The Past And The Future

9.8K 697 8
                                    

Na jima a haka ina kuka mai tsuma zuciya, jikina har rawa yake yi. Why is my life always so complicated, me yasa komai ni baya zuwa min da sauki. I hate hurting Ibrahim. Ya sha wahala sosai akan soyayyata, he deserves happiness from me now, but I can't give it to him because it is not mine, it belongs to somebody else. Lallai kaddarar rayuwa kowa da irin ta sa.

Ina jin wayata tana ta ringing, kira na wajan goma kenan, amma ba zan iya dauka ba saboda ba zan iya magana ba. Da zuciya ta da kaina gabaki daya sun toshe kaina sam babu wani abinda yake fahimta, abinda nake tunawa shine naga Ibrahim, kuma soyayyata da na gani a idonsa ta ninka wacce na san yana yi mini a da kafin mu rabu. A hankali na fara abinda na saba yi indai ina so in saisaita tunani na, na fara kiran sunayen Allah daya bayan daya idona a runtse, a hankali nutsuwa ta fara shigomin kuka na ya fara tsayawa. Na bude ido na ina kallon titi, gari ya fara duhu dan tuni anyi sallar magrib. Na fara tunani straight. So Ibrahim did came back like he promised he would. Yanzu kuma saura kwana goma bikina, bikina da Sultan. Ibrahim har yanzu yana so na, yana sona fiye da yadda ya soni a baya. But ya dawo rayuwata a little bit too late. My heart already belongs to another. I loved him before. Nayi masa son da a lokacin nake tunanin ba zan taba yiwa wani irin sa ba. But it is all gone now, abinda ya rage a zuciyata a game da shi shine respect and good wishes. Sultan ya cike dukkanin guraben da suke a zuciyata.

Ibrahim yace Allah ya hada mu ne a yau saboda we have a future together, in haka ne kuwa to ba zabi na bane kenan. Even if da akwai sauran son Ibrahim a raina to yana can kasan zuciya ta wanda tono shi sai an dauki lokaci, and time is what we don't have. Even if an tono soyayyar Ibrahim a raina ta yaya zan iya facing iyayena ince musu na fasa auren Sultan wani kuma daban nake so? Wanin kuma da a baya na gaya wa Daddy cewa he is not serious akan magana ta. Komai sanyin Daddy na tabbatar sai naga bacin ransa ballantana Mommy da inajin sai ta kaini psychiatric hospital.

I couldn't even imaging tunkarar Sultan da maganar wai na fasa aurensa saboda wani tsohon saurayina da muka rabu kusan seven years back. Duk wanda yaje ya gaya wa Sultan wannan maganar will be like committing suicide. I couldn't even imaging my life without Sultan. Kamar yadda Ibrahim ya fada hakane, God have reasons for everything He did. Tunda Allah ya hada mu yau to da akwai wani abu daya boye a cikin haduwar tamu, ko da kuwa ba aure bane. I just hope that whatever God has planned for us zai kawo happiness a rayuwar Ibrahim sannan kuma ba zai wargaza rayuwa ta da Sultan ba.

Waya ta ta cigaba da ringing, na dauka ina kallon sunan Sultan har ta katse, a cikin dictionary din Sultan babu wata kalma wai ita giving up, he never gave up, yanzu kiran nan da ya ke yi min zai yi ta yi ne har sai na dauka ko kuma sai charging wayar ya kare. Na duba missed calls naga 23, amma 5 daga Mommy ne, sauran kuma nashi. Na fara tunanin abinda zance musu tunda duk cikin su babu wanda zan iya gayawa gaskiyar abinda ya faru yau. Mommy na fara kira, bugu daya ta dauka tace "ina kika shiga? Sai da nace muku fa kar ku kai magrib gashi har after seven baki dawo gida ba?" A nutse nace "Mommy mun dan samu matsala ne shagon, Amira ce suka dan samu sabani da wata cashier shine abin yayi delaying din mu, kuma nabar wayata a mota shi yasa ban san kuna ta kira na haka ba" ta dan rage fadan da take yi tace "to amma ai da ko wayar ita Amiran sai ki karba ki kira ki fada mana halin da kuke ciki, ni ba sai inzo da kaina ko in turo wani yaji matsalar da aka samu ba? Na kira wancan yaron ma yace shima yana ta kiranki baki dauka ba, duk kin tayar mana da hankali wallahi" na danyi murmushi a raina nace 'I love you too Mommy' nace "gani nan zuwa yanzu, zan kai Amira gida ne kawai in taho" da sauri tace "NO, duhu yayi kuma unguwar su Amira akwai nisa. Ku tsaya a inda kuke ki kira shi yazo ya same ku sai ya kai ku ya dawo dake gida" nace "yes mother" na kashe.

Ina katsewa kiran Sultan yana shigowa, sai da nayi bismillah sannan na dauka, ina dauka yace "damn it! where have you been?" Cikin sanyin murya nace "am sorry Sultan, na manta waya ta ne a cikin mota, muna cikin wani supermarket ne kuma muka samu wata 'yar matsala, but everything is Ok yanzu na kai Amira gida zan taho gida nima" kamar sun hada baki da Mommy yace "no, ki zauna a gidan bara inzo in dauko ki, dare yayi kuma hannunki bai yi kwari ba" nace "yes sir" ya sauke ajjiyar zuciyar da har sai da naji ta ta cikin wayar yace "you almost gave me a heart attack. Gaba na yana ta faduwa, kuma ina ta kiran wayarki tana ta ringing baki dauka ba. Please don't ever do this again in ba so kike zuciya ta ta buga in mutu ba" kalmar mutuwar da ya fada ce ta saka ni nayi murmushi nace "kar ka zama ragon maza mana, ko three hours fa ba muyi da waya ba" yace "anything can happen ai a cikin three hours din, kin san babu abinda ban aiyana a raina ba? Har sai da na hango ki a kasan tirela" nayi dariya, yace "yanzu shikenan date din na mu ya wargaje? Har nayi musu waya nayi mana reserving table" nace "am sorry, in sha Allahu I will make it up to you. Yanzu Mommy tana can tana jirana in muka tafi fada zata yi. Insha Allahu zan lallabata ta sake bari na fita sai muje" ya shagwabe murya yace "baki ga kwalliyar da nayi miki ba fa" nayi murmushi nace "really?, show me, I want to see" yace "how?" Nace "kayi snapping picture ka turo min yanzu" yayi dariya yace "no, it is kind of special, in kina so ki gani sai dai kisan yadda zaki samar mana fita da wuri. Yanzu cirewa zanyi ma in boye" mukayi sallama yace gashi nan tahowa.

MaimoonWhere stories live. Discover now