****   ******   ***********

Gagarumin biki ne akayi tsakanin Alhj. Muhammad Zayyan da Haj. Amina sulaiman Soro, ba k'aramin shagali akai ba, biki ne na atara dangi a basu labari, bayan an gama aka kai amarya gidan angonta kano a sharad'a, gidan da ya fara ginawa, d'an k'aramin gida ne dai dai zamansu, rayuwa suke cikin tsabta da girmama juna baka jin kansu, a hankali da taimakon Allah Alh. Muhammad ya ta samun albarkar dukiya, domin kullum kasuwancinshi bunk'asa yake, shekararsu guda da aure Allah ya uxurta tasu da samun k'aruwa, Haj.Amina ta haifo d'an ta namiji kyakkyawa, suka samashi Abdallah, Abdallah ya taso cikin gata, so da kulawa fiye da yadda kuke zato, iyayen suka d'auki son duniyan nan suka aza akan d'an nan, haka ma y'an uwa duk inda ya shiga kamar a lashe shi don so, in ta k'aicemaku yaron akwai farin jini, sai da sukayi da gaske sannan suka rik'a d'an nasu, don da yaje hutu ko can Mai duguri ko nan Kano dai su nemi su rik'e shi, sai iyan nashi sun fidda kunya sun nuna masu sufa sam basu yadda ba, kana suke hak'ura, bayan shekara ukku suka haifa mace suka sa mata Urwa, a lokanci Alh.Muhammad ya bunk'asa don yazama shaharrarn mai kud'i, ba k'aramin jida Naira yake ba, shekarar urwa d'aya Alh. Muhammad ya auro Shafa'atu, tunda Allah ya tsaga da rabon aurensu, farko haj. Amina tayi kishi amman daga baya sai ta sassauto ganin yadda shafa'tu ke sonta da y'ay'anta, tana matuk'ar son yaran har sun saba da ita, kuma son tsakani ga Allah take masu, kuma dama ance in kana son kasamu son uwa to kaso y'ay'anta, yakasance ma duk ran girkin Amina a b'angaren shafa'atu suke kwana, yaran ma suna sonta to hakan ne yasa taci auntyn yara, ganin haka yasa Haj. Amina sakewa da ita sosai, suna zaune lafiya da junansu, suka d'auki kansu kamar ya da k'anwa, sam bakajin kansu sai dai abunda ba'a rasa ba tunda zaman tare ya gaji haka, hakan kuwa ba k'aramin dad'i yama Alh. Muhammad Zayyan ba, to hankulan mutanen gidan ya kwanta sai suka zage sukaita zuba y'ay'a, y'ar haj. Shafa'atu ta farko mace aka samata Hibbah, sai ta biyu Hauwa'u wadda suke sa'anni da Shaila y'ar wajen Haj. Amina, daga nan auntyn yara ta haiho yasmeen a lokacin Ammie bata haihu ba, sai bayan shekara biyu ta haifi Bilkisu ( Mimi), bayan wata ukku kuma auntyn yara ta haifo Nihal, ya kasance Abdallah ne kad'ai d'a namiji a gidan, kuma ya saba da Abbah sosai, shiyasa kullum suna tare duk in da zashi Abdallah, komai nashi Abdallah, nikam nace kodan shi kad'ai ne namiji shi yasa yafi nuna yafi nan nan dashi ne oho, yana matuk'ar son y'ay'an nashi, ya basu ilimi boko da arabi ga tsantsan tarbiya, Abdallah an rasa halin wa ya d'auko dan shi kwata kwata magana ba ta damai ba, amman a idon bak'unta, in bai sanka ba to bazakaji surutunshi ba, amman in kuka saba ya sanka to za kaji surutun sa, gashi da tsabta uwa uba wata muguwar natsuwa da yake da ita, wanda ganinka na farko dashi zaka fuskanta haka, sun taso tun suna k'anana shida Mahmud d'an wajen aunty uwani tare, da yake wajen lokaci guda aka haife su, kuma anan gidan hajiyar kano wato mahaifiyar su Abbah aka yaye su, daga nan shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanin su, da k'yar aka rabasu, suna ko gama primary iyayen nasu suka yanke hukuncin kaisu makarantar secoundary d'aya, London sukayi makarantar MACMILLIAN SECOUNDARY SCHOOL, bayan sun gama su kadawo gida Nigeria, don duk ra'ayin su na karatu yazo d'aya, dukkansu suna son su zama sojojin ruwa ne, don haka suka wuce makarantar sojoji don cinma burikansu.



Sauran k'annan Abdallah kuwa suna gama secoundary Abbah yake aurar dasu, a cewarsa mace na gama secoundary school zai mata aure alabashi in tayi auren shi zai biya mata ta cigaba da karatu har son ranta, kuma dukansu sai sun sauke k'ura'ani a hadda kafin su shiga senior class, kuma sai ya kaisu d'akin Allah kamin ya kaisu na miji, Urwa ta auri mijinta shima d'an kasuwa ne amman akwai ilimin boko sosai na addini kam malami ne, da auranta ta karanci SHARI'A LAW, yanzu haka ita cikakkar Lawyer ce mai zaman kanta, y'ay'anta biyar, ASWAD, MAHEER, NABILA, FATIMA sai BILAL.

Hibbah ma tayi aure, mijinta likita ne yanzu y'ay'ansu uku, MINAL, AKRAM sai SAUDAT.

Shaila da Hauwa'u a tare sukayi aure yanzu suna da y'ay'a d'add'aya, Hauwa'u tana da Fudhal d'inta, a yayainda shaila take da Zaitoona, to iyakar waenda sukayi aure kenan a y'ay'an Alh. Muhammad Zayyan, wannan kenan.







Su Abdallah da Khalil an gama karatu cikin sa'a, bayan an gama k'addamar dasu a matsayin sodojin ruwa (Navy), gida ma ba k'aramar liyafa aka shirya masu ba, bayan an ci an sha anyi bidiri an watse, Abbah ya masu kyautar filaye don su fara gininsu, banda plazas supermarkets da gidajen mai da ya basu akan suyi jari dasu su cigaba da kasuwansu, sannan yace su fito da mata suyi aure, da yake bakinsu d'aya sai suka ce su ai yara ne basu isa aure ba, Abbah rik'e baki yayi yana mamakin wai mai shekara 25 ne yake cema kansa yaro, in haka ne kenan su sadda suke aure jarirai suke, nan ya masu tatas tare da cewa duk wanda bai fito da mata ba a cikinsu dakansa zai mai matar, kullum cikin tuna masu yake, kuma su a zahirin gaskiya basu shirya ma auren bane, kuma ma basu da wadda suke so, har gwanda Khalil yana budurwowi shidai bai da ra'ayin aure yanzu ne kawai, shi ko gogan kwata kwata mata ma basu a gabanshi a lokacin, kullum dai da ya bijiro masu da maganar sai sui ta mai kwana kwana, ana haka har aka masu posting d'insu na first mission d'insu, ba k'aramin jin d'ad'i sukai ba domin wannan ne karo na farko za su fita aiki ba training ba, kuma ki ba komai Abbah zai daina damunsu suyi aure, murna a wajensu kar ku tona haka ma iyayen su, ranar nata matsowa su kuma sai shiri suke, duk sunje bankwana wajen y'an uwa da abokan arzik'i kasancewar basu san iya tsawon lokacin da zasu d'auka ba, don har yanzu bama agaya masu mission d'insu ba da garuruwan dazasu, haka sukajje kowa sai albarka yake sa masu da fatan samun nasara, ranar tafiya suka fito cikin shirinsu na fararen uniform d'insu wanda yake masu kyau abun sai kun gani, jirgi za su hau suje can abuja head quarter su, inda rundunar zata taru kamin a rarraba masu missions d'insu da kuma garuruwa, har airport suka rakasu, sai da jirginsu ya d'aga Abuja birnin tarayya kana suka jiyo bayan sun masu addu'oi.








wash nagaji, sai gobe insha Allah page biyu zan maku in Allah ya bani iko, muje zuwa.






*THERE ARE MORE GOODS BOUGHT BY THE HEART THAN BY THE HEAD.*

👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now