The Battle

9K 703 8
                                    

Ibrahim's POV

9 hours ago
Ya daga kai ya kalli agogonsa da yake kada karfe goma sha biyu na rana. Ya mayar da idonsa ya lumshe yana jin zafi a ransa. Tun safe yake kwance akan gadonsa, ko breakfast bai yi ba. It is time, yasan yau ne yasan kuma yanzu ne daurin auren Maimunatu dan har katin daurin auren yana dashi. Ya dauko katin yana juyawa a hannunsa, sau nawa za'a bashi katin auren Maimunatu ne wai?

Kamar yadda ya gaya mata ya hakura, he just want her to be happy, kuma indai happiness dinta will come from wannan auren to dole zai hakura da ita ko da kuwa zai cigaba da zama babu aure har karshen rayuwar sa. Amma tun ranar da yace mata ya hakura din bai samu sassauci na radadin da zuciyar sa take masa ba har yau. Why must his destiny be so cruel ne? Da ya rasa ta ya sha wahala after several years kuma sai gata har office dinsa only for her to tell him cewa bata sonsa yanzu wani take so kuma.

Ya tuna sunan mijin da Moon ta aura, Sultan, a Prince, ya tabbatar ba zata samu matsala ba tunda at least babban gida zata shiga, gidan daraja, she will be respected in the society. By impulse, kawai ya jawo wayarsa ya shiga instagram saboda yana son ya rage tunani, yana shiga ya fara scrolling through feeds, ya jima a haka kawai yaga hoton Moon tare da wani, ya tsaya yana kallon hoton saboda irin kyan da yaga tayi masa, yayi sauri ya dauke kansa yana kiran "auzubillah" matar wani ce yanzu, ko kallon mijin nata baiyi ba ya bude labarin kasan hoton.

Zuciyarsa ce ta buga da karfi har sai da ya mike zaune, jikin sa ya fara karkarwa, ya sake maimaita heading din labarin "The Drunk Prince of Abuja weds Today" a hankali ya fara karanta labarin, an danyi brief magana akan Sultan, irin halayensa da mutane suka sanshi dashi, sai kuma akayi bayanin yadda bikin ya kasance da irin kudin da aka kashe a bikin. Kafin ya gama karantawa gaba daya gumi ya jika jikinsa, ya fara duba comments din mutane, most of them suna cewa suna tausayawa Moon ne 'she looks so young'
'iyayenta sun cuceta'
'poor girl'

Wadanda kuma basu san iyayenta ba suna cewa 'kudi iyayenta suka gani suka bashi'

Ibrahim ya ajiye wayar akan gado ya rike kansa da yake sara masa, ya ilahi, me yake faruwa ne? Mai yasa Maimunatu ta auri mutum irin wannan? Ba class dinta bane ba. Ya sake daukan yawar yana ta bincike akan Sultan, anan yaga labarin gang bang da irin abubuwan da suke aikatawa a duk fadin Nigeria.

No, no, no, kawai yake maimaitawa "no I will not let Maimunatu destroy her life. But why is she doing this?"

Gani yake kamar duk abinda ya faru fault dinsa ne, da ace tun farko bai tafi ya barta ba da duk haka bata faru ba. A ganin sa babu wacce zata auri dan giya tace zataji dadin aure, babu kuma wacce zata auri known criminal kamar Sultan tace zata ji dadin aure.

Da sauri ya zura rigarsa ya dau key din motar sa ya fice, yama manta da zancen bai ci abinci ba. Supermarket dinsa ya tafi yayi kamar zai shiga sai ya tsaya, mai gadi yazo ya gaishe shi, yace masa "kasan wani dan Sarkin garin nan kuwa da ake bikinsa yanzu?" Da sauri yace "sosai ma kuwa yallabai, ai wannan babu wanda bai san shi ba a garin nan, tun yana yaro ya gagari ubansa, mai martaba sarki da kansa ya kaishi gidan gagararru, acan ya girma, naji labarin ma har kisan kai yayi a gidan shine suma suka ga ba zasu iya ba suka sallamo shi ya dawo" (kunji mutane ko? hmm)

Ibrahim yaji yawun bakinsa gaba daya ya dauke, mai gadin yace "Yallabai Allah dai yasa ba wani abun ne ya hada ka dashi ba?" Ibrahim yace "babu komai kawai labarin bikin naji" daga nan bai shiga ba ya fito da motar sa ya kuma hawa titi, tafiya kawai yake bai san inda zashi ba, mai yasa Daddy ya yarda ya aura wa Moon Sultan? Tabbas da akwai wani abu a kasa. Maybe blackmailing Daddy yake yi, tunda Daddy babban mutum ne, Sultan zai iya hada wata karyar yace idan Daddy bai bashi Moon ba zai fada a gari, irin abinda blackmailers suke yi.

Wani gurin cin abinci ya tsaya ya shiga, ya duba agogonsa yaga karfe biyu har da rabi, time is running out, he have to think of something. Dan kadan yaci abincin yaji ba zai iya ci ba, ya tashi yaje gurin biyan kudin sai yaga bayarabe ne cashier din, ya tambayeshi da yarabanci "kasan dan sarkin garin nan da aka yiwa aure kuwa?" Mutumin kamar dama jira yake yace "ni kuwa na san shi, ni da suka hana ni bacci jiya da daddare ba dole in san shi ba?" Ibrahim yace "suka hana ka bacci kamar yaya?" Mutumin yace "ai gidan da suka yi party jiya a kusa da gida na ne, shi mai gidan, Solomon, is a known criminal in Lagos, ya gagari kowa, he is a kidnapper as well as an arm robber. Gida kawai ya saya a garin nan ya ajiye in yayo barna a Lagos sai ya taho nan ya zauna kwana biyu sannan sai ya koma. Jiya a gidansa sukayi partyn su har gari ya waye babu wanda yayi bacci a unguwar nan saboda kiɗa, kwalaben giya kuwa da aka ringa shiga dasu gidan ni dai har kallo na fito yi, da safe makocina ya ce min ya leƙa ta window dinsa yaga ana ta shiga da matan banza gidan, mata irin wadanda bana mutunci ba, mu dai jiya Allah ne kadai ya saka ba'a kife da unguwar mu ba saboda yawan zunuban da aka aikata a ciki"

MaimoonWhere stories live. Discover now