The Wedding

8.2K 663 3
                                    

Six days to....

Duk an gama shirye shirye. 'Yammata ana ta rigima da tailors din da basu gama dinkuna ba, ni kam duk kayana sun kammala kuma suna dakin Sultan, nace ya barsu a can saboda cikin gidan duk a hargitse yake kar inzo in rasa wani abun ranar da nake bukatar sa.

Wajan 12 na rana aka ce inzo nayi baki a palour, na sauko na ga 'yammata su uku a zaune, already an riga an cika musu gaban su da kayan ciye ciye, ban gane ko daya daga cikin su ba amma daga ganin su kasan 'ya'yan manya ne, biyu bakake daya fara, amma jikina ya bani cewa farin mai ne. Na zauna da murmushi na ce musu "sannun ku da zuwa" kallo kawai suka bini dashi sannan suka kalli juna, sai suka sake kallona, daya daga cikin su tace "Amaryar ta mu ce?" Na sake murmushi nace "sunana Maimunatu" suka sake kallon juna sannan dayar tace "eh haka muka gani a jikin IV. Ita din ce kuwa. But you are younger than we expected. An ce mana medical doctor ce"

Nayi dariya nace "I am a neurologist and also a psychologist. Karatu ai ba shine shekaru ba, in dai ka fara da wuri shikenan" bakaken biyu suka yi dariya, daya tace "sunana Fa'iza, wannan kuma kanwata ce Saratu. Mu kannen ki ne" ban gane ba, tace "if you know you know" sai yanzu na fahimta, kannen Sultan ne, he never talks about them kamar basu yi existing ba.

Na kara fadin murmushi na nace "sai yau kuka tuna dani? Nayi fushi" Saratu tace "sorry big sister, ba laifin mu bane, mu bamu san ma dake ba sai kawai IV aka kawo mana, ko ince sai IV muka gani, dan mu yaya Sultan ko gayyatar mu bai yi ba, maimakon ace mune masu gayyata ma amma sai a gari muke ji" nace "to kusha kurumin ku, har sai kun gayyaci wasu ma" suka yi dariya, nace "and who do we have here?" Na nuna wacce suka zo tare, Fa'iza tace "antin mu ce, Ummukhulsum" ban nuna komai a fuskata ba nace "sannu da zuwa aunty" da alamar tsokana, ta bata rai tace "in kika ce min aunty ai sai ki mayar dani kamar tsohuwa" muka yi dariya.

Bayan sun dan motsa bakin su na tafi dasu sama dakina, har bayan azahar suna nan, tare mukayi lunch dasu, kowa sai da na nuna masa kannan Sultan. Ina lura dasu suna ta kallon gidan, ni kuwa nasan ba 'ya'yan sarki ba, ko 'ya'yan waye karya suke su kushe mana gida. Tunda suka zo suke ta yi mini tambayoyi akan Sultan, wai yana dariya kuwa? Har da tambayar is he romantic, nace sosai kuwa. Around 3pm aka zo aka dauke su, na hada musu kayan kyalliya masu tsada da turaruka na basu tare da katinan kowanne event na bikin.

Na koma gida nayi wanka na shirya, nayi sallar la'asar aka sake cewa nayi bako kuma, na sako hijab dina na fito ni da Amina, a tsaye muka ganshi a jikin motar sa. Yayi kwalliya kamar babu gobe. Daga ganin sa kasan hutu ya zauna masa. Ina ganin da na gane shi. Abbas ne, muka karasa muka gaishe shi ya amsa yana tsokanar mu "wacce ce yayar tawa ne a ciki?" Na nuna Amina, yace "to tunda kika nuna ta ke ce" muka yi dariya yace "ya shirye shirye?" Amina tace "Alhamdulillah' nayi kokarin a kaishi part din su ya Habeeb amma yace sauri yake, yace karar Sultan ya kawo min, wai bai saka shi a cikin harkar bikin ba kwata kwata, shida ya kamata ace shi yake organizing bikin amma sai dai yake gani ana yin abubuwa babu shi, nayi masa alkawarin zanyi wa Sultan magana akan hakan.

Ya sake cewa "sai magana ta gaba, ina so in shirya masa hawan angwanci a matsayin wedding gift dina amma yace baya so, ni ban taba ganin inda akayi bikin dan sarki babu hawan angwanci ba" na jinjina maganar, nasan Sultan ba zai yi ba, tunda yake babansa bai taba hawan sallah dashi ba, kuma ko a magana ban taba jin yana maganar yin hawan angwanci ba, da yana so kuwa da zai ce zaiyi. Nace masa "insha Allah zanyi masa maganar shima, amma babu guarantee zai yi, in ba zai yi ba kawai ka rabu dashi", ya daga kafada yace "it's OK, ina son kuma cards saboda friends dina" na tura Amina ta dauko masa da yawa ta kawo masa. Shima muka yi sallama ya tafi.

Da daddare Sultan bai samu zuwa gida da wuri ba saboda friends dinsa na America da suka zo, yana can nema musu masauki da entertaining dinsu, dan haka bamu hadu ba sai waya mukayi. Na gaya masa bakin da nayi yau da yadda muka yi dasu duk, yace "what? Munafukan yaran nan karya suke yi, babu abinda ban basu ba, su dai kawai tsegumi suka zo yi" nayi murmushi nace "it is OK ai. Tom Abbas kuma yace ka ki sakashi a organisers" yace "Abbas ba zai iya organising komai ba, bai san ni ba bai san me nake so da wanda bana so ba, role din Amir yake so in bashi kuma bazan bashi ba" nace "but at least involve him in something, tunda ya nuna yana so karka sace masa guiwa" yace "Moon baki san halin yaron nan bane ba. But whatever, zan gaya wa Amir in da akwai wani abu ya bashi. Zancen hawan angwanci kuma bazan yi ba, I already told him bazanyi ba, he is trying me" jin ya fara daukan zafi nayi shiru, sai da naji ya huce nace "tell me something nice" daga muryar sa kadai nasan ya ware yace "what's nice without you. Sai yanxu nake nadama big wedding din nan, da na sani kawai daurin aure akayi aka kaimin amaryata" nace "tukunna ma, sai jibi in an fara ido zai raina fata" yace "ohh jibi za'a fara ko? Gaskiya ya kamata gobe ki san yadda zakiyi maganar date din nan. I really want to see you wallahi" nace "insha Allah tomorrow zamu fita. Kar ka manta da kwalliyar da ka yi min alkawari, I want to see it" yace "baki da problem. Thanks , Love"

MaimoonWhere stories live. Discover now