New Little Love

9.7K 678 6
                                    

Shiru dakin babu wanda yayi magana. Ummee ce ta fara katse shirun tace "me ake jira ne wai? Ka bishi mana kuje ya dauka asaka mata" babu wanda yayi magana still.

Doctor ya fahimci akwai tension a gurin sai yace "bara inje office, Ibrahim in zaka bayar din ka same ni a office amma da sauri saboda ina son in saka mata sai inyi mata allura tayi bacci, kafin ta tashi an gama saka mata" ya juya har zai fita Daddy yace "doctor bara inzo ka dauki nawa, blood group din mu daya da ita, ban san ana bukatar jini ba da tuni na bayar. Ita da Hafsat group din mu daya su kuma boys din suka dauko na Mommyn su" Doctor yace "that's OK" ya fita.

Ummee ta mike tsaye, "NO Daddyn Moon, da shekarunka zaka bada jini bayan ga matashi yayi matching?" Ta kalli Ibrahim "ko kaine bakason ka bayar?" Still idonsa akan Sultan yace "it would be my honor to give my blood to her. But I think it is better a dauki na Daddyn kawai" Ummee ta sake cewa "why? Ji nake kai mijin sister dinta ne? Doctor yace blood din is clean, so why?"

A hankali Sultan yace "I don't want his blood in her" Ummee ta juyo tace "me kace?" ya maimaita da ɗan karfi "I don't want his blood in her" na rintse idona ina gode Allah daya kasance babu bare a gurin duk 'yan'uwa ne, ya Walid yace "Sultan, it is just blood. Babu abinda ake transferring a cikin jini in ba ciwo ba, kuma doctors sunce the blood is clean, don't make a case out of it please"

Sultan ya mike tsaye idonsa akan Ibrahim yace "it is not just blood, it is HIS blood, and that's what makes it different. I am her husband and I said ba za'a saka mata jininsa ba. I would rather buy it from a total stranger than take HIS. I don't even know what the FUCK he is doing here"

Idanuna a rufe naji karar mari, na saka hannu na na rufe fuskata, ba sai na kalla ba nasan wa aka mara kuma nasan wa yayi marin. Ummee ce ta mari Sultan. Shi aka mara amma ni naji zafin. Ummee ta fara fada muryarta har rawa take yi, na tabbata da zan iya kallon idonta da zan ga hawaye a ciki, tace "Sultan a gaba na? A gaban Daddy? I know you are spoilt but didn't knew you are this spoilt. Mijin kanwar matarka, yazo har asibiti ya dubata kuma yayi offering zai bata jininsa a saka mata amma ka zage shi? Wanne irin mutum ne kai?"

Daddy yayi magana "Khairat, Ibrahim is Moon's ex boyfriend, wannna shi yasa Sultan yake reacting this way" Ummee tace "dan yana tsohon saurayinta hakan bai kamata ace ya saka yayi treating dinsa this way ba. Karewar aure ji nake ɗa ta haifa masa ma yanzu. Shi kuma sister dinta ya aura. Menene kuma saura a ciki? Yanzu shi baiji kunyar ganin idonka ba? Baiji kunyar Amina ba? Ko da baya so ai da akwai hanyar da zai bi yace baya so ba sai yaci mana mutunci ba. Wannan ai mu ya wulakanta ba Ibrahim ba. Ina lura da Ibrahim din tunda ya shigo bai kalli inda Maimunatu take ba har ina tunanin me yasa haka ashe shi wulakanci yake gudu"

Fada Ummee take kamar zata ari baki. Sai da tayi shiru Ibrahim yace "am sorry. Ban zo da nufin creating trouble ba, na kawo Amina, muna tare da su Habeeb aka kira su gurin daukan jini, at first nace banda ni doctor din yana min wasa yace ina rowar jini ne, I didn't know it will match, I didn't want to create a scene shi yasa na bari aka dauka"

Daddy yace masa "it is OK Ibrahim duk mun fahimta and you don't have to explain your being here to anyone" ya fada yana kallon Sultan "It was just a misunderstanding. A bar maganar haka ta wuce" Ummee tace "ya kusa wucewa dai" ta kalli Sultan tace "tashi ka bashi hannu ku gaisa kuma ka bashi hakuri, sannan ka raka shi da kan ka gurin doctor a dau jinin kuma ka kawo da kanka a saka mata, that's your punishment for been arrogant"

Da sauri Ibrahim yace "No ma'am, that's not necessary. Na fahimci Sultan sosai kuma banji haushin sa ba. Idan nine nasan I might do something worse than what he did. Bana son a kuma samun wata matsala akaina."

Ummee tace "ba akan ka bane Ibrahim, akan sa ne, ina son yasan cewa idan yayi ba dai dai ba dole ayi punishing dinsa. So nake inga in an saka mata jinin ya zaiyi" ta juya tana kallon Sultan tace "tashi ka bashi hakuri nace"

MaimoonOnde histórias criam vida. Descubra agora