Brave Heart

8K 661 17
                                    

Hannu na saka na murza ido na, ni dai nasan ba bacci nake ba ballantana in yi tunanin ko mafarki nake, idonsa yana kaina kamar yadda nawa yake kansa. He looked different, but it was still him. Ya rame shima. Ban taba ganin sa da manyan kaya ba maybe shi yasa naga ya kara chanzawa, but by God he looked more handsome than ever.

Kamar in ruga da gudu in taba shi dan in tabbatar ba hallucination nake ba. Muryar Daddy naji kamar daga sama yace "Sultan, da kai nake magana fa" yayi sauri ya dauke idonsa daga kaina tare da sunkuyar da kansa kasa yace "sorry Daddy" sannan ya zaro wayarsa yayi dialing ya saka a kunne "kana ina ne? Daddy fa har ya fito, kayi sauri" ya kashe.

Muryarsa ce, so it is really him. Ya bude wa daddy kofar baya, bayan Daddy ya shiga ya gyara masa rigarsa sannan ya rufe. Yana rufe kofar ya juyo ya sake maida idonsa cikin nawa, with all my psychology amma a lokacin kasa reading dinsa nayi, so clouded. Daddy ne ya sauke glass dinsa yana kallon Sultan sannan ya kalleni, wannan karon nice nayi saurin dauke idona na sunkuyar da kaina sannan kuma sumi sumi kamar munafuka na tafi motar da naga Mommy ta shiga, na zauna a baya a kusa da ita. Ta window na cigaba da kallonsa duk da yanzu bana ganin fuskarsa, bamu jima ba naga yaya Walid ya taho da dan gudun sa ya shigo gaban motar da muke ciki, ina kallon Sultan ya bude gaban motar da Daddy yake ciki ya shiga.

Tunda muka fara tafiya babu wanda yayi magana, can Mommy tace a hankali "yana motar Daddyn ku ko?" Ban fahimci me take nufi ba kuma nasan ba dani take magana ba shi yasa nayi shiru, ya Walid ne ya amsa "yes, Mommy" tayi kwafa tare da dafe kanta. Ina son in tambaye su maganar wa suke yi saboda in tabbatar wanda na gani shi dinne dai ba wani ba, amma kuma bazan iya ba. Na runtse idona ina so in fahimci me yake faruwa. Wata na uku da sati biyu rabona da Nigeria amma ji nake kamar wadda nayi shekara daya. Me Sultan yake yi tare da Daddy na? A iya sanina ko haduwa basu taba yi ba. Me ya faru bayan tafiya ta?

Kafin Moon ta samu amsarta mu bara mu koma baya mu riga ta sani.

Nigeria bayan tafiyar Moon

Walid da Habeeb suka bi bayan motar Mommy da kallo. Walid ya juyo ya kalli Habeeb yace "ina zasu je?" Habeeb ya daga kafada yace "oho, nima kawai ganin su nayi suna shiga mota" Walid ya kalli agogon hannunsa, 7 ma bata yi ba, where can they possibly go to at this hour? Jikin sa dai bai bashi dai dai ba. Yace "OK, mu jira su su dawo kawai" ya juya ya koma ciki.

Sai around nine mommy ta shigo gidan ita kadai, babu Moon babu Daada, a palo ta same su suna breakfast, ta shige ciki, har ta shirya ta fito suna palon, ta zauna tana hada tea, Habeeb yace "Mommy ina su Moon suka tafi ne da sassafe haka?" Ba tare data kalleshi ba tace "inda ka aike su nan suka tafi" daga nan babu wanda ya kuma cewa komai, daya bayan daya suka mike suka bar palon, tabi bayan su da harara.

Tana gamawa ta shirya ta tafi office. Sai karfe biyar ta dawo, tana yin packing wayarta tana yin kara, ta duba screen din 'Dear' tayi ajjiyar zuciya, tasan maganar dai, tun jiya maganar daya ce, tasan dole zatayi facing wannan challenge din but she is ready. Moon is weak, too soft, tun da aka haife ta haka take, she trust too much, love too much and gives her all in everything she do, she is her father's daughter, shima haka yake, dan haka ita Mommy dole ta zama strength din su, ba zata taba barin wani ya yi taking advantage of her sweet daughter's innocence ya cuce ta ba, not that so called Sultan and not that stupid Munir.

Ta fahimci plan din Munir, so yake a tilastawa Moon ta aure shi, ita kam ba zata taba barin ayiwa 'yarta auren dole ba musamman da mutun kamar Munir, over her dead body, abinda yayi recently ya tabbatar mata da ba son Allah da annabi yake yiwa Moon ba, idan da ace yana sonta da ko ita data haife ta ba zata san abinda ya gani ba.

Kiran ya sake shigowa wayarta, tayi taking deep breath sannan ta dauka, "hi dear" da sauri ya amsa sannan yace "ina kika shiga ne haka? Wajen five missed calls?" Ta danyi murmushi tace "kasan aiki yayi min yawa tunda na dawo dinnan. Ina office ko wayar ma ban samu damar dubawa ba sai yanzu na dawo gida. Ya kake?" Ya danyi murmushi "am fine Mommyn kids, busy body, ya kuke?" "Lafiya lau, just missing you" "wai Moon har yanzu wayarce bata gyaru ba? Tun shekaran jiya rabon da muyi magana da ita. Please in tana kusa bata wayar" ta shirya abinda zata ce masa dama "bata gida yanzu, kafin in fita dama tace zata je gidan su Amira, yanzu na tarar bata dawo ba, nima bana son rashin wayar tata amma tace she is taking a time off....." ya tare ta "ba wani time off, tell her in ta dawo na turo mata kudi taje ta siyo wata wayar, and also tell her to call me ASAP" tayi dariya sosai tace "to Daddy, an gama" shima dariyar yayi, suka dan taba soyayya kadan ta kashe.

MaimoonWhere stories live. Discover now