All of you

8.3K 627 10
                                    

Yana gama fadin haka ya ficewarsa ya barni. Naje nayi locking kofar amma a raina ina cewa wannan ai bonono ne rufe kofa da barawo. Na dawo na kyara inda muka ci abinci sannan nayi shirin kwanciya, ranar sam na kasa bacci saboda rashin sabo da sabon gurin, kawai na tashi nayi alwala na yita salloli ina rokon Allah ya bani karfin zuciyar da zan iya controlling Sultan shi kuma Allah ya shirya min shi, na tuno da maganar Amira da tace am too soft and Sultan is too hard, in dai har ina so in gyara masa rayuwarsa dole nima in zama hard amma how? I have been soft tunda nazo duniya how can I be hard kuma yanzu?.

Washegari muka fara aikin da ya kawo mu tukuru, aikin shine koyon yadda ake raba twins din da aka haifa kan su a hade, yadda kowanne daga cikin su zai rayu physically independent of the other. Kullum wuni muke yi a lab sai yamma likis sannan zamu dawo, kuma kullum muna dawowa zan tarar da abinci Sultan ya ajiye min, wani lokacin ma har da ruwan zafin wanka, sai yanzu na fahimci dalilin da yasa ya dauki spare key dina kuma inajin dadin yadda yake kula dani sosai, saboda badan shiba gaskiya zaman zai yi min wahala sosai, fita siyan abinci kawai sai ya isheni. Wani abin mamakin shine duk da cewa ni kadai nake zaune yanzu amma Sultan har yau bai taba kai hannunsa jikina ba, ko wani abu zai bani baya barin hannayen mu su hadu, na jinjina masa ta nan gurin sosai dan ba ko wanne namiji ne zai iya haka ba, wani lokacin har tunani nake "to ko he is not attracted to me?" Amma kuma in na kalli idonsa ina gani a ciki, wani lokaci har bana son hada ido dashi saboda irin abubuwan da nake karantowa a ciki, abinka da psychologist, lol.

Watan mu daya a America wani aiki ya taso wa Sultan wanda ba zai iya yi tanan ba sai lallai yaje Nigeria, ji nayi kamar zanyi kuka har sai da ya gane yace to ya fasa tafiyar sannan na hakura. Kafin ya tafi sai da ya bada order a restaurant din da yake siyo mana abinci cewa kullum zasu ringa kawomin safe, rana, dare babu fashi. Yana tafiya muka dinke a waya, kudin da Sultan ya kashe a saka credit daga tafiyarsa zuwa dawowarsa Allah ne kadai yasan yawan su. Satinsa biyu acan ya dawo amma ji nayi kamar wata biyu yayi. Yana dawowa ya shiga lodo min siyayya yana ajiye min wai tsarabar da zan kaiwa 'yan gidan mu, nace "Sultan wannan uban kayan ya zanyi in tafi dasu?" Yace "shipping dinsu zanyi miki ai" na sake cewa "to yanzu in naje dasu gida ince da Mommy a ina na samu kudin saye?" Na danyi tunani kadan sannan yace "tell her you won the lottery or something" kawai na saki baki ina kallonsa, shi a ganinsa wannan is a total excuse, shi bai saba in yayi abu a tuhume shi ba dan haka bashi da idea yadda za'a yi wa iyaye karya. Haka yayi ta lodo kaya yana jibgewa.

Sati daya ya rage mana mu dawo England, duk ayyuka sun yi mana sauki dan kusan zan iya cewa mun kammala, ana koya mana ne yadda za'a kula da twins din ana monitoring dinsu har su warware. Sai lokacin Sultan ya samu damar fita dani yawon ganin gari, ai kuwa nasha gararamba lungu da sako na New York sai da ya shiga dani. A lokacin ne ya kaini gidan sa ya nuna min. Tun sanda yace min can zamu je na kudurta a raina cewa bazan shiga ba, muna zuwa yayi packing ya zagayo ya bude min kofa naki fitowa, ya tsaya yana kallona "ko sai na fito dake ne?" Nace "no kawai dai bazan shiga bane" in yayi mamaki ma ya boye bai nuna min ba yace "ohh really? Duk zirga2 da nake yi gurinki ke ko shiga ki saka min albarka a gida na baza kiyi ba? Thanks a lot" wani barin na zuciyata yace min 'he is trying to control you, don't give in' na daga kafada nace "sorry, kawai dai naga kamar shiga gidan ka is way ahead of limit" shima kafadar ya daga yace "if you think so, amma matsalata guda daya ce, what I plan is in munzo nan zan barki anan zanje wani guri in karbo sako a gurin wani wanda gobe zai bar gari kuma gurin da zamu hadu is no place for a lady especially lady din da ba zata iya shiga gidan fiancé dinta ba" na daga masa hannu nace "wait, technically kai ba fiancé na bane yet" yayi murmushi tare da jingina da jikin motar yace "OK, yanzu ya kike so ayi?" Na kalleshi ya langwabar da kai side daya, na dauke kai a zuciyata ina cewa, don't fall for that, ya sake zagayo wa ta side din dana mayar da fuskata yace "na rasa me yasa har yanzu kin ƙi trusting dina, if I want something da tuni na karba, you are too precious for that, I just want you to see my house, nan shine inda na zauna for thirteen years, tun ina twelve years nake rayuwa a gidannan har na kai twenty five years"

MaimoonWhere stories live. Discover now