wannan mafarkin ne ya dawo mata tas a ƙwaƙwalwarta, cewa tayi

"Wata ɗaya kafin inzo gidan nan nayi mafarkin nan" tsayawa tayi kaɗan tana faɗin "to meye amsar wannan? meye saƙon dake ciki?" 


Take zuciyar ta tace "ki tuna labarin Abdallah da Mimi ta baki"

Wage idanu tayi cikin mamakin gano amsar
a fili take faɗin "da zuwanki wata ɗaya dai dai kenan da faruwar hatsarin ya Abdallah" haka ta faɗa kamar yadda Mimi ta gaya mata sadda ta gama bata labarin, wasu zafaffun haweye ne suka gangaro a kan kuncinta a fili ta ƙara faɗin

"wata ɗaya da yin mafarki, wata ɗaya da hatsarin ya Abdallah, inna fahimci saƙon mafarkin yana nufin kenan ila ranar da abun ya faru nayi mafarkin tunda da dare ne duk abubuwan suka faru, kenan saƙon dake ciki ya Abdallah yana neman a taimaka masa a ranar, to MEKE FARUWA ne, ruhinshi da ruhina suna haɗuwa ne in munyi bacci ko yayane, to wannan wani irin abune yake faruwa dani ba shakka wannan shine saƙon mafarkin ban taɓa jin kallar wannan abu ya taɓa faruwa ba ko a film ko a littafi sai a kaina?"

Sai da ta nisa kana tace " Ya Abdallah kayi haƙuri ka nemi taimako na a lokacin da ban gane yaranka na mafarki, kuma banda ƙarfin taimakonka a lokacin"

Hannu tasa a kai tana faɗin "sai wane mafarkin kuma nake tunanin akwai saƙo a ciki?".

########

_Asmah kar ki cuce ni, da ina ta maki magiyar kizo gareni don ki taimakeni sai kuma da kika zo kike son juya mun baya? miyasa?"__ 

_Wallah bangane me kake nufi ba? waye kai? me kake son na taimaka maka dashi? wane irin juya baya ne kake gudun in maka? kuma yaushe nazo gareka? nifa bansan ka ba! ban tab'a ganin kaba! dan Allah kabar yaudarata kana sani tunani kullum, in kana son nasan da kai ka bayyanar mun da kanka! in kuma Aljani ne kai ka taimaka ka rabu dani kar ka cutar dani dan giman Allah!_

_hmmmm, Asmah kenan ni mutum ne kamar ki, kuma kar ki tab'a kawowa zan iya cutar ki, domin ina matuk'ar k'aunar ki, kuma duk tambayoyin da kika mun amsar su na gare ki!_

_taya zakace amsar su na gareni, bansan komai ba kar ka rikita mun k'wak'wallwa._

_kiyi tunani ku........._

"Wannan kuma yana nufi na iso gareshi, tabbas da gaskiya ya Abdallah duk amsoshhin tambayoyina na gareni, yanzu na gane bari muga na farko na san ka kaine ya Abdalllah, na gane maganar nazo gareka kusa kusa ma kuwa, maganar ban taɓa ganinka ba bai ma taso ba, nace in kana son in san da kai ka bayyanar mun da kanka, kuma ka bayyanar mun da kanka, kuma kai ba aljani bane, sai dai abunda har yanzu na gaza ganewa shine juya bayan da kake cewa zan maka?, cutar war da kake cewa zan maka?" wani nazari ta ƙarayi sannan ta cigaba

" Ya Abdallah haƙika wannan shine so daga Allah, son tsakani da Allah domin yazo a cikin hadisin SAHIHUl BUKHARI cewa

*"THE PROPHET MUHAMMAD (SALLAL LAHI ALIHI WA SALLAM) SAID: THE SOULS ARE LIKE AN ARMY JOINED IN THE WORLD OF SPRITS, WHICEVER SOULS KNEW EACH OTHER IN THAT WORLD ARE ATTRACTED TOWARDS EACH OTHER IN THIS WORLD AND WHICH EVER REMAINED DISTANT AND INDIFFERNT THEY ARE DISINTRESTED TOWARDS EACH OTHER IN DIX WORLD.*
        SAHIHI AL-BUKHARI.

*ANNABI MUHAMMAD TSIRA GA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI YANA CEWA: HAƘIƘA DUKKAN RUHINAN MUTANE SUNA HAƊE NE A CIKIN DUNIYAR RUHIKA, DUK RUHINAN DA SUKA SAN JUNA KUMA SUKE SON JUNA A WACCAN DUNIYAR TO BA SHAKKA A WANNAN DUNIYAR MA HAKAN ZATA KASANCE, HAKA KUMA WANDA BASA SHIRI KUMA BASU SAN JUNANSU A WACCAN DUNIYA TO HAƘIKA HAKA ZASU ZAMO A WANNAN DUNIYAR.*
          SAHIHUL BUKHARI.


"Kenan son gaskiya shine wanda ruhinku ma suna son junansu ikon Allah, na gode ma Allah ni Asmah na gano wanda ke mun kallar wannan son, ya Abdallah ka yafe mun nayi kuskure *ZAN SOKA A HAKA* zan kuma aure ka koda yana cikin ƙaddararka ba zaka taɓa warkewa ba wallahi *ZAN SOKA A HAKA*  har ƙarshen rayuwata, ya Abdallah na ka yafe mun, infact ni ban maga aibunka ba wallahi, na yadda zan aure ka, zan zama matarka mai ɗeba maka damuwarka, uwar ƴaƴanka, mai son farin cikin ka har ƙarshen rayuwata, wannan shi ake kira da ƙaddarar Allah, its called destined, its called fated ohhh Allah his my soul mate, Allah na gode maka na gano masoyin ruhi na" ta faɗa tana sakin kuka mai tsuma zuciya.

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now