Friends

7K 613 3
                                    

Washegari tun kafin assuba na tashi nayi wanka na saka uniform dina, assuba tana yi na tafi masallachi nayi sallah daga nan na wuce islamiyya. Nayi haka ne saboda bana son muyi rigima da Hafsat. Har muka fara karatu Hafsat bata zo ba. Amira ta tambayeni ina Hafsat na daga mata kafada alamar I don't know, har aka tashi daga islamiyya babu Hafsat babu labarinta, sai na ringa jin babu dadi a raina, what if she is sick? Na taho na barta. Ana tashi na kira Amira nace mata please tayi checking on Hafsat, ni class zan wuce bana son komawa hostel, tace min ba problem. Ina yin breakfast na wuce class na zauna ina karatu na har aka fara zuwa class. Karatu nake amma duk hankali na yana kan masu shigowa ina jiran inga shigowar ta. Can sai gata ta shigo fuskar nan babu alamar fara'a, tana zama na mike na tafi wajen ta nace "Hafsat lafiyar ki kuwa yau ban ganki a islamiyya ba?" Tayi min kallon sama da kasa tace "what is it with you idan ban je islamiyya ba? Ko zaki saka shi yayi min bulalar fashi ne?" Nayi murmushi nace "that settled it, dama ina ao in san lafiyar ki, na fahimci kuma lafiyar ki kalau" na koma nayi zama na. Ina zama sai ta mike ta kama jan seat dinta sai da ta kai shi can row din baya sannan tayi zamanta.

Sam bana jin dadin abubuwan da Hafsat take yi amma kuma bana son in bata chance din da zata ke controlling rayuwata. Farko Ibrahim ya fara kulata yana tsokanar ta da big sister amma sai ya lura cewa bata so dan haka ya rabu da ita. Rannan muna karatu ya tambayeni "how is your sister" nayi mamakin tambayar amma na maze nace "she is fine" he snickered kafin yace "she hates me" na ajiye rubutun da nake yi nace "no, she doesn't hate you, she has always been like that dama, believe me sometimes I feel like she hates me too" daga nan bai sake yi min maganar Hafsat ba.

Bayan munyi wata daya da fara term din su mommy suka zo mana visiting. Tun da aka kira mu gaba na yake faduwa dan bansan me Hafsat zata kulla min a gurin mommy ba. Muna tafiya zamu je gurinsu na matsa kusa da Hafsat nace mata "what are you planning to tell Mommy?" ta kalleni da murmushin mugunta tace "that's my business, me kike ci na baka na zuba?" na hadiye yawun tsoro cikina ya kulle kamar zanyi zawo a wando amma na daure na cigaba da binta a baya ina ɓuya a jikinta kamar munafuka.

Muna zuwa visitors room sai muka tarar da Daada da faruk, nan da nan na manta da damuwar da nake ciki na fada kan cinyar Daada ina murnar ganinta, Hafsat ma tazo ta rungume ta muna ta dariya, Daada tace da yaren buzanci "kai ni kar ku ji min ciwo, ku baku san kun zama 'yan mata bane" nace mata "haba Daada, ina abin yake? Sai dai ki gaya wa Hafsat bani ba" Hafsat kuma tace "ai komai girman da zanyi bazan daina hawa cinyar ki ba Daada" muka sake yin dariya. Faruk yana zaune yana kallon mu nace "autan mommy ko magana babu?" Yace "au kuna gani na? Na dauka ai ni invisible ne tunda babu wacce ta kula ni a cikin ku" nan kuma muka tafi da gudu a tare muka rungume shi yana ture mu wai yayi fushi.

Hafsat ce tace Daada wai ina Mommy ne?" Daada tace "muna zuwa principal dinku ta kira ta" nan take wani gumi ya karyo min, tunda muka shigo ban ga Mommy ba na dauka bata samu damar zuwa ba har hankali na ya kwanta. Nayi saroro har wani daci nake ji a baki na. Hafsat ta dafa ni tace "yayane Moon? Ko bakya murnar ganin Mommy ne?" na ture hannunta na koma kusa da Daada ina tambayar ta su ya Habeeb. Muna cikin haka sai ga messenger daga principal's office wai ana kiran mu ni da Hafsat. Muka tashi muka tafi, nice a gaba Hafsat tana bina. Ina tura kofar office din naga Mommy a zaune a kujerar gaban table din pc daga can gefe kuma Ibrahim ne a zaune yayi folding arms dinsa yana kallon Mommy.

Sandarewa nayi a gurin na kasa motsi, komai nawa ya tsaya hatta bugun zuciya ta. Hafsat naji tana fadin in matsa in bata guri ta shigo tunda ni bazan shiga ba. Sai a sannan numfashi na ya dawo sai kuma zuciyata ta fara bugawa da karfi, dacin da nake ji a baki na ya karu, Hafsat ta karewa office din kallo sannan tazo dai dai kunnena tace min "whatever goes up must come down" tana yi min murmushin mugunta ta shige ciki da sallama. Ba yadda zanyi dole na bita a baya. Ga mamaki na sai naga Mommy ta juyo da fara'a sosai a fuskar ta ta mike tsaye ta buda hannayenta tare da cewa "come here my darlings" ban san sanda na manta da komai ba na fada jikin Mommy ina murna. Ta rungume mu sosai a jikinta na wani lokaci sannan ta sake mu, muka gaishe ta, muka gaida pc sannan na juya na gaida Ibrahim. Hafsat ko kallon inda yake bata yi ba Mommy kuma bata lura ba dan suna magana da pc a lokacin.

MaimoonWhere stories live. Discover now