Her Father's Daughter

6.9K 643 4
                                    

Yace "Don't worry about Sultan. Kar ki bari Zaliha tasan kin kirani har sai na nemi contact da mijin ta, dashi zamuyi magana. Badan jirgi baya zuwa agadaz ba Moon da yau zanzo in dauke ki. Amma highest jibi. Ki kwantar da hankalin ki kinji?" Na gyada kaina kamar yana kallona sannan nace "I miss you daddy" ya danyi shiru sannan yace "I miss you too, sunshine" daga haka ya kashe wayar.

Nayi tunanin in kira Hafsat amma kuma sai na fasa kar ta gayawa Mommy na kira ta. Na mayar da wayar cikin jaka ta na fito daga toilet din ina kalle kalle. Babu kowa a dakin. Na dan tsaya ina tunani, a raina nasan kiran daddy da nayi dai dai ne amma kuma duk da haka sai nake jin feeling kamar nayi ba dai dai ba. Na tsaya a gaban mirror, when was the last time dana kalli fuskata? Tunda muka zo na saka wani towel na rufe mirron dakin saboda bana son kallon fuskata. A hankali na bude, ni kaina sai da na tsorata, babu komai a fuskar sai katon hanci da idanuwa kamar na mujiya, dama haka idona yake? Lallai kiba ma rahama ce. Na kalli wuyana naga wani katon kashin da bansan ina dashi a gurin ba, amma kuma kirjina yana nan dam dam, ramar da nayi ma sai ta karawa girman su fitowa. Na mayar da mirror din na rufe na koma na kwanta. Ina kwance Daada ta dawo tayo alwala tazo tayi sallah sannan ta tashe ni, har da dan magagi na kamar me baccin gaskiya sannan na mike na shiga toilet nayo alwala nazo nayi sallah ni ma, muka fita falo tare. Musbahu ne kadai a zaune yana kallo, Daada ta zauna kusa dashi ya fara bata labarin film din da yake kalla, hankalinta gaba daya yana kam kallon na zaro wayar na ajiye a kusa dashi na koma gefe na zauna. Ina kallonsa ya dauka ya saka a aljihunsa ba tare daya kalleni ba.

Muna zaune a palon har akayi magrib, anan muka yi sallah aka fara kawo abinci. Mun fara zubawa kenan mukaji shigowar abban su Mustapha, gaba na ne ya fadi saboda nasan ba lokacin yake dawowa ba, tun daga compound yake kwalla wa aunty Zaliha kira, ta mike tsaye fuskarta da alamar tsorata, yana shigowa ya fara balbalin fada "Zaliha yanzu dama abinda kuke aikatawa kenan ke da Fatima? Kika ce min yarinyar nan hutu tazo yi gidan nan, dama ni ina mamakin tunda tazo ban taba ganin ta fita waje ba, ashe ita nan zaman prison take yi a gidana. Saboda tsabar rashin hankali ku raba yarinya da ubanta da 'yan'uwanta kawai dan saurayin da take so bai yi muku ba?" Kamar zatayi kuka tace "abban Musaddiq dan giya ne fa" yace "to amma baku yi tunanin cewa baban ta shima yana da right na zaba mata miji ba? Ko ita Fatima tana ganin cewa tafi ambassador son ta ne? Yanzu kinga ni kinsa naji kunyar mutumin nan, mutumin kirki wallahi, sai da nayi tayi masa rantsuwa cewa babu hannuna a cikin maganar nan. Yanzu da wani ne da sai dai kawai inga 'yan sanda a gidana"

Ya zo gaba na ya sunkuya yace "Maimunatu kiyi hakuri kinji? Dana san halin da kike ciki kenan da tuni na dau mataki a kai, babanki ya taho already, a daren yau zai sauka a Niamey dan da private jet ma ya taho, ni kuma ni zan kai ki Niamey da kaina. Ki tashi kije ki shirya" aunty Zaliha ta ce da sauri "wai a yanzu zaku tafi?" Ya tashi yayi hanyar dakinsa yana cewa "in bamu tafi yanzu ba yaushe zamu isa can?"

Yana shiga daki kowa yayi shiru a palourn, na mike sum sum zan shiga daki aunty Zaliha ta danko hannuna fuskarta babu rahama tace "uban waye ya baki waya kika kirashi?" Nan da nan hawaye ya kawo idona saboda zafin rikon da tayi min, nace "ni bani na kirashi ba, bansan yadda akayi yasan ina nan ba" ta juya tana kallon 'ya'yanta har yanzu bata cika ni ba tace "cikin ku waye ya bata wayarsa?" Duk sukayi shiru, cikin tsawa tace "ba za'a bani amsa ba?" Nan suka kama rantse rantse banda musbahu da yake ta game dinsa kamar bai san me akeyi ba, tace "Mustapha kai ne ko? Dan na lura da yawan shishshige mata da kake yi?" Mustapha ya kama rantsuwar bashi bane, ko ta kan Musbahu bata bi ba dan sam tunda nazo gidan baya kulani, shi dama ko a cikin 'yanuwansa bashi da harka sosai.

Ta sake ni tana girgiza kai fuskarta kamar zatayi kuka "poor you, you have no idea what you have done to yourself. Sai kije ai, shi baban naki ya aura miki wanda yake so din. Duk abinda Fatima tayi, she did it to protect you amma ke gani kike ta takura miki ne saboda bata son ki" ban gane mai take nufi da babana ya aura min wanda yake so ba, ni dai nasan Daddy bai zaba min miji ba kuma shi da kansa ya fada cewa baya son Munir.

MaimoonWhere stories live. Discover now