The Weddings

9.7K 680 2
                                    

Bikin Amir aka fara. Babu abinda Ummee da Takawa basu yi masa ba. Duk wani gata da ɗa yake nema a gurin iyayensa Amir ya samu a lokacin bikinsa, duk abinda uwa zata yi Ummee ce tayi abinda uba zaiyi kuma Takawa ne yayi. Sanda za'a tafi dauko amarya Ummee hana ni zuwa tayi, tace maiduguri yayi nisa bazan je ba, amma sanda aka kawo amaryar direct  fada aka kawo ta gurin Ummee, ni kuma ina zaune a hannun daman Ummee. Sai a lokacin naga abinda Amir yake yiwa naci, ba wai kyawun yarinyar ne kadai zai ja hankalin ka gare ta idan ka kalle ta ba, kana ganin ta kasan she is well brought up, har cikin raina ina kyautata zaton cewa Amir yayi dacen mace ta gari insha Allah.

Washegarin da aka kawo Aysha, ni da Sultan muka shirya musu dinner. Takanas na kira Saratu da Fa'iza suka taya ni organizing dinner din, a cikin fada muka karbi hall akayi dama yanuwanta basu tafi ba dan haka tare da su akayi komai, Sultan ya zuba kudi sosai, kuma abin ya kayatar sosai. Bayan an tashi daga dinner Amir ya sake kawo min Aisha har gida muka sake gaisawa. Haka kawai naji ta kwanta min a rai kuma daga dukkan alama tamu zata zo daya.

Saratu da Fa'iza kam by now sun fahimci cewa auren iyayensu ya rabu amma bana jin sun san dalilin rabuwar auren. Ba laifi sun dangana, dan suna yiwa Ummee biyayya dai dai gwargwado, Ummee kuma kullum tana jan su a jikinta, dan komai zatayi sai ta hada da daya daga cikin su. Abbas har yanzu basu shirya da Hajiya ba, dan har yanzu anan gurina yake komai nasa. Yaji shawarata kuma ya koma makaranta, shi da kansa yaje ya nemarwa kansa admission, saboda sunan Takawa da yake amfani dashi bai sha wahala ba gurin neman admission ba aka bashi, tunda ya fara zuwa makaranta ya tattara harkar sarautar ya ajiye a gefe ya rungumi karatunsa. Ya nuna min rashin jin dadinsa game da kwafsa masa da Amira tayi, ni kuma nayi masa alkawarin zan samo masa mata wacce tafi Amira komai.

Na sami wani private hospital mai kyau, likitan su kwararre ne a harkar gynecology, nayi booking anan zan haihu. Sun yi min aune aunen duk daya kamata suyi min kuma sun gayamin zanke zuwa duk sati ana dubani, tunda yanzu edd na saura sati uku ya cika. Likitan yayi noticing high bp na, kuma mun zauna munyi magana dashi akan irin kalubalen da zan iya fuskanta. Na riga na sani, tun sanda na samu ciki, amma so far Alhamdulillah, dan lafiya lau nake bani da wani problem in banda bp din da take high.

Rannan muna palona ni da Sultan, ina zaune akan kujera shi kuma yana kwance akan kujerar ya dora kansa akan cinyata muna kallo, na saka hannuna absently ina shafa gashinsa, ina jin cikarsa da laushinsa, nace "wannan gashin dai ya kamata a rage shi, in ba haka ba zan fara yi maka kitso" ya danyi dariya yace "bismillah" na fara tsagawa da hannuna ina kitsawa, yace "ouch, da zafi fa" nace "kar ka bada ni mana, ka tsaya inyi maka mai kyau" ya biye min kuwa ya tsaya, nayi ta jagwalgwala masa gashin, nayi masa kitso guda biyar, ya tashi zaune yana shafa kan ni kuma ina tayi masa dariya, shine har da zuwa bedroom ya kalla a madubi, ya dawo ya tsaya yana kallona yace "da ace ni macene da maza sai sun bi layi sannan zan zaba"

Nayi dariya ina kallonsa nace "Allah yasan nufin jaki shi yasa bai bashi kaho ba" ya koma daki sai gashi da comb ya dawo ya kwanta ya dora kansa a cinyata yace "tsefe min" na karbi comb din ina tsefe masa ina tajewa. Yana kwance yayi shiru kamar mai bacci amma ba baccin yake ba. Na fara magana "you once asked me yaushe na fara son ka and I told you ban sani ba, amma yanzu na tabbatar cewa I fell in love with you the second time I saw you"

Ya gyara kwanciyarsa yayi rigingine yana kallona yace "a dinner din Hafsat?" Na girgiza kaina nace "A Hilton" ya dan bata rai alamar tunani yace "that's the first time" na girgiza kaina nace "no, it is the second. The first time dana fara ganin ka a TV ne. Kuna fada da wani akan titi 'yan jarida suna dauka, daga baya aka kirawo police suka zo suka kama ku, they handcuffed you and you were smiling, it was as if you were enjoying yourself"

Ya danyi murmushi yace "I can't remember wanne daga cikin fadan ne kika gani but I know I was" na cigaba "wannan shine dalilin da yasa sanda muka hadu a Hilton, duk da cewa naji wani abu a zuciyata game da kai amma sai na baka wrong information, saboda a lokacin na riga na saka a zuciyata cewa you are a bad person. But my love for you is too strong. A hankali na fara gane ainahin ko kai wanene and the love I have for you grow stronger" duk maganar da nake idona yana cikin nasa hannuna kuma yana kan fuskarsa ina shafawa.

MaimoonWhere stories live. Discover now