The Manager

8.4K 657 1
                                    

Na kalli cikin idonsa nace "I will never leave you Sultan, dama parents dina kawai nake ji, tunda yanzu na samu go ahead din su babu abinda zai saka in rabu dakai" a hankali yanayin fuskarsa ya fara chanzawa daga bacin rai zuwa murmushin da ya saka nima na fara murmushi yace "then I don't need anybody else" 

Mun dau hanyar gida again naji wayata tana ringing, na daga naga Mommy, ina dauka tace "ya akayi har yanzu baku dawo ba? Ku zarto asibiti mun tafi da Hafsat yanzu tana labor" a rikice ta katse wayar ina kallon Sultan nace "Hafsat....labor... Hospital" nan take Sultan ya gane abinda nake nufi ya juya kan mota muka tafi asibitin da Hafsat take antinatal. A hanya na dauko wayata ina neman number, Sultan yace "wa zaki kira?" Nace "Zayed" yace "No, ki bari sai ta haihu tukunna" na mayar da wayar na ajiye.

Muna zuwa da sauri na fita na bar Sultan a mota, a waiting room na samu Mommy da Amina, Mommy tana ta faman jan charbi. Na samu guri nima na zauna muka yi jigum jigum. Ba'a jima ba aka leko aka ce wata a cikin mu ta shiga ta zauna da ita, da sauri na tashi na shiga. Zan iya cewa tare muka yi laborn da Hafsat, in tana kuka nima sai in kama kukan, in tana addu'ah in taya ta. A haka mukayi ta fama har dare ya raba, Sultan yana ta kira yana tambayar jikin Hafsat, a lokacin na kara jinjinawa mata da irin wahalar da suke sha a gurin haihuwa, a lokacin kuma na kara jin haushin duk matar da zata haihu ta dauki dan taje ta yar, kuma na kara tsanar duk dan da zai ki yiwa iyayensa biyayya.

Hafsat ba ta haihu ba sai da alfijir ya fara ketowa, ta rike ni gam tamkar zata ballani sannan ta haifo kyakykyawar 'yarta mace, ana goge yarinyar na karbe ta na rungume ina jin sonta yana shiga zuciya ta, Hafsat ba kunya babu tsoron Allah tana samun kanta tace in bata 'yarta, har nurses din wajan sai da suka yi dariya. Na dora mata ita akan cinyarta ta fara shayar da ita (shayar da baby a wannan lokacin yana taimakawa wajen tsayar da jini da kuma saurin fitar mabiyya, kuma yana taimakawa jariri wajan saurin koyon shan nono da wuri kuma wannan ruwan nonon na farko yana da matukar amfani a gurin jariri).

Gari yana wayewa aka fito dasu dakin hutu, nan fa dakin ya cika da 'yan ganin baby, ina ta Allah2 in kira Zayed ashe har Sultan ya riga ni, Mommy da Daddy sai rige rigen daukan baby suke, Hafsat kam cewa tayi mu fita mu bata guri tayi bacci dan tana son hutawa, tayi kwanciyarta a ciki mu kuma muka taho daya dakin muna ta hayaniyar mu. Bayan azahar Sultan ya kirani a waya, ina fita na tarar dashi a mota ya ce min "shigo" ba musu na shiga, naga ya tayar da mota, nace "ina zamu je?" Yace "gida zan kaiki kije ki huta, jiya baki yi bacci ba throughout" nasan gaskiya yake fada dan haka na kira Mommy nace mata zanje gida in anjima zan dawo, ina zuwa kuwa na tafi daki na na kwanta sai bacci, ban koma asibitin ba sai da daddare muka tafi tare dasu Asma'u da suka dage sai sunje sun ga baby ba zasu jira su dawo gida ba, muna zuwa Zayed ya kira Daddy yake gaya masa cewa ya samu delay din flight dinsa dan haka Daddy yayi wa baby huɗuba da sunan Mommy, Fatima Zahra, Mommy kasa rufe baki tayi dan murnar an yi mata takwara, kowa sai murna har Hafsat taji dadi sosai, Daddy ya karbe ta yayi mata huduba ya miko min ita, Amina ce tace "to Hafsat yanzu me zamu ke ce mata kenan, tunda dai ai mu ba zamu kira ta da sunan ta ba" Hafsat ta daga kafada, sai gaba daya suka juyo suna kallona, ni aka barwa zabi kenan, na kalli babyn sosai ina ganin tsantsar kyawunta na larabawa, nayi murmushi nace "Khairat, we will call her Khairat" a tare Daddy da Sultan suka juyo suna kallona, nayi kamar bansan sun gane me nake nufi ba, Mommy tayi dariya tace "perfect, yayi sosai, Allah yasa ta zama sanadin alkhairi a gare mu baki daya" nan kowa yace "Ameen"

Hafsat ma murmushi take da alama sunan itama yayi mata dadi, Sultan bai yi magana ba sam, ni kuma ban kalle shi ba, sai daga baya na lura ya fice daga dakin. A mota na same shi ya kwantar da kujera ya rufe idonsa kamar mai bacci, na zauna kusa dashi nace "in bacci zakayi ka tafi gida mana" ba tare daya bude idonsa ba yace "why Khairat? Why do you want her when she doesn't want me?" Bance masa komai ba saboda babu abinda zance masa, jin nayi shiru ya saka ya bude idonsa yana kallona yace "yanzu zaki tafi gida ne?" Nace "a'a, anan zan kwana ai" yace "OK, but ki tabbata kinyi bacci sosai, kar ki biye wa little Khairat" nayi murmushi na fita, na tsaya nace "good night" yace "good night Love".

Maimoonحيث تعيش القصص. اكتشف الآن