tace


"Ya Abdallah ina son iɓ gaya maka wata magana, kasan nan ba gidan mu bane ko? kuma ni mai aikinka ce ko? to lokaci yayi dazan koma garinmu, can ƙauyen mu domin za'ayi mun aure ne kaga dole na bar nan gida kuma na bar yi maka aiki, na gode da duk karamcinka a tsawon lokacinan, ka yafe mun in na maka abunda baka so, zan tafi yanzu zan fita daga nan, kuma in na fita yanzu baza ka ƙara ganina ba har abada" ta faɗa tare da juyawa tana fara fita daga ɗakin.



ZAN SOKA A HAKAOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz