The Cook

10.2K 721 7
                                    

Ranar baƙin gidan mu suka zo yi mun sallama, daga 'yan 'yalleman har 'yan Niger duk washegari kowa zai tafi gida. Zuwan su ne ya saka na manta da hirar mu da Baba Gaji. Nan take 'yammata na suka fara hidima dasu, sun iya aiki sosai dan ba sai nace ayi abu ba zanga kawai anyi, da kyar na samu kebewa da Amina nace mata "Amina kin kira Ibrahim din kuwa?"

Ta dauke kanta ta bata rai tace "na kira shi ones, bai dauka ba ni kuma na rabu dashi" sai naji ba dadi a raina, it has been three days, ya kamata ace an san halin da yake ciki. Nace "please Amina ya zaki yi haka, gashi gobe zaki tafi and I don't know who else zan saka" ta daga min hannu tace "relax, ba tare zamu tafi dasu ba, Mommy tace in zauna anan for the time been" nayi ajjiyar zuciya nace "please Amina, kema kinsan ai ranar in kika kira shi ba zai dauka ba amma yanzu at least na san ya dan huce zai saurare ki" Ta kara tabe baki tace "I will try amma ban miki alkawari ba, in naga yana daga min kai I won't go around chasing him" na yarda a haka.

Sai bayan zuhr Sultan ya dawo, tun daga waje yaga motocin gidan mu dan haka sai ya zagaya ta baya ya shiga ta great room dinsa sannan ya kira ni a waya ya ce min ya dawo. Ina shiga palourn sa na ganshi a zaune ya kunna TV da remote a hannunsa, na tsaya daga bakin kofa nace "sannu da zuwa" ya juyo yana kallona sai ya nuna min cinyarsa yace "come here" na makale kafada, yace "to ni ma bana cin mike, bana amsa gaisuwa daga nesa" na karasa shigowa na rufe kofar nace "Sultan baƙi ne a gidan, in na zo nasan ba bari na zakayi in fita da wuri ba" ya bata rai yace "da ni da bakin waye yafi muhimmanci?"

Ban bashi amsa ba nace "amma ai su tafiya zasu yi ko? Sallama suka zo yi mana fa" yana kallona kasa kasa yace "OK, just a kiss, shikenan" na karasa gurin sa na tsaya, ya nuna min lips dinsa yace "here" na matso da fuska ta dai dai tasa, ina kallonsa har da lumshe ido wai shi nan za'a yi masa kiss, na cije shi kadan akan hanci na juya da gudu, ina jinsa yace "ouch, zan kama ki ne" na juyo nayi masa gwalo na fice.

Sai bayan la'asar baki na suka tafi, na koma gurin Sultan na tarar yana lunch din da na kai masa tun dazu, nace "au baka ci abincin ba sai yanzu?" Yace "bayan yau wulakanta ni kike yi dan kinga 'yan gidan ku ko? Tun dazu nake jiranki kizo muci abincin shine kika ki zuwa ko?" Na karbi cokalin a hannunsa nace "am sorry, ban dauka zaka jira ni ba, nasan halinka da abinci" na diba na fara bashi a baki, yaji dadin hakan sosai, na tambaye shi "how are the kids?"

Take naga fuskarsa ta haska da murmushi yace "they are fine, suna ta tambayarki, wai suna so su shirya mana surprise party" nayi dariya nace "then it is no longer a surprise tunda sun gaya maka" yace "kuma bayan gaya min din da akayi har list aka bani na abubuwan da suke bukata for the party" ya dauko wata takarda muka fara karantawa, tarkace ne nasu balloon da ribbons, har da cake, wai suna so a jikin cake din a rubuta 'happy married life mom and dad, we love you' muka yi ta dariya nan na kara abubuwan da basu saka ba.

Bayan Sallar magrib sai ga Hafsat da Zayed da little Khairat suma sunzo mana sallama zasu koma England. A palourn Sultan zauna dasu muna ta hira. Hafsat da tsegumi har bedroom din Sultan ta shiga, yace "Hey lady, me zaki yi min a daki ne? Baki san cewa bedroom dina sirrin mu bane ba?" ba tare data kalleshi ba tace "koma menene ba sirri ba sai na gani, nasan babu abinda zan tarar sai kazanta" ta shige ciki, ta dade kafin ta fito, knowing halin Hafsat nasan har toilet ta shiga, tana fitowa Sultan yace "kin dau bashi, duk sanda naje gidan ku sai na shiga dakinki" mu dai dariya muke musu ni da Zayed.

A nan Hafsat take gaya min in sun koma England Zayed zai dauki leave zasu je saudiyya, dan 'yan'uwansa da yawa basu santa ba ga kuma Khairat itama babu wanda ya santa. Tare muka yi dinner ina ta mamakin yadda Sultan yake sakewa da Zayed duk sanda suka hadu, dan yadda yake yi masa ko yaya Walid da suka saba sosai baya yi masa haka. Sai very late sannan suka tafi, ji nayi kamar zanyi kukan rabuwa da Hafsat tunda ban san kuma ranar da zamu sake haduwa ba in dai ba wani abun ne ya tashi ba.

MaimoonWhere stories live. Discover now