The Lightening and The Thunder

9.2K 708 5
                                    

Ibrahim ya juya shima da sauri yana kallon inda nake kalla, yace "ya salam" yayi two steps gefe, Sultan ya fara takowa a hankali yana tahowa inda muke, idanuwansa a kaina har ya karaso gabana ya tsaya, ko kallon inda Ibrahim yake tsaye bai yi ba, ga mamaki na sai naga yayi murmushi, amma murmushinsa bai rage min ko kadan daga cikin faduwar da gabana yake yi ba sai ma karuwa da yayi, I know that smile very well.

Ya miko min turaren hannunsa yace "see, I got it" ban karba ba kuma bance masa komai ba, kawai kallonsa nake yi ina jiran bomb din ya tashi. Ya saki kwalbar turaren ta fadi kasa ta fashe, har yanzu murmushin yakeyi, jajayen idanunwansa har kwalli suke yi, yace "kin gama sayen chocolate din? Naga kamar basket din bai cika ba. Let me help you fill it up, in ma gaba daya sweets din gurin kike so sai in saya miki" a hankali nace "Sultan not here, let's go home" yace "oh let's go home? Kin gama kenan ashe, oh na tuna fa ashe dama ba sayen sweets kika zo yi ba kin zo ne ki ganshi, kuma kin riga kin ganshi, mission accomplished, so let's go home"

Jin maganganunsa nake tamkar wuta a kirjina, na juya na kalli inda Ibrahim yake tsaye naga bayanan, na dawo da ido na kan Sultan, yana kallona yace "baya nan ai, ya gudu, ko baki gaji da ganin sa bane inje in kira wo miki shi? Am sure bai bar building din nan ba by now"

Mutane sun fara tsayawa suna kallon mu, na ajiye basket din hannuna na juya nayi hanyar fita daga gurin, tafiya kawai nake amma bana ganin gaba na sosai, how can Sultan even think that? Babu komai a hannuna dan ko waya ta ban dauko ba ballan tana in hau taxi. Na tsaya a packing space din na rufe fuskata da hannayena ina kokarin dai dai ta numfashi na, kaina ya chunkushe bana iya tunanin komai.

Tsayuwar mota naji a gaba na, na bude ido na naga Sultan ya fito daga seat din driver ya zagayo ya bude seat din gaba, ba tare da yace min komai ba ya chusa ni a ciki ya mayar da kofar ya rufe, ya zagaya seat dinsa ya shiga ya ja motar a guje muka bar gurin. Na hadiye dacin da nake yi a bakina nace "how can you even think that Sultan? How can you hurt me like this?"

Ba tare da ya kalle ni ba yace "what do you want me to think ehh? Ke kika matsa lallai sai mun fito yanzu and you also insisted sai munzo sahad, wai zaki sayi chocolate, since when did you start eating chocolate? You also kept delaying us unnecessarily. And I also saw you holding hands and whispering to each other. Tell me what do you want me to think?"

Da hannu daya yake driving din kuma a guje yake tafiya yana ta overtaking motoci. Na lumshe idona saboda kaina da naji yana bala'in sara wa nace "ya kamata a ce kasan ni by now, Sultan ya kamata a ce by now kasan me zan aikata da kuma menene bazan aikata ba" yace "I tot I know you, but when it comes to him am not sure where I stand. He is your first love, har hawan jini kika samu sanda ya gudu ya barki saboda irin son da kike masa, you waited for him years after years, sanda ya dawo it is already days to our wedding, ko kince kin fasa aure na ma kinsan it is impossible Daddy ya fasa....."

Na katse shi nima cikin daga murya nace "duk wannan tsahon lokacin dama abinda kake tunani kenan?" Shima ya daga tasa muryar "what do you want me to think? Kullum mutane suna gaya min you are too good for me, and I also know you are too good for me, you always kept secrets from me..." Na juyo ina facing dinsa sosai nace "kasan dalilin da yasa nake keeping maka secrets? Kasan babban dalilin da yasa tun farko ban baka labarin Ibrahim ba? Because I know you will act exactly the way you are acting now. You always let your temper get in your head and stop you from thinking clearly. Kawai ganina kayi tare dashi, baka tambayeni nayi maka bayani ba, you just conclude and start making accusations, a cikin mutane Sultan a cikin kasuwa Sultan,  I don't think koma menene nayi I deserve something like that from you, you made a fool of me and you made a fool of yourself"

Ban taba jin raina ya baci irin na yau ba, sam na manta da mijina nake magana, na koma na kwanta akan kujerar na dafe kaina da nake ji kamar zai tsage gida biyu, I felt my blood pressure rising. Can kasan muryarsa naji yace "she now calls me a fool" a hankali nace "am sorry. Ban taba jin raina ya baci irin na yau ba, ban taba zaton a ranka za kayi tunanin ina son wani bayan kai ba. Yazo gurina ya rike hannuna ne saboda ya dauka Amina ce, tare suka zo gurin da ita, ba wai da gan gan yayi haka ba, bayan ya gane ni ce ya bani hakuri, he saw that I got scared and was wondering me yasa zan ji tsoron ka"

MaimoonWhere stories live. Discover now