Zayed

6.6K 651 2
                                    

Tun daga ranar Mahdi ya zama best friend dina, in har ina cikin asibiti to muna tare dashi, rannan muna zaune dashi nace "dan Allah Mahdi in tambayeka" ya cire glasses dinsa yana kallona yace "ina jinki" nace "dan Allah da gaske kai bahaushe ne? I mean biologically?" Straight yace min "no, babana adopting dina yayi" da sauri nace "yes!! I knew it" dariya yayi sosai har yana buga kafa sannan yace "wasa fa nake miki, serious ni bahaushe ne, why do you doubt it?" Sai naji kunya kuma nace "kawai dai ba kayi kama da hausawa ba" yayi shiru sannan yace "my mother was shuwa arab, ni kadai ta haifa Allah yayi mata rasuwa, so.... I am different duk a family, wannan shi yasa na taho kasar waje karatu, I want to feel like I belong, a gida kullum kamar alien nake ji na a cikin siblings dina" na sunkuyar da kaina inajin ba dadi, ace ka zama kamar bare a cikin 'yan'uwanka babu dadi, nace "am sorry about your mom, am sorry I asked you" yayi murmushi yace "chill, ba komai, it is better that you know".

Har gida na kai Mahdi ya gaishe da Daddy, take Daddy ya gane shi kuma yayi masa fada akan baya zuwa yana gaishe shi. Karatun mu muke yi sosai har muka gama first year din mu a clinical, sanda muka je hutu gida kamar za'a chinye mu danyu, babu shiri Daddy ya sako mu a jirgi muka dawo England. Munir da ya ganni kamar zai yi hauka, lallai ai shi Baffa yayi masa alkawarin aure na. Inna da Daada ma yanzu sun fara mita, a cewarsu ya kamata by now ace muna da tsayayyun samarin da muna gama makaranta sai aure. Four years kenan rabona da Ibrahim, tabbas har yanzu ina jinsa a raina amma sosai na rage tunaninsa. Sometimes na kan yi lissafin ko me yake yi yanzu? Sai kuma in yi sauri in kawar da tunanin saboda bana son in dawo wa da kaina aiki baya. Sai da muka shiga final year din clinical sannan na fara fahimtar cewa Mahdi is gradually falling in love with me. Yawan kira na a waya, kullum da weekend yana hanyar embassy gurina, ga yawan compliment, duk kayan da na saka sai yace nayi kyau, ko kuma yayi ta kallona a sace in mun hada ido ya yi sauri a dauke kai. He is really a nice guy and I really don't want to hurt him, amma sam ni bana jin sonsa a raina, I like him, but I don't love him.

Rannan muna daki da Hafsat da Amina, sai Amina ta dau waya ta tana ganin pictures kawai sai taga hotona da Mahdi. Tace "wow, Moon wannan gayen fa?, gaskiya ya hadu ba karya" nace "wa kenan?" Ta juyo min screen din naga Mahdi nace "ohh, he is my friend, sunan sa Mahdi" tace "wait, don't tell me bahaushe ne" nace "dan kano ma kuwa, kanon ma cikin badala" ta bude baki tana kallona da mamaki sannan ta sake kallonsa, sai kuma tayi murmushi tace "something is really cooking here, wannan din za ki ce min wani friend din ki? Mu dai a fada mana ba sai tayi tsami ba" nayi dariya nace "am serious, we are just friends" tace "then something is definitely wrong with you, anya kuwa kina da lafiya, anya kuwa female hormones estrogen and progesterone suna aiki a jikin ki kuwa?" Nayi dariya kawai na share maganar ta, amma kuwa maganar ta tsaya min a rai, ba maganar Mahdi ba, maza in general, sam bani da interest a kan su, sam bana jin wani feeling idan naga wani namiji me kyau ko kuma in muna tare da wani namiji ballantana Mahdi wanda jinsa nake kamar Hafsa. Na tuna sanda muna tare da Ibrahim yadda nake jin attraction a tsakanin mu, why is it now gone? Yanzu dana kara girma ma ya kamata ace libido na ya karu amma it's like I have none. Na zauna ina lissafo Mahdi, komai nashi is perfect, sai kawai naji a raina ina comparing dinsa da Ibrahim. Mahdi is far more handsome than Ibrahim, more educated, more richer, his family is well known, kuma a kyawun dabi'a ma ban taba kama Mahdi da hali marar kyau ba, dan tunda muke bai taba taba ni ba. Amma why is it that in na tuna shi bana jin komai amma in na tuna Ibrahim nake jin pang a zuciyata, why must love be so cruel? Da haka na yanke shawarar cewa I must do something about Mahdi tun kafin inyi hurting dinsa.

Rannan yazo gida gurina kawai sai nace masa "ni kuwa Mahdi baka taba fada min wacce irin mata kake son aure ba" kamar wanda na sosa masa inda yake yi masa kaikayi nan ya fara lissafo min duk siffofi na da halaye na yana murmushi, yace duk sune abinda yake bukata a gurin matarsa. Ji nayi kamar hawaye zai zubomin dan na tabbatar da cewa he is head over heal in love with me. Sai da ya gama tsarinsa sannan yace "ke kuma fa" na kakalo murmushi nace "OK, inason namiji baki, kakkarfa, mai ilmi, mai addini.. " ya katseni yace "baki kuma? Why?" Na sake yin wani murmushin nace "tun ina yarinya haka kawai sai nake ganin kamar dark color is for men and fair color is for women, to har girma na sai ya kasance I am more attracted to darker men then fair men" murmushin fuskarsa naga yana subucewa, nayi sauri nace da alamar mamaki "oh God am so sorry Mahdi, you are very handsome the way you are, it's just my short coming and it's not as if you are in love with me, right?  Na tambayeshi zuciyata na bugawa, ya sunkuyar da kansa kasa sannan ya girgiza kai yace "you are right, I just find it weird cewa ba kya son maza farare" ya hadiye wani abu a makogwaronsa yace "bara in tafi, see you tomorrow " bayan ya tafi na jima a gurin a zaune, I hated hurting him amma it's better this way, na dafe kaina nace "ohh Ibrahim, what have you done to me? Kai kana can kayi auren ka ni kuma I can't even have a boyfriend"

MaimoonМесто, где живут истории. Откройте их для себя