Latifat

7.1K 703 6
                                    

Ina zuwa class Hafsat ta taso take tambaya ta "well, what did he said?" Na kalleta da jajayen ido nace "it's none of your business" ta jima tsaye a kaina sannan ta daga kafada tace "OK, in tayi tsami maji" da ace ana sayar da maganin sa ido da saina sayo na bawa Hafsat.

Two days suka wuce, zuciyata ta fara sanyi amma har yanzu ban huce ba. Ibrahim duk ya gama rikicewa saboda silent treatment da nake bashi. Amira kuma ta ja baya da komai, ta zama wata irin silent ba ta yiwa kowa magana, musamman ma ni.

On the third day muna aji a zaune sai ga Ibrahim nan yazo, ya taho direct gurina ya tsaya a gabana yace da karfi yadda kowa a class din zaiji "nace miki I don't love her, what more do you want from me?"

Gabadaya ajin kowa yayi shiru yana kallon mu ballantana su Hafsat sa ido. Nayi kasa da murya nace "what are you doing?" Ya kara daga murya yace "am telling everyone bana son ta ni ke nake so, ke kadai nake so"

Wata Jamila tace "sir wacece? A ajin nan take? Cewa tayi tana sonka?"

Na dan saci kallon Amira sai naga ta juya ma class din baya tana kallon waje, sai kawai naji zuciya ta ta karye, na dauki wani katon textbook na fara dukan Ibrahim da shi ina korar sa waje, amma yaki tafiya yace lallai saina fada masa cewa maganar ta wuce sannan zai fita, su kuwa 'yan aji sai kara tambayarsa suke ya basu labari.

Da naga dai Ibrahim da gaske yake so yake yayi wa Amira tonon silili sai nace masa na yarda, maganar ta wuce, yace "kinyi alkawarin ba zaki kara tayar da maganar ba?" Nace "I promise" sannan ya juya ya fita.

Yana fita Hafsat tace "well, dama nace in tayi tsami zanji, 'yan class din nan duk mai son yaji wacece yazo in gaya masa" nan da nan duk suka tafi gurin Hafsat, na kalli Amira naga alamar tsoro a fuskarta, nayi sauri naje gurin Hafsat nace "Hafsat dan Allah ki bar maganar nan" tace "sai kinyi min alkawarin daga yau aunty Hafsat zaki ke ce min" nace "done, Aunty Hafsat from today".

Sai da muka je hostel sannan Hafsat tace "ni daga ke har Amira kun bani mamaki wallahi, ni banga abin so a jikin wannan dogon mutumin ba" nayi dariya kawai ba rabu da ita, amma maganar ta ta tsaya min a rai. A lokuta da dama mutum ba shi yake zabar wanda zuciyarsa zata so ba, kawai haka kawai zakaji kana son mutum, wani lokacin kuma daga kaga mutum sai kaji baka son sa, ba tare da yayi maka komai ba. Kamar yadda lokaci daya na ji zuciya ta tana son Ibrahim duk da irin banbancin da yake tsakanin mu kuma ba tare da wani dalili ba dan ba zan iya cewa saboda abu kaza nake sonsa ba, kawai dai nasan ina son sa. Da nayi considering Amira sai naga itama haka ne a wurinta, kawai taji tana sonsa ne amma saboda kusancina da ita ya saka ta boye a ranta har sai yanzu da suke spending time together sannan ta fara nuna masa, it must be hard on her, especially yanzu da yayi declaring a gaban kowa cewa baya sonta, sannan gashi gandantakar mu ta shekaru kusan shida tana so ta baci saboda kawai ta kasa controlling zuciyar ta. She deserves a break from me.

Ina yin wanka na shirya sai na tafi dakinsu Amira, na tarar da ita a kwance idonta a rufe kamar mai bacci amma kana ganinta kasan ba baccin take yi ba. Na daka mata duka a cinya nace "sleepy head, ki tashi mu tafi karatu" ta bude idonta tana kallona da mamaki. Ita tasan na sani. A hankali tace "bana jin dadi ne" nace "yeah right, in kika fita zaki warke" a haka na takura ta tayi wanka muka fita.

Tun daga nan muka cigaba da kawancen mu da Amira, amma duk abinda muke yi da Ibrahim yazo gurin zata tashi, ni ma kuma bana cewa ta tsaya saboda ta ciki na ciki daurewa kawai nake yi.

Soyayya sabuwa muke shimfidawa da Ibrahim. Gani nake tunda na shiga SS3 ai I am old enough, shima kuma dama kiris yake jira. Sam Ibrahim baya kunyar nuna min soyayya ko a gaban waye ma kuwa, ni dai duk sai kunya ta rufe ni. Rannan a class ya zo yana cewa wai ya kasa bacci jiya kawai sai yaji muryata yake so yaji, wai saura kadan ya taho hostel, su kuma 'yan ajin sai su biye masa suyi ta tsokana ta, inna ga sun dame ni sai in tashi in bar musu ajin.

MaimoonWhere stories live. Discover now