The Breakup

7.4K 616 5
                                    

Na yi shiru na zuba mishi idanu kamar yadda shima ya zuba min. Can ya dan yi murmushi yace "are you scared?" Na gyada kaina alamar eh. Yayi dariya yace "I am scared too, amma dole muyi haka, saboda inaso in kun koma gida zan ke zuwa gurin ki kuma kinga bazan ke zuwa bada iznin Daddy ba, it's not right" na sunkuyar da kaina nace Allah ya kai mu.

Washe gari har muka fitar da kayan mu bakin gate banga Ibrahim ba, mun dawo hostel muna sallama da mutane sai gashi yazo bakin gate, daga ganin sa nasan cewa he is not OK. Hafsat ce ta tambaye shi "sir, baka da lafiya ne?" Yace mata "wallahi kwana nayi da zazzabi" nan Hafsat ta saka shi a gaba da tsokana wai dan zamu tafi ne, nima kaina zazzabin nake ji. Muka je bakin gate yace shi ba zai karasa ba, wai ko wanka bai yi ba baya son ya shiga gurin mutane. Nan Hafsat ta barmu ta karasa gate. Tana tafiya ya matso kusa dani yace a hankali "so, finally dai zaki tafi ki barni" nace "ba kace za ka ke zuwa ba" yace "ba dole in zo ba? dan ke fa nake zaune a garin nan, only for you, yanzu ma tunanin yadda zanke spending days with out you nake yi." Nace masa "ai zamu ke yin waya" yace "bayan ke baki da waya? Kuma in kinje gidan bakya kirana da wata wayar" nace "ai zan kira ka yanzu" ya girgiza kai "ban yarda ba, ki bani number Mommy kawai" na zaro ido "laa to in ka kira ta me zaka ce mata?' "Sai ince mata son in-law dinta ne"

Nayi dariya, a raina nace lallai wannan bai san wacece Mommy ba. A fili kuma nace "Allah da gaske nake zan kira ka" ya marairaice fuska "yanzu tafiya zaki yi ki barni?" Nayi dariya ganin yadda yayi da fuskarsa, yace "au dariya ma kike yi min ko? Duk sanda Daddy ya bani permission kullum sai nazo" nace "Allah ya kaimu lokacin" Hafsat naji tana kwala min kira, naga tana dago min hannu, nasan anzo daukar mu kenan.

Naƙi tafiya, na kasa tafiya....

Sai gata tazo tace "in ba zaki tafi ba zanyi tafiya ta wallahi" na kalle ta na dauke kai. Ta riƙe baki tace "au kuka zakuyi? Bani phone dinka inyi muku hoton tarihi" kawai sai ya fito da phone din ya mika mata, ta karba ta bude camera ta dauke mu.

Na dan kwantar da kaina a kafadarsa shi kuma ya juyo da kansa yana kallona. Hoton yayi kyau sosai. Daga haka Hafsat ta figi hannuna muka tafi, ina jinshi a hankali yace "Maimunatu" amma ban juyo ba ballantana in amsa masa.

Muna zuwa gida muka tarar Daddy da Mommy sun shirya mana surprise party na graduation, duk kowa yana nan har neighbours an gayyato, ga cake kato da hotunan mu a jiki ni da Hafsat. Nan da nan muka chanja kaya zuwa dogayen rigunan da Mommy ta bamu as gift din ta, ta Hafsat pink tawa red. Munyi kyau ba kadan ba, Mommy tayi mana light make up.

Muka fito muka yanka cake tare da daukar hotuna, nan take naji duk na manta da alhinin rabuwa da Ibrahim. Muna gamawa Daddy ya kawo mana nashi gift din. Muna unwrapping muka ga wayoyi ne sababbi fil kirar Samsung galaxy edge ta Hafsat pink tawa red. Ai ji nayi kamar Daddy ya saka ni a aljanna. Muka rungume shi muna murna tare da cewa "thank you daddy" a tare.

Bayan an tashi daga partyn muka dawo main palo muka dasa sabuwar hira, muna ta basu labarin makaranta su kuma suna bamu labarin abubuwan da suka faro sanda bama nan. Ya Habeeb ya samu admission shima a Oxford inda zai karanci accounting. Anan Daddy yake ce min sunyi waya da PC din mu akan scholarship dina, "is that what you really want" nace eh, yace "to shikenan zance a bata din, Allah yasa haka ya zamar miki sadaqatujjariya" nace "amin daddy" nan ya kara yi mana nasiha akan tausayawa na kasa damu da duk wanda muka ga yana bukatar taimako, wanda duk ya taimaki wani Allah zai taimake shi.

Muna komawa daki da daddare mu ka dauko wayoyin mu muka kunna, dama already an saka mana sim cards a ciki. Hafsat ta dauko address book din da muka karbi numbers din friends din mu ta fara saving a wayar ta, ni kuma number da nake so inyi saving tana cikin kaina. Na zauna nayi dialing, bugu daya ya dauka, sai kuma na kasa magana, yayi ta hello3 can yace "Maimunatu talk now, ko so kike zuciya ta ta buga ne" da mamaki nace "ya akayi kasan ni ce?" Yayi dariya yace "nasan babu wanda zai kira ni yayi shiru, wato wayo zaki yi min ko?  Ke kina jin murya ta amma ni kinyi min rowar taki ko?" Nace "a'a ba haka bane ba fa. Dama so nake ince maka Daddy ya saya min waya" da sauri yace "haba? Amma daddy ya gama yi min komai"

MaimoonWhere stories live. Discover now