His Mother's Son 2

10.5K 684 1
                                    

Tace "to ni yanzu moon ta ina zan same shi?" Nace "How will I know ni da bana kasar ma" tace "Moon tsoronsa nakeji, tunda ya gane gaskiya bamu hadu ba, bansan wacce irin karba zai yi min ba" na danyi tunani a raina, tabbas Ibrahim yana jin haushin Amira sosai, dan haka ba lallai ne yasaurare ta ba in taje wajansa, Allah ma yasa karya faffalla mata mari. Sai kuma wata shawara ta fado min arai na, nace "abinda za'ayi Amira, kije gidan mu gurin Amina, ni zan kira ta in yi mata bayanin abinda nake so tayi, zata hada ki da Ibrahim kuyi magana, duk abinda ake ciki kuma sai muyi waya"

Ina gama yawa da Amira na sake kiran Amina, ta dauka tace "what again?" Nace "ke dalla can ba maganar shi zanyi miki ba" sai nayi mata bayanin duk yadda mukayi da Amira, nace "yanzu taimako nake nema a gurinki, so nake ki hada su ta roke shi gafara, kema dan Allah sai ki tayata rokonshi" tace "kuma kika ce min ba maganarsa zakiyi min ba" nayi dariya nace "amma ai ba maganarsa dake nayi miki ba, maganar abinda ya faru tsakaninsa da Amira nayi miki" ta danyi tsaki tace "ba lallai ne fa ya yafe matan ba, tunda har yanzu bai manta ki ba ba lallai ya yafewa wadda ta raba ku ba"

Nace "in kika hada su ne zaki tabbatar cewa ya manta dani yanzu, nayi miki alkawarin zaki sha mamaki, bazan miki alkawarin zai manta dani completely ba tunda nima ban manta dashi completely ba amma babu zancan soyayya, an wuce gurin, sai mutunta juna. Duk kanin mu, ni da ke, Ibrahim da Amira, duk mutane ne mu, muna making wrong decisions a rayuwar mu, muna sabawa Allah ma kansa ballantana mutum, amma in muka nemi gafarar Allah sai ya yafe mana, ya sake bamu chance saboda yana son mu chanza mu zama mutanen kirki, to me yasa mu mutane ba zamu ke yafe wa junan mu ba? Me yasa zamu ke riko a ranmu bayan munsan cewa muma muna so in mun yiwa wani laifi ya yafe mana. Please Amina kiyi kokari kiga Ibrahim ya yafe wa Amira kema sai ki yafe masa ki sake bashi chance"

Ina kallon Sultan ya shigo dakin da takardu a hannunsa ya tsaya yana kallona, Amina tace "shikenan, zanyi magana da Amirar in gani, I will see what I can do" muka ajiyar wayar.

Sultan har yanzu yana tsaye yana kallona, am sure yaji ambaton sunan Ibrahim da nayi a waya, na tsaya ina jiran inga reaction dinsa, ya karaso inda nake yace "Madam problem solver, kina nan amma kina solving problems din wadanda suke thousands miles away" naji dadi da ya fahimce ni, ya zauna a gefe  na ya miko min takardun hannunsa yace "Ummee tayi miki maganar nan?" Na karbi takardun ina dubawa, da sauri na mike zaune sosai ina kara dubawa, na girgiza masa kai nace "bata yi min maganar ba, ta dai ce saboda kai ta fara kasuwancin ta, amma bata gaya min cewa sunan ka ne akan komai ba" dukkan takardun abinda Ummee ta mallaka ne, hatta takardun wannan gidan, da bank account dinta, da takardun dukkan contracts din data karba na shigo da kaya, duk sunan Sultan ne a jiki.

Na ajiye takardun ina kallonsa, yace "how do I tell her ni bana son kudinta without hurting her?" Na girgiza kaina nace "mahaifiyar kace sultan, duk abinda ta baka ba faduwa tayi ba kuma kaima in ka karba ba faduwa kayi ba, karbar da zaka yi a ganina shine nuna godiyar ka gareta, inka mayar mata ka nuna mata baka so ba zata ji dadi ba, ka karba amma sai kace mata ka barta a matsayin care taker ta dukiyar taka, ta cigaba da kula da ita kamar yadda takeyi da" yace "to wannan uban cash din kuma da yake banki ya zanyi dashi?" Nace "kudi ne fa, you can do anything with it" ya jawo ni kan cinyarsa yace "ke a shawarar ki me kike ganin ya dace inyi dasu?" Na gyara kwanciyata a kan cinyarsa na danyi tunani kadan sannan nace "why not ka sake gina wata orphanage din, kuma ka bunkasa wacce kake da ita already, kace kana son gina musu makaranta da daukan malamai. Kaga idan kayi haka daga kai har Ummee zaku samu lada har karshen rayuwar ku", yana murmushi yace "har ke da kika kawo shawarar" na mayar masa da murmushin nace "yes, har ni dana kawo shawarar".

Washegari Ummee ta kaini gidan su Zayed na wuni a can Umm Zayed me kirki sosai gata wayayyiya, da sister dinsa Zahra, na sake sosai dasu muna ta hira da Zahra muna hirar London tunda acan ta tashi wai tana son komawa tayi karatu amma an hana ta a gida, muna cikin hira tace "amma kinfi sister dinki kirki, ita bata yiwa mutane magana" nayi dariya sosai nace "ba haka bane ba, Hafsat tana da kirki sosai, kawai dai banbancin halayya ne a tsakanin mu, ni ina da surutu da saurin sabo da mutane ita kuma bata kula mutane sosai, amma in kika saba da ita zaki fahimci tana da kirki sosai. Abinda zakiyi ki lallaba a barki ki je England gurinsu ki dan kwana biyu, zakiyi mamakin kirkin Hafsat"

MaimoonWhere stories live. Discover now