The Wedding Night

10.9K 890 8
                                    

Mun jima muna tattaunawa akan abinda ya faru, anan ne Hafsat ta bawa Amina labarin alakata da Ibrahim, yadda Amira ta raba mu da kuma labarin rayuwar Sultan, tace ta gaya mata ne dan tana son ta fahimci abinda ya faru sosai, kuma tana fatan cewa maganar zata tsaya a tsakanin mu, Amina duk jikinta yayi sanyi ta kasa maganar kirki.

Na rike hannunta nace "Amina, sam yanzu bana yiwa Ibrahim soyayyar aure, amma still ina jinsa a raina kamar dan'uwana haka nake jinsa. Na tausayawa rayuwar da yayi bayan rabuwar mu kuma ina tausayin halin da yake ciki a yanzu. He thinks he is doing a good thing. He thinks I am in trouble. He needs an explanation. He needs to know the whole truth. Dan Allah Amina ina son kiyi reaching out to him kiyi masa bayani yadda zai gane sosai cewa ni na zabi Sultan duk da halayensa. Kiyi masa bayanin cewa Sultan is not as bad as people think he is. Ki bashi duk wannan labarin da muka baki yanzu ki gaya masa cewa na auri Sultan saboda ina sonsa, saboda ina ganin soyayyata zata kawar da duk wani mugun hali nasa, kuma so far I have succeeded. Ki gaya masa kyaleshin da Sultan yayi yau alama ce ta cewa he is no longer who he was before" tunda na fara magana Amina take girgiza kanta alamar ba zata yi ba, ni kuma ban daina maganar ba har saida nazo karshe, tace "No, Moon, bazan iya ba, ba zai saurare ni ba, yaudara ta fa yayi ya saka na shigo dashi har cikin gidan ki" na kara rike hannunta nace "please Amina, you are my only hope akan sa, duk da yadda nake son in taimaka masa ba ni da yadda zanyi sai ta hanyarki kadai, please help me as your sister" da kyar na samu tace maybe zata yi in ta huce saboda taji haushin using dinta da yayi.

Muna cikin haka Amir ya dawo yace Amina tazo ta taya shi su kwashe abincin partyn da ba'ayi amfani dasu ba, wadanda ba zasu lalace ba suka shiga dasu suka adana, wadanda kuma zasu baci Amir ya aika dasu cikin gida. Ni da Hafsat kuma muka shiga ciki muka koma cikin bedroom dina muna cigaba da jajantawa, kafin su Amina su gama sai around 12:30, dan haka dole kwana ya kamasu a gidan.

Hafsat ta kira zayed wanda tunda yazo bikin ya kama hotel, kullum da daddare yake lallabowa ya dauke matarsa sai da safe yake dawo da ita, ta gaya masa zata kwana a gida na saboda dare yayi. Sai da duk mu kayi wanka muka yi shirin kwanciya sannan naga sun tashi suna yi min sallama wai wani dakin zasu tafi su kwanta. Nace "saboda me?" Hafsat ta harare ni tace "oho miki, yau ne fa first night dinki, kawai kuma sai muzo muyi dare dare akan gado? In angon ya shigo kuma fa?"

Na kasa basu amsa har suka fice. A raina nace "wannan angon nawa ai Allah ka dai yasan inda yake" nayi tunanin in kira wayarsa inji ina yake amma kuma kar ya dauka wani abin nake nema. Na kwanta ina kallon dakina, karshen kyau yayi kyau, babba ne sosai dan duk girman gadon baifi quarter din dakin ba, babu ce kawai a kayan da ake bukata a daki Daddy da Mommy basu saka min a dakina ba. Komai yaji, komai da akwai except ango. Ina Sultan ya tafi?

Na gyara nayi kwanciyata duk jikina yana yimin ciwon gajiya amma sam babu bacci a ido na, nafi 30 minutes a haka sai kuma na mike zaune na jawo wayata nayi dialing number dinsa, switched off, yayi fushi, nasan he has the right na yin fushi dani amma abinda yafi damuna shine abinda zai aikata a cikin fushin nasa, ya Ilahi give me the strength. Number din Amir na lalubo na kira, bugu daya ya dauka da alama bai kwanta ba, sai kuma na rasa mai zance masa, yace "Moon baku kwanta ba? Ko akwai abinda kuke bukata ne?" Nace "amm babu komai, dama ina son inji ko Sultan yana tare da kai ne?" Yace "No, ban ganshi ba, na dauka kuna tare ai" nace "a'a ai tunda ya fita bai dawo ba" na dan yi jim sai kuma yace "OK bara in duba shi" na zauna akan gado na harde kafata ina jiran tsammani, can Amir ya kira ni yace "naje har gate na tambaya sunce bai fita ba, kuma naga duk motocinsa da suke gidan nan suna nan, yana cikin gidan, kin duba part dinsa?" na girgiza kai kamar yana kallona nace "a'a ban duba ba" yace "ok, ki duba can" nace "to na gode" sai kuma yace "Moon, he will be alright, Sultan is a tough guy, ya fuskanci abubuwan da suka fi wannan kuma yayi surviving. Idan kin duba baki ganshi ba just kiyi baccin ki, let him be, mostly in yayi zuciya yana rufe kansa a wani gurin ne ya zauna shi kadai har sai ya huce, you will be surprise in yazo zaki ga kamar ba'ayi komai ba" na ce "OK, thank you Amir, really thank you, for everything" yace "you are welcome".

MaimoonTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon