The Pink Handkerchief 2

10.1K 702 10
                                    

Na kashe wayar na mike da sauri na saka dogon hijab dina na bude kofar balcony. Yana tsaye ya jingina a jikin railer yana murmushi. Wandon jeans ne a jikin sa army green da farar singlet yayi stocking dinta a cikin wandon ya daure da belt, sai light green din top wadda ya balle duk buttons dinta ya barta a bude, iskar da ake kadawa a gurin tana ta diban rigar tasa kamar zata chire ta, at the same time kuma tana diban gashin kansa.

Na dan bata rai nace "Sultan me kake yi anan cikin daren nan" shima bata ran yayi yace "to tunda kin hanani zama acan ba sai in taho nan ba. Ni nasan kona kwanta yau ba zan iya bacci ba, ba gwara in taho nan ki tayani hira ba" naji dadi har raina dana fahimci ya bar gurin partyn saboda nace bana so, nasan it was a hard decision but a good one.

Na jawo kofar na rufe saboda tunawa da nayi cewa Amina tana cikin dakin, na karaso inda yake na jingina da railer nima ina kallon kasa nace "thank you" yayi ajjiyar zuciya yace "I will never do any of those things da Daniel yake fada" nayi shiru ban ce komai ba, ya danyi dariya yace "they will kill me in suka kamani gobe da safe, dan duk cikin su babu wanda yasan na fito, sai daga baya zasu lura bana nan" ya dauko wayarsa a aljihu yayi switching off ya mayar aljihun sa. Ya kalleni ya fara murmushin mugunta r,v yace "but there is a price for everything, tunda kika hana ni kwana a gurin party na to yau a dakinki zan kwana" nima murmushin muguntar na mayar masa nace "bismillah, ina nuna kofa" babu musu yaje ya bude kofar, sai yayi sauri ya rufe ya dawo da baya, dariya nayi sosai nace "ka shiga mana, wallahi in ta fara ihu sai duk mutanen gidan nan sun tashi daga bacci" ya dan jima yana tunani sai kuma ya sake bude kofar, ina hango yadda Amina ta kudundune a cikin bargo tana baccinta, hannu ya saka ta bayan kofar ya zare key din jiki sannan ya mayar da kofar ya rufe yayi locking ta waje ya saka key din a aljihunsa yace "then we will sleep here" da mamaki nace "you are not serious are you?" Yace "sa ido kiyi kallo" daga haka ya tafi ya kwanta rigingine a kan carpet din da yake gurin. Tsayawa kawai nayi ina kallonshi naga yayi pillow da hannunshi ya rufe ido, gaba daya rigar ta bar jikinsa sai singlet din kawai.

Nayi sauri na dauke kaina na daina kallonsa na koma ina analysing situation din, nayi tsaki a raina ina cewa 'Sultan, wannan fa shine baccina na karshe kafin aure a gidan mu amma ba zaka barni in kwanta a gado na ba'.

A kwai security light sosai a compound din gidan amma duk waje suke haskawa, wannan ne ya kara wa balcony din duhu, ma'ana babu wanda zai hango mu daga waje amma mu zamu ke ganin su. Amma Amina da take daki zata iya farkawa kowanne lokaci taga bana nan. Already jikina ciwo yake min saboda gajiya amma kuma ace zan kwana akan carpet. Amma kuma gwara haka da ace Sultan ya kwana a gurin wadancan mutanen.

Sai dai ni ban yarda inje kawai in kwanta a kusa da Sultan ba. Na mayar da dubana kan kujerar da take gurin, sai naji dadi da na tuna cewa ana iya kwantar da ita ta koma yanayin dan karamin gado, naje nayi reclining dinta yadda zata yi min daɗi tunda ko pillow Sultan bai bar ni na dauko ba, na kwanta akai tare da kudunduna a cikin hijab dina, kadan kadan nake kallon Sultan, ina lissafin ko yayi bacci ko idonsa biyu a haka har daga baya bacci ya dauke ni.

Cikin bacci naji kamar ana hura min iska a fuska a hankali na bude idona da suka yi min nauyi saboda bacci, fuskar Sultan na gani dab da tawa yana kallon fuskata. A hankali tunani na ya fara dawowa, nayi sauri na mike zaune ina rarraba ido, na fahimci assuba ta kusa, na mayar da idona kan Sultan da yayi tagumi da hannu daya yana kallona sannan kuma na kalli jikina, making sure hijab dina yana jikina, har da saka hannu in shashshafa jikin dan inji lafiyar komai.

Duk abinda nake Sultan kallona kawai yake yi yana dariya, sai da ya gama dariyar sa sannan yace "Don't worry gobe ne ba jibi ba. And when I touch you ko tashi zaune ba zaki iya ba" na bata rai ina ƙunƙuni a zuciyata ina mitar ciwon da jikina yake min saboda kwanciya a kujera.

Na mike tsaye ina kara kallon waje, ya mike shima yana gyara rigarsa data cukurkude ya karaso kusa dani yace "zanje in shirya, karfe shida zamu bar nan saboda muje akan lokaci" ban bashi amsa ba ya kara matsowa kusa dani yace "are you scared?" A hankali na lumshe idona sannan na gyada kai nace "yes, yes I am scared" yace "me too. I am scared I might fail you as a husband. Na sani kamar yadda mutane suke ta fada min koda yaushe cewa I don't deserve you. Ni kaina bansan dalilin da yasa Allah ya bani ke ba, kin fi karfi na nesa ba kusa ba. Amma abinda na sani without doubt shine ke alkhairi ce a gare ni"

MaimoonWhere stories live. Discover now