The Rush

7.5K 641 5
                                    

Sai around 11pm muka bar club din, muna tafiya a hankali kamar yadda ya saba, ya tambaye ni "so, anything you want to ask me?" Na danyi shiru for some seconds sannan nace "why do you join the gang bang?" Sai da yayi dariya sannan yace "ke baki ji yadda sunan yake ba? It sounds dangerous, duk wanda aka ce dan wani gang ne mutane zasu ke tsoronsa, tsoro kuma yana kara wa mutum kwarjini, irin bad boy dinnan" nayi dariya nima nace "kai kuma burinka shine mutane suce maka bad boy right?"

Yayi shiru bai ce komai ba, sai ya chanza maganar yace "waye ya baki labarin gang bang?" Nace "Amira, she told me about the rape case" na fada direct ina studying dinsa ga mamaki na sai naga yana dariya, yace "dama wannan Amirar daga ganinta zatayi surutu da tsegumi" na hade rai nace "ba abin dariya bane ba ai, how can you get involved with those kind of people? Duk wandanda zasu hadu suyi raping yarinya karama kamata yayi ka nisanta kanka dasu ba wai ka kirasu friends ba"

Ya daina dariyar yace "no body raped anybody fa, it was all politics. Shi yaron da akayi case din akansa Daniel, lokacin babansa yana takarar governor a Nassarawa. Yarinyar da ake magana akanta tsohuwar budurwarsa ce fa, dama sun saba harkarsu kuma she is not an ordinary girl dan banbancinta da karuwa kawai dan ita a gaban iyayenta take, she knows duk sunayen friends din Daniel, lucky for me bata san ni ba, kawai rana daya aka zo aka bawa iyayenta da ita kudi suka ce wai Daniel da friends dinsa sun zo har gida sunyi raping dinta"

Na katse shi nace "maybe kai a yadda kaji labarin kenan, mutane irin su fa babu abinda basa iya aikatawa" shima ya katse ni yace "OK, she mentioned Amir's name, kuma ranar da tace abin ya faru tare muka wuni muka kwana da Amir, sai dai in a cikin bacci yayi raping din nata. Abubuwa da yawa yadda ake bada labarin su ba haka suke ba, kawai ke dai believe what you see, duk wani abinda wani ya gaya miki kar kiyi believing".

Sai da yayi packing sannan na lura how late it was, few minutes to 1am, ni da a gida nake na isa in kai karfe goma ma a waje? Sai kawai naji guilty feeling. Ya zagayo ya bude min kofa na fito muka yi sallama sannan ya koma mota amma yaki tafiya, nasan sai yaga na shiga gida zai tafi dan haka na tafi na fara kokarin bude kofa, ji nayi kamar ana kallona, na waiga baya da sauri sai naga Mahdi can nesa damu a gurin flowers, duk da cewa gurin da akwai duhu amma hasken fatarsa ya tona masa asiri. Ban nuna na ganshi ba saboda Sultan will not take it lightly, na bude kofa na shiga nayi waving at Sultan sannan na rufe. Da jikin kofar na jingina zuciya ta tana bugawa, is Mahdi stalking me? Mahdi yasan Daddy na kuma yana sona dan haka yana kishin mu'amala ta da Sultan, nasan babu abinda zai hana shi zuwa ya bawa Daddy labarin Sultan. Menene abinyi yanzu? To ko zuwa zanyi in same shi muyi magana ta fuskantar juna? Zuciya ta naji duk babu dadi, na mike na shiga toilet nayi wanka nayi alwala, nazo nayi shirin kwanciya, ina kwanciya na fara lissafin abubuwan da suka faru yau ina rewinding dinsu daya bayan daya ina kara fahimta, yau na sake fahimtar abubuwa da yawa akan Sultan, kuma naji dadin mafi yawa daga abubuwan dana fahimta. Na dago hannuna daya saka min ring ina kalla. Wani nishadi naji yana shigata, kawai na fara murmushi ni kadai like an idiot.

Kwanci tashi har muka kammala duk abubuwan da suka kawo mu America muka fara shirye2n komawa England. Ana gobe zamu tafi Sultan ya kuma dauka na yawo, wannan karan cewa yayi zai nuna min abubuwan da yake yi for fun sanda yana America. Farko race track muka je kallon car race. Daga nan muka tafi bayan gari wajen wani ranch yace mu hau dokuna, ni kam ban iya hawa ba dan haka sai na dauko camera nake yi masa video. Sosai ya burgeni yadda ya iya sukuwa a doki danni har tsoro yake bani dan gani nake kamar zai fado, shi kuwa kamar wadda nake kara zuga shi har mike wa tsaye yake yi, yadda iska take diban gashin dokin tana wasa dashi haka take diban na Sultan shi ma. A mota ma bayan mun bar gurin videon na cigaba da yi masa yana ta tsokana ta wai ni matsoraciya ce nace na yarda din.

Daga nan yace "I want to show you one last thing kafin in mayar dake gida" tafiya muka sake yi mai nisa sannan muka zo gurin wasu duwatsu, sam babu mutane a gurin, muka fara hawa wani dutse mai tsaho dan ni kam da kyar na kai duk na gaji. Muna zuwa na kunna camera ta na cigaba da video, ya nuna min gurin da zan tsaya shi kuma ya koma baya, sai da yayi kusan rabin dutsen sannan yayi  min magana da karfi yace "get ready" ni dai bansan me zai yi ba kuma, nayi zooming dinsa ta camerar naga ya cire shirt din jikinsa ya bar singlet kadai, ya durkusa kamar me shirin gudu, kar dai Sultan yace min da gudu zai hawo dutsen nan, ina kallon fuskarsa yayi taking deep breaths sannan ya fara hawowa a guje, wow , shine kadai abinda na iya fada, na saki baki ina kallonsa ta screen din camerar, dukkan jikinsa a mummurde yake musamman yanzu da ya cire rigarsa, yadda muscles dinsa suke rippling ne ya saka nayi sauri na runtse idona, I shouldn't be looking at this kamar yadda I shouldn't be doing abubuwa da yawa da nake yi. Iskar gudunsa kawai naji tazo ta wuce ni sannan na bude ido na naga ya doshi clip din dutsen kuma bashi da niyyar tsayawa, yana zuwa karshe naga ya doka tsalle ya fada. Zuciya ta ce naji kamar ta fado kasa, a rikice na yar da camerar hannuna na tafi inda ya fada da gudu ina kiran sunan sa. Ina zuwa karshen dutsen na leka kasa tare da durkutsewa a gurin, kadan ne ya rage ban faɗa ba nima.

MaimoonWhere stories live. Discover now