The Emir

11.2K 768 9
                                    

Bara mu dan yi magana akan rashin iya girkin Moon. Na saka cewa Moon ba ta iya girki ba ne saboda ina son in nuna wa mazan da suke karanta littafin nan dama matan cewa 'nobody is perfect' babu, kar ka saka ran zaka auri mace kyakykyawa mai ilimi mai addini mai tsafta mai son mutane mai ladabi da biyayya mai iya kula da miji, mai iya kula da miji a other room kuma mai iya girki, NO, ba zai yiwu ba, kamar yadda shima namijin ba za'a samu wanda yake 100% complete ba. Tabbas akwai matan da basa son girki, kamar yadda akwai matan da basa son shara da wanke wanke, kamar yadda akwai mazan da basa son kallon ball. Girki is a hobby, sometimes yana zama necessity, to idan ya zama both shine ake samun matar da ta iya girki sosai. Idan kuma aka samu matar da bata da interest akan girki amma kuma ya zame mata dole to sai azo a samu matsala, saboda hakkin kula da abincin miji da 'ya'ya yana hannun mu mu mata. Idan kinsan bakya son girki to kiyi kokari ki fara son shi, saboda ba zaki koya ba har sai kina son ki koya din, make it a hobby, make it a challenge, ki fara da kadan kadan a hankali zaki ga kin fara son sa.

Har mota muka raka Amira da Amir, suna tafiya nayi gaba na bar Sultan dan har yanzu ba hucewa nayi ba. Daki na na tafi nayi kwanciya ta, ko minti biyu banyi ba kuwa ya shigo, na juya bayana na rufe ido. Ya zagayo ta gabana ya zauna akan gadon "wai kar dai ki ce min maganar abincin nan ce baki manta ba?", na turo baki, ya mintsini bakin nayi kara na sake juya masa baya.

Ya hau kan gadon sosai yace "to wai bana baki hakuri bane ba. I never meant anything by it. I don't want a good cook, I want you. Idan abinci ne I can get it anywhere amma ke guda daya ce, there is no one like you" ya juyo dani yace "please kiyi murmushi mana in gani" ina so inyi murmushin amma na kara bata rai nace "just promise me ba zaka kara cin abincin ta ba" yace "abincin wa?" Nace "ita dai" yace "ni bansan wa kike magana akai ba, I don't know anyone bayan ke" ya dora goshinsa akan nawa "now smile" nayi murmushi tare da zagayo hannayena a wuyansa, yace "that's what am talking about" na saka fuskata a wuyansa irin yadda yake min nace "I will learn to cook, for you" yace "NO, I don't want you stressing yourself out akan abinci, I will get a cook for us" nace "na riga na kira Mommy ai, tace zata bani aron Asma'u for sometimes" ya jawo fuskata ya rike a hannunsa yace "dakin bar musu Asma'un su mu ba sai mu samu tamu ba?". A haka dai muka kare har magrib sannan ya tashi ya tafi masjid.

Washegari tunda safe ya ce min zamu je mu gaishe da Yaya da Nani. Nace masa Hajiya fa? Yace sai Takawa ya dawo, baya kasar, in ya dawo sai muje mu gaishe su gaba daya. Muna gama breakfast na shirya cikin doguwar rigar lace, budaddiya, na gyara fuskata amma babu kwalliya sosai, na dauko jeweleries na zuba, na daura dankwali sannan na yafa babban mayafi, na kalli kai na a madubi, ni kaina sai da nayi mamakin chanzawar da nayi in few days, lallai aure daban ne, that little girl is gone, am a woman now, matar aure.

Sultan ya shigo ya same ni a tsaye gaban madubi, yazo ya tsaya a bayana muna kallon kan mu ta cikin mirror din. Ya sunkuyo a hankali yayi kissing kuncina yace "you look beautiful, Darling" na daga hannuna na shafa fuskarsa ina kallonsa ta cikin madubin nace "you look handsome too, Darling" a tare muka yi dariya, ya dauko wayarsa yayi mana selfie ta cikin mirror sannan muka tafi.

A bayan palace din sabon gurin yake, an kawata gurin sosai dan zaka dauka wani palace din ne daban, ko da yake gidan mahaifiyar sarki ai dole a kawata mata shi. Tun daga bakin gate ake ta gaishe mu, ni har kunya nake ji in naga manyan mutane suna durkusawa har kasa suna gaishe mu, na kalli fuskar Sultan naga ya wani hade rai kamar bai taba dariya ba, ni kuwa sai washe baki nake ina amsawa.

Direct part din Yaya muka shiga, da kanta ta fito har kofar palourn ta tare mu, ta kama hannuna ta jani jikinta ta rungume, sai naji kunyar ta sosai, naja mayafina na rufe fuskata, tana ta dariya tace "ni fa kakar kice ba surukarki ba, ki bude fuskarki ki kalle ni sosai, in kika tsaya wasa sai in kwace mijin, dama ara miki nayi" ina jin Sultan yana cewa "nan gani nan bari Yaya, ai wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa" suna ta wasan su na kaka da jika muka shiga ciki, har cikin bedroom dinta ta zarce damu.

MaimoonWhere stories live. Discover now