Little Love

8.3K 614 3
                                    

Na taso na dawo kusa da ita na zauna nace "yes Ummee, we will. Nayi miki alkawarin Sultan zai zo gidan nan, kuma in yazo zaki yi mamakin sa, dan duk wannan zuciyar da wannan fushin na dan lokaci ne, haka yake, akwai saurin hawa kuma akwai saurin sauka, I assure you yana ganinki shikenan komai zai wuce, he is just not sure of yadda zaki karbe shi ne, duk wannan girman jikin da wannan kwarjinin a ido ne kawai, in side him he is the kindest man I have ever known, yana da tsananin tausayi da kuma kokarin kyautatawa mutane, ko da kuwa wadanda suka zalince shine bai damu ba, he said kyautatawa mutane makes him feel good shi yasa yake yi, ballantana ke da kika haife shi, kallo daya zaiyi miki and it will all be over, he will take you in his arms and cry on your shoulders, he will love you fiye da yadda kike tsammani, zai zamar miki ɗa daya tamkar da dubu, he will feel Lucky to have you as his mother"

Sosai maganganu na sun kwantar mata da hankali dan har murmushi na gani akan lips dinta, ta kama hannayena duka biyun tace "Maimunatu bansan me zance miki ba daga ke har iyayenki, you are really an angel a rayuwar ɗana, bani da bakin da zan gode miki sai dai in dawwama har karshen rayuwata ina yi miki addu'ar"

Ta dora hannunta daya akan cikina tace "ubangiji Allah ya jagoranci rayuwarki, da duk kanin zuri'ar ki, ya baku kyakykyawar rayuwa fil duniya wal ahkhira, Allah ya daga garajarki da duk kanin ahlinki, Allah ya kade duk wani sharri dake cikin rayuwar ku ya tabbatar da alkhairi a duk al'amuran ku, Allah yayi miki sakayya a bisa duk abinda kika yi a rayuwar Sultan. Allah ya albarkaci zuri'arki yasa su zamo sanyin idaniya a gare mu baki daya. Allah kuma ya kara soyayya a tsakanin ki ke da mijinki, ya dauwamar da zaman lafiya a tsakaninku, ya sa ku kasance tare har karshen yaruwar ku"

Duk abinda take fada ina cewa amin, kuma ina jin dadi har raina, sai da ta gama yi min addu'ar sannan ta jawo ni jikinta ta rungume tace "Nagode Maimunatu".

Kwana biyu bayan nan, ni gani nake yi ma kamar nafi Sultan damuwa, komai nake yi hankali na yana kansa, da kaina nace Hafsat ta bani sim card dina amma taki, kullum Sultan yana cikin kiran wayar Hafsat, tun yana yi mata masifa har ya koma bata hakuri yana lallashinta, ita kuma tace sai ta rama fadan da yayi mata, in naji suna waya sai in ji kamar in kwace wayar amma nasan muna yin magana da Sultan zai kalallame ni yace in dawo Nigeria, I don't think I can resist him in inajin muryarsa.

Little Khairat ce ta zama babbar ƙawata dan tun ranar da muka je gidan su Zayed na taho da ita gidan Ummee, tana ta rarrafenta ko'ina, in tana gurina babu abinda yake kaita gurin Hafsat sai in zata ci abinci. Ummee kuwa sosai muka kara sabawa da ita. Kamar yadda tayi min alkawari haka ta zage wajan koyamin girki, abincin larabawa iri iri haka take koyamin, babu abinda take so irin in zauna inyi ta bata labarin Sultan, wannan kullum shine abin hirar mu. Hotunan sa kuwa na waya ta ta gansu yafi a kirga.

A wayar Hafsat na hada ta da Mommy suka gaisa, nan take suka kulla kawance. Mommy ta gaya min ta yaba da ita tun kafin ma ta ganta.
Ranar dana kwana biyar a Riyadh, muna dinner da daddare sai ga kiran Sultan a wayar Hafsat. Ta nuna min screen din sannan ta daga. Sun danyi magana sannan tace min "yace in ba zaki karbi wayar ba in saka shi a speaker zai yi miki magana, na kalli Ummee naga alamun anticipation a fuskar ta, she has never heard her son's voice tun da suka rabu, na gyada wa Hafsat kai, ta saka wayar a speaker ta ajiye a kusa dani, naji muryarsa "Moon please listen to me, why are you punishing me for the crime I didn't commit? Ni laifin me nayi wai? Kina so zuciyata ta buga in mutu ko?"

Na danyi murmushi, dadin baki yake so yayi min, ya cigaba da magana, "Love please, nasan kinaji na, kuma nasan me kike so, I promise you zanzo amma kinsan it will take time, dan Allah na wahala haka, kar kice ba zaki yi min magana ba sai nazo, I can't take it kin sani"

Ummee ta taso ta dauki wayar da fitar daga hands free ta miko min, na karba na ajiye Khairat da take bacci a kan cinya ta, na mike na fita veranda, ina jiyo Hafsat tana gyaran muryar tsokana amma ban kula taba, na saka wayar a kunne na nace "My Love" kamar ba zaiyi magana ba amma ina jiyo numfashinsa a hankali, sannan yace "why are you doing this?" Nace "I just want you to come and see your mother, shikenan"

MaimoonWhere stories live. Discover now