Amina

10.7K 742 4
                                    


Kadan ya rage dariya bata kubce min ba saboda ganin reaction din fuskokin su. Sam ba haka suka yi tsammani ba, su a tunanin su babu matar da za'a gaya mata irin wannan maganar ta hadiye sannan ta bayar da amsa irin wacce na bayar.

Hajiya tace "kin sani? Kina nufin ya gaya miki exactly wannan maganar?" Ita kanta tasan cewa nasan karya suke yi, Nace mata "eh ranki ya dade ya gaya min, ai baya boye min komai. Ya gaya min komai na labarin sa har labarin asalin fara shan giyarsa" a take naga kalar idonta ya chanza, murmushin fuskarta ya kau. I got her exactly where I wanted her.

Na gyara zamana na harde kafafuwa na irin zaman da Sultan yake yi, na cigaba da cewa "nasan komai akansa, nasan duk abinda ya aikata a baya nasan kuma wanda bai aikata ba, nasan kuma abinda zai aikata nasan kuma abinda bazai aikata ba"

Daya matar tace "kuma duk kinsan halayensa kika yarda kika aure shi? Shi fa aure ba abu ne na wasa ba, in kika auri mutum kamar kin zabe shi ne ya zama uban 'ya'yan ki" nayi mata murmushi nace "ai in kana so kasan mutum, ranki ya dade, ba wajansa zaka kalla ba, ko kuma abinda mutane suke fada akan sa ba. Abinda zaka kalla shine his inner self, deep down waye shi. Sultan deep down is a good person, very good person, na gani kuma nayi niyyar fito da wannan goodness din nasa waje yadda kowa zai gani. Alhamdulillah, na fara samun nasara, dan duk wanda yasan Sultan shekara daya data wuce in ya ganshi yanzu yasan da akwai banbanci. Wata rana ina fatan kuma zaku ganshi kamar yadda nake ganinsa."

Sai a sannan Khulsum tayi magana bayan tayi tsaki tace "tana magana kamar wata psychologist" na juya na kalle ta nace "but I am a psychologist, I have a first class degree in psychology from the second best university in the world. I know exactly when someone is lying to me, and I also know when someone is hiding or trying to hide something, ni kuma in na san haka sai curiosity ya saka in fara binciken gano menene ake boyewar. Tun farkon ganina da Sultan na san cewa he is hiding a very dark secret dan haka na fara bincike, yanzu so far nasan abubuwa da yawa a kansa, wasu abubuwan da na sani ma shi kansa bai sani ba".

Na bi fuskokin su da kallo, kamar an tsiyaye musu jinin su daga jikinsu, na hango kiyayyata karara a rubuce akan fuskokin su. Kusan minti biyu babu wanda ya sake cewa komai a cikin mu. Hajiya ce ta kirkiro murmushi tace "ku tashi mu tafi, mun bar ango yana ta jiran amaryarsa" Khulsum ce ta fara tashi ta fita ba tare da ta kalli inda nake zaune ba. Har mota na raka su ina ta nanata godiya ta a gare su bisa ziyarar da suka kawo mana da kuma albarkar da suka saka mana a auren mu, na daga musu hannu sannan suka tafi.

At least nasan yanzu tsakanin mu is clear, babu munafunci babu yaudara. Ba zasu sake zuwa su ce zasu gaya min wata magana akan Sultan ba, amma kuma nasan na kunno wata wutar kuma. Na gaya musu nasan secrets din su dan haka na kara wutar kiyayyarda suke yi min. But I was ready, Allah yana tare dani and I was not scared. Na yarda da Allah na yarda da kaddara, nasan su basu isa suyi min komai ba, duk abinda ya same ni daga Allah ne ba daga gare su ba. Kuma komai nisan jifa kasa zai dawo, duk kuma abinda ka shuka shi zaka girba, in khairan khairan in sharran sharran.

Ina komawa cikin gida na koma part dina nayi wankan da ban samu nayi ba, ba fito na shafa special mai na, na kuma fesa turaruka daban daban. Na jima ina neman kayan da zan saka, daga baya na dauko wata rigar bacci deep red, wadda akayi da lacy material, tsahon ta bai karaso rabin cinyata ba, tana da hannun bra da kuma matching panties amma babu bra. Ni kaina dana kalli madubi sai da naji kunyar kaina, kalar ta kara fito da haske da kuma kyan fatar jikina. Na dauko deep red lip stick na shafa a lips dina. Na dauko dogon hijab har kasa na saka, sannan na fita.

A palourn sa na ciki na tarar dashi, yana  kashingide da fararen singlet da gajeran wando a jikinsa, ya kunna TV ya rike remote a hannunsa amma kuma ba kallon yake ba, yayi nisa a tunani yana kallon sama. Na jima a tsaye ina kallonsa amma bai ma san na shigo dakin ba. Na dan daga murya nace "wanne film kake kallo ne?" yayi sauri ya kalle ni sannan ya kalli TV din, ya daga kafada yace "I don't even know me suke yi. Baƙin naki sun tafi ne?"

MaimoonWhere stories live. Discover now