The Phone Call

9.8K 746 2
                                    

Bayan sati daya da dawowar mu daga asibiti, Sultan ya fara saukowa daga emotional height din da ya hau, ya fara accepting Takawa a hankali. A nasa bangaraen kuwa, Takawa kullum sai yazo part din mu, tun ina jin nauyinsa ina baya baya dashi har na saba na fara yi masa surutu in yazo, dan haka duk sanda yazo nice abokiyar hirar sa Sultan bin mu kawai yake yi da kallo, daga baya sai Takawa ya mayar da zuwa gurin mu da daddare al'ada, kullum anan yake cin abincin dare a great room din Sultan.

Sai yanzu nake kara jin dadin koyon girkin da nayi, duk da dai har yanzu Asma'u tana nan amma hannu bibbiyu yafi sauri. Kullum Takawa bashi da labarin bawa Sultan sai na Khairat, Sultan kam sai yayi shiru ya rabu dashi baya tanka masa. Nayi nayi da Sultan ya gaya masa cewa mun sami labarin ta amma yaki. Shi har yanzu fushi yake yi da ita, yace in ta ki neman mijinta saboda taji haushin ya sake ta to shi kuma fa? Ina laifinsa a ciki?

Wata ranar friday da daddare, Takawa yazo kamar yadda ya saba, ni kuma ina ta faman hidimar jera musu abinci akan table mat din dana shimfida musu akan carpet, sai ga Amir nan ma yazo, ya gaishe da Takawa, suka gaisa da Sultan ni kuma na gaishe shi. Sultan yana ta tsokanar sa suna dariya kamar yadda suka saba.

Takawa yace "Sultan baka da kunya, Amir fa uba ne a gurinka" Sultan ya bata fuska yace "Uba kuma?" Takawa yace "eh. Mahaifina ne yayi adopting dinsa, dan haka legally ƙani na ne, hakan ya saka ya zama uba a gurinka" dani da Amir mukayi ta dariya, Amir har da rike ciki, Sultan ya bata fuska yace "wallahi ba'a isa ba" Takawa yace "daga yau baba Amir zaka ke ce masa. Amir duk ranar da bai ce maka baba ba kazo ka gaya min"

Amir harda yiwa Sultan gwalo, sannan yayi mana sallama ya fita, ina tayi masa mitar yaki tsayawa yaci abinci. Yana fiya na dauko yankakken apple na kawo gaban Takawa ya dauka ya fara ci yana min godiya, idonsa akan Sultan yace "me Amir yake ciki ne?" Sultan yace "as far as I know bashi da problem. Amir is the must cheerful man I have ever known, kullum cikin farin ciki yake, sam bai dauki duniya da zafi ba ko kuma wai ya saka wa kansa damuwa akan neman asalinsa. Matsalar da yake fuskanta daya ce, akan neman auren da yake yi, iyayen yarinyar da yake nema sun hana shi aurenta, wannan shi yasa kwanan baya naga ya tayar da hankalinsa amma yanzu ya fara dawowa normal duk da dai har yanzu ba wai rabuwa yayi da yarinyar ba"

Takawa yace "wacece yarinyar?" Sultan ya gaya masa sunan mahaifinta wanda yake malami ne a maiguduri, Takawa yace "ka gaya wa Amir, ya gayawa yarinyar ta gaya wa iyayenta, ni zanje da kaina har maiduguri in nema masa auren ta, nine waliyinsa"

Nan take sultan ya washe baki yana dariya, sai ince wannan shine karo na farko da naga Sultan yayi wa mahaifinsa dariya, nima kaina sai da naji dadi, Amir deserves more than that, saboda duk wahalar da Sultan ya sha a rayuwa tare suka shata, shima ya kamata ace ya samu farin ciki.

Amma kuma can kasan zuciyata ina tausayawa kawata Amira, Amir din ma data dan samu gashi ya gudu ya barta zaiyi aurensa, amma kuma banji haushin Amir ba tunda bai taba furtawa yace yana son ta ba ballantana ace ya yaudare ta. Amma duk da haka sai dana yiwa Sultan maganar bayan Takawa ya tafi, kamar bai jini ba daga farko sai kuma yace "why do you care about her ne wai? Ina ruwanki da ita? She is not loyal" nace "she was not loyal. Amma hakan ba wai yana nufin bata yi learning lessons din ta ba. Everyone deserves a chance at redemption"

Ya sake dauke kai, na saka hannu na juyo fuskarsa gurina nace "pleeeassse" ya kara bata fuska "to wai ke me kike so ayi mata ne? Shi Amir ga wacce yake so, so kike ince masa Amir ka fasa auren wacce kake so ka auri wacce Moon take so?" Nace "ba haka nake nufi ba honey, kasan yadda Amir suke da Amira, na tabbatar ba za'a rasa sonta a cikin zuciyarsa ba kawai dai wancan son ne ya danne wannan. Kuma shi na miji ai mijin mace hudu ne ko?"

Yana kallona kuma sai ya fara murmushi yace "ki sani, in dai akayi auren nan sai na gayawa Aysha kin ce ayi mata kishiya tun kafin a aure ta" nayi dariya nace "a'a kar ka hada ni da ƙawata, in dai har akayi auren to dama an rubuta cewa matar sa ce, bani na saka ba, shi aure ai rai ne dashi, ba'a creating dinsa ba kuma a destroying dinsa, sai dai a zama sila".

MaimoonTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang