The Wedding 2

7.4K 718 3
                                    

Thursday
Tunda na tashi da assuba na koma na cigaba da bacci na, cikin baccin naji kida na tashi kamar a tsakiyar kaina, na dauko pillow na dora a kaina na toshe kunne na amma a banza. Na mike a fusace ina mita "wai ba mother's eve aka ce ba? A bari sai evening din mana. Ni wallahi bacci bai ishe ni ba".

Amina da ta fito daga wanka tana shiryawa tace "to ke da wa ya aike ki ki zauna hira da Sultan har karfe dayan dare? Dama ta yaya bacci zai ishe ki? Ai kawai hakura zaki yi ki tashi haka" na mike ina tsaki, na leka ta window na ga DJ ne ya baje kayan kidan sa a dai dai gaban tagar dakina. Na kara wani tsakin ina duba agogo, 11:30, kamar zan yi kuka nace "fi sabilillahi karfe goma sha daya za'a dasa min kida aka? Ni dai kam an shiga hakkina"

Hafsat ta shigo cikin kwalliya tana kallona tace "wai yanxu kika tashi? Har Mommy tana cewa a kira ki ku gaisa da mutane?" Na kara bata rai na shige toilet. Ruwa na hada a tub na cire kayana na shiga na mayar da idona na rufe, take wani baccin ya sake dauke ni. Knocking kofar da akayi shiya farkar dani, ni ban ma san nayi baccin ba, muryar Mommy naji tana fada "uwar me kike yi a toilet din nan da har yanzu baki fito ba kin bar mutane suna ta jiranki?"

Da sauri na tashi na kammala wankan ina mita a raina 'duk Sultan ne ya jawo min wallahi'. Ina fitowa na tarar mai kyalliyata tazo dan haka mai kawai na shafa na zauna muka fara, Hafsat ta shigo ta zauna tana feeding Khairat sai ga Mommy ta shigo itama, ta zauna akan bed side tana kallona tace "me ya hada ku da Amira?" Gaba nane ya fadi duk da dama nasan wannan tambayar tana nan zuwa, nayi shiru bance komai ba, ta sake cewa "fada kuka yi ko?"

Hafsat ce ta bata amsa tace "eh Mommy, fada suka yi" Mommy ta danyi shiru sannan tace "akan me?" Nan Hafsat ta zauna ta bawa Mommy labarin duk abinda ya faru, har ta gama Mommy bata ce komai ba. Sai da ta gama sannan Mommy tace "Maimoon3. Sau nawa na kira ki?" Murya can kasa nace "sau uku" tace "you are not to see that man again. Kinji ni ko baki ji ni ba?" Nace "Naji" ta kuma cewa "I am very serious in na sake jin maganar sa sai nayi mugun saɓa miki wallahi. Yanzu ace few days to daurin auren ki har kuma kina fada da best friend dinki a kan wani saurayi daban?"

Nace "Mommy ni ba akan Ibrahim bane ba, akan tayi betraying dina ne, kuma ni ban hana ta zuwa gurin bikin nan ba, ita taga dama ta ki zuwa" Mommy tace "whatever, ni dai nace bana son sake jin maganar nan. Ok?" Nace "yes mother" tace "ita kuma Amira zata zo ta same ni ne, haka kawai akan wani saurayin da ko damuwa bai yi da ita ba zata watsar da rayuwarta kuma ta yi loosing best friend dinta"

Ta dauko wayarta tayi dialing ta fara magana "Hajiya salamatu lafiya kuwa? Jiya anyi kamu babu ke babu Amira yau ma kuma gashi har yanzu baku zo ba?" Ta danyi shiru tace "Kano kuma? Me ya faru? Aa gaskiya ku dawo, please ko jirgi ku shigo ni zan biya ko baku samu mother's eve din ba ku samu dinner. Ok na gode sai kun zo din" ta kashe wayar ta fita.

Da yamma akayi mother's eve, ranar naga gatan iyaye da 'yan'uwa, gidan taf ya cika da mutane kuma wai kowa saboda ni yazo, su Fa'iza ma sunzo tare dasu akayi komai. Har magrib sannan aka watse. Sallah kawai mukayi kuma muka fara shirin tafiya dinner. Na aika aka karbo min kayan dinner a gurin Sultan naxo na sake wanka na dan kwanta na huta zuwa isha sannan na tashi nayi sallar isha aka fara shiryani. Yadi ne cotton cream color doguwar riga data kamani daga sama sannan ta bude sosai daga kasa, daga baya kuma tana jan kasa sosai kuma anyi mata adon stones masu kyalli, ta gaba kuma anyi mata aiki kalar golden brown. Head dina, jaka ta da takalmina duk golden brown ne da adon stones cream. An gyara min gashina ya sauko har saman bayana an jera masa stones cream color sannan aka tubke shi da golden brown ribbon. Ni kaina dana kalli kaina a madubi sai da nayi mamakin irin kyan da nayi, a zuciyata nayi tasbihi ina godewa Allah.

Around 8:00pm muka isa hall din taron, already kowa ya shiga ya zauna amarya da ango ake jira. Sultan da tawagarsa ne suka fara shiga, aka saka musu kidan su aka gama cheering, sannan akace mu shigo, na juya na kalli tawagar kawayena duk sun saka ankon su na jan lace da yellow head, ga Hafsat a kusa dani ita kuma da yellow lace da jan head a matsayinta na maid of honour.

MaimoonWhere stories live. Discover now