Ya Habeeb

8.2K 615 3
                                    

"What?" Ya tambaya da mamaki, ban maimaita tambayata ba sai ruwa dana zuba a cup na mika masa, bai karba ba, na ajiye a gabansa. Ya sake tambayata "me kika ce?" Na kalle shi cikin ido nace "cewa nayi me yasa kake shan giya?" ya bata rai sosai yace "who told you that?" Nayi shiru ban kalle shi ba, can yace "damn it, it's Steve, isn't it?"

Nace "tun kafin muyi magana da Steve na sani" ruwan dana ajiye masa ya dauka ya shanye sannan ya mike ya bar dining area din ya koma cikin palourn, nima na mike na bi bayansa, na zauna kujerar kusa dashi. Jin bashi da niyyar yin magana yasa na sake cewa "baka ce komai ba fa?" Ya juyo yana facing dina ya wani bata rai yace "can we please just drop this? I really don't want to talk about it now" nima na bata rai nace "why not? I think this is the right time to talk about it. Sai bayan anyi bikin mu tukunna zamuyi maganar? Look Sultan da ace zan rabu dakai saboda kana shan giya da tuni na rabu da kai, amma ba wai hakan yana nufin nayi na'am da dabi'ar ba, ina dai saka ran cewa zaka daina. Nayi maka maganar ne yanzu saboda naga har mun fara maganar zuwan ka gurin Daddy dan haka ya kamata duk wani personal issues din mu muyi solving" na dan yi shiru ina studying dinsa, he looks really disturbed, ya saka duk kan hannayensa a cikin gashin sa, na cigaba "nasan kusan 70% na troubles dinka with the police are related to your drinking habit, saboda fadar annabi ne cewa ita giya itace shugabar dukkan alkaba'i, zata iya saka mutum yayi sata, zina, har ma kisan kai. Sultan zanyi tolerating komai akan ka amma banda drunk husband, what if one day ka dawo a buge kayi min duka?"

Da sauri ya kalloni idonsa kamar zaiyi kuka yace "I will never hurt you" nace "you can't be sure, duk sanda kasha you will loose control of yourself, maybe ma ba zaka gane koni wacece ba" alamun bacin raine karara a fuskarsa yace "please ki daina wannan maganar mana, wai what has come over you ne today? Ke fa baki san komai akan maganar nan ba kuma banyi niyyar ki sani ba har abada, yadda kika dauki abin sam ba haka yake ba. Amma na miki alkawarin one day zamuyi maganar but not today. You have no idea what I was going through kafin in hadu dake, and you also have no idea how much I have changed bayan na hadu dake" nace "na yarda, I don't understand and I may never understand. Ni yanzu dai please so nake kayi min alkawari guda daya. Promise me that you will never touch alcohol again" ya jingina da jikin kujerar ya zubo min idanuwansa, ina kallo yadda yake relaxing a hankali sannan yace "I will do anything for you"

Na girgiza kaina nace "and that's where you are wrong a duk changes din da kake kokarin yi tunda muka hadu, you are trying to change for me, what I want is for you to change for YOU. Ka gyara ba dan ni ba sai dan kanka, dan ka gyara tsakaninka da ubangijin ka. Idan Allah ya duba niyyar ka yaga cewa dan shi kake komarin gyara rayuwarka sai ya taimaka maka, amma idan ya ga cewa danni kake kokarin gyarawa sai ya barka dani ko kuma ma ya hana ka ni din gaba daya"

Zuwa yanzu tension din fuskarsa ya tafi gabakidaya, a hankali ya fara murmushi idonsa a cikin nawa yace "thank you for loving me this much. I love you too. Na miki alkawarin one day zamu zauna zan baki labari akan my drinking habit, yadda na fara da struggles din da nayi akai" na lumshe idona inajin tausayinsa a raina, oh dear Sultan, what other dark secrets are you hiding? Ya sake langwabar da kai gefe yace "please mu bar maganar nan haka, OK? Dan Allah kiyi min murmushi in ga dimples dinki mana" na rufe fuskata da hannayena ina jin kunyar kallon da yake min.

Daga nan muka bar maganar muka koma plans na rayuwar mu, dan yanzu gaba dayan mu munyi shirin taryan koma menene zai faru. Sultan ya yanke shawarar ba zai gaya wa babansa ba saboda yasan ba zai shiga maganar ba. Ya yanke shawarar samun Uncle din shi Galadima, amma first sai ya fara ganawa da Daddy na. Ni kuma na yanke shawarar samun Uncle Aliyu in yi masa bayanin komai akan sultan, na yanke wannan shawarar ne saboda sanin halin Daddy na, he is too smart, idan nace shi zan yiwa bayani har sai ya tono abinda ni a lokacin nake ganin bai kamata ya sani ba.

Sai after ten sannan Sultan ya tafi. Ina shiga gida na tarar da Mommy da Amina jigum jigum a palour sun saka uban kaya a gabansu, na karasa nima ina kallon kayan sannan na fahimci kayan da Sultan ya lodo min a America ne, dama yace zai yi shipping dinsu nan, ashe ya riga ya turo su shine yanzu ya aiko dasu cikin gida ba tare daya gaya min ba.

MaimoonWhere stories live. Discover now