"To gata kin ko cu sa'a da ƴan sauran kuɗi a ciki"
ta faɗa tare da miƙa mata wayar.

Amsa Asmah tayi tace    " To na gode" ita kuma Aunty Nafy ta shige ciki, Ammie na faɗin maraba maraba da manyan baƙi.

Ita ko Asmah guri ta samu ta zauna, number ya Marwan ta fara kira sai dai har tagama rurinta ta katse bai ɗaga ba tace "inaga bai kusa ne bari na kira ya Khaleel" tayi dialing number shi bugu ɗaya biyu ya kama, sun gaisa sosai yana tambayar ta ya karatunta, tana amsa mai da komai lafiya shima ya na shi karatun, bayan sun gama gaisawa suka yanke wayar, kashewarsu keda wuya kira ya shigo, har zata miƙe kai ma Aunty Nafi ganin ya Marwan ne ya sata komawa zaune ta ɗaga da sauri tana faɗin,

"Asalamu alaikum ya Marwan"

Take ya ɗau murya ya amsa da "wa alaikumu salam gimbiya"

Dariya tai tace " wannan suna dai ya bini"

Shima dariyar yai yace "ba gaisuwa?"

"Au ina wuni Yaya"

"sai dana roƙa maida abunki banso"

"Kai ya Marwan halinka baya canjawa"

"Har sai sadda naki ya canja"

"To ni nawa bai canjawa"

"Haka nawa nima"

Dariya suka kwashe da ita gaba ɗayan su.

Shiru ne ya ɗan wanzu na sakwanni can Asmah ta katse shirun da faɗin
"To ya Marwan ya makaranta ya karatu ya kake? fatan ba ko dai wata matsala ko?"

"To duk ni waennan tambayoyin a tare ai sun mun yawa, to bari na gwada amsawa ɗaya bayan ɗaya makaranta lafiya lau, karatu Alhamdulliah kullum
daɗa wahala yake, ni kuma bana lafiya, kuma ina da matsala da fatan na amsa maki ko wacce ?"

"Ay amman ban gamsu da amsoshi biyu da ka bani ba"

"wacce da wacce kenan?"

"Ta ɗaya kace baka cikin ƙoshin lafiya meyasa?, ta biyu kace kana da matsala wace iri?"

"Well Ay haka nace sabida hakan take, kuma duk matsalar da nake da itan da kuma rashin lafiyar tawa duk tana da alaƙa dake ne"

Zaro iɗo tai ta dafe ƙirji tana nuna kanta kamar yana kallonta kana tace
" Ni? ya Marwan?"

"Ay"

"To saika faɗa mun taya"

"Yanzu kuwa tunda kin buƙaci kiji"

"To inaji"

Sai da yaɗanyi shiru na sakon biyar can kuma cikin muryar roƙo yake faɗin " ASMA'U? ASMAU?"

A hankali Asmah tace "Na'am ya Marwan"

Ya cigaba " Na daɗe ina son in faɗa maki abu mai mahimmanci da yake addabar birnin zuciyata, yake ɗawainiya da zuciyata tun lokacin dana fara saka idona a naki, a lokacin naji kada ƙarancin shekaru yasa kima abun mummunar fahimta shiyasa ban gaya maki ba na ci gaba da rainon abun a zuciyata duk da ba ƙaramar wahala na sha ba, amman yanzu nasan kinyi girman da duk abunda kunnuwanki zasu jiye maki zasu iya gane ma'anarsu, kuma kin kai girman da zaki iya aje  kallar wannan maganar a zuciyar ki, dan haka zan fayyace maki sirrin zuciyata yau tunda kin buƙaci ki sani" jinta shiru yasa shi cewa "Asmah kina jina?"

Asmah ko da tunda ya fara maganar ta natsu tana sauraren shi amman bata gano inda ya dosa ba duk da zuciyarta tayi wani wajen sai dai ta ƙaryata zuciyar ta da faɗin ya Marwan ne fa, Yayana, ko dai zolayar shine da ya saba ta tashi, sai dai yadda yake maganar dagaske yake yi, cikin shagwaba da rashin fahimtar inda maganarsa ta dosa tace " Yaaaa marwaaaaan"

Yadda ta faɗi sunan nashi ya ƙara sawa zuciyar shi narkewa, ya cigaba " Asma'u ina sonki so na tsakani ga Allah, sonda bana iya tunanin akwai wanda zai maki kallar sa a doran ƙasan nan, na daɗe ina tarairayar sonki a zuciyata duk da kullum barazanar fasowa yake, Asmah ki amince mun kizama uwar yayana, mafarki na naki ne ke ɗaya, Asmah bana kula wata ƴa mace sabida sanku da ya mamaye dukkan gurbin da filayen da ke cikin zuciyata, Asmah ke kaɗai nama tanadin zaciyata,  dan Allah ki rungumi soyayyata in ba haka ba zan faɗa wani mawuyacin halin da ba mai iya tsamoni sai ke Asmah, ki tausaya mun Asmah kar kice A'A dan kalmar nan kaɗai zata iya ruguza mun zuciya"

Asmah kam da ruwan hawayen dake zubowa daga kwarmin idanunta yamata kaca kaca da fuska tunda Marwan ya fara magana.

"Asmah yanaji kinyi shiru?"

Kukan kawai ta cigaba a ranta tace " Ya Marwan a bari ya huce shi ke kawo rabon wani"
tun tana kukan marar sauti har ta koma mai sauti, daga ɗayan ɓangaren yana jiyo shesheƙar kukanta, yace "Asmah kuka kike yi? Sabidami? Ko magana tace ta ɓata maki rai? Ya haƙuri, kimun alfarma ɗaya kiyi tunani akan maganar sai ki faɗa mun  amsar daga baya nasan dole hakan ta faru tunda kinji maganar da bakiyi zato ba, ina zaman jiran jin alkhairi daga bakinki gimbiya, kuma ki daina kuka dan Allah ban faɗa ba da niyar saki kuka, kuma a ganina ba abun kuka a abunda na faɗa, dan haka ki share hawayenki dan Allah"

Itako ta cigaba da kukanta, duk ta gane shima kukan yake daga yadda yake magana, ita tausayi ma ya bata, duk yadda yaso tayi magana amman abun ya faskara dole ya haƙura yace zai ji amsar shi daga bakinta, sannan yace "ki huta lafiya gimbiya" dut dut ya yanke wayar, sai lokacin Asmah ta zare wayar daga kunnenta, sai da ta gama shan kukanta wanda har tazo ta ma rasa dalilin yin kukan nata, sai da ta saita fuskarta sannan ta fito suka ko ci karo da Aunty Nafi, sai dai taga fuskar Aunty Nafyn ta canja ba kamar yadda ta shiga ba, hannu Aunty Nafy tasa taja Asmah suka fita harabar gidan sai da suka kusa gate sannan aunty Nafy ta tsaya tare da cewa "...........




A/N

To makaranta nasan kuna da tambayoyi da yawa akan page ɗinnan, amman kar ku damu komai zai warware muje zuwa, sai gobe in Allah ya kaimu za kuji next page.

Fiamanillah (na barku cikin amincin Allah)
👸🏼Queen bk👸🏼

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now