Skeleton in the closet

8.7K 661 8
                                    

A hankali Takawa ya fara dawowa haiyacinsa, ya bude idonsa da sauri yana kokarin ya dai dai ta tunanin sa, Ya Rabbi, wannan wanne irin mugun mafarki yayi haka?

A mafarkinsa wai an raba shi da Khairat, a mafarkin sa kuma wai baya son Little Love, a mafarkinsa little love shine abinda yafi tsana fiye da komai, kuma wai har anyi shekaru da yawa har Little Love ya girma yayi aure. Oh wannan wanne irin mugun mafarki ne haka? Ya yunkura ya tashi zaune yana duba gefensa dan ya tashi Khairat ya bata labarin mafarkin da yayi, amma sai me? Babu Khairat a gurin, kuma wannan gadon ba nasa bane ba, ya kalli dakin shima, wannan dakin shima ba dakin sa bane ba, yayi kama da royal suite na asibiti.

Ya dafe kansa, a karshen mugun mafarkinsa an yi forcing dinsa ya je asibiti duba little love daga nan kuma bai san me ya faru ba sai ya farka daga mafarkin, to ko dai still har yanzu mafarki yake yi ne? Ya matsa ledar drip din da ya gani a jikin hannunsa yaji zafin shigar ruwan, mutum ai baya jin zafi a mafarki. Ya tashi zaune sosai ya cire drip din ya mike tsaye, gaban taga yaje ya daga labulen tagar, tabbas nan asibiti ne. Ya ilahi what is happening? Kofar toilet ya bufe ya shiga dan ya wanke fuskarsa maybe ko zai dawo haiyacinsa sosai, abinda ya gani a cikin madubi shine ya saka ya daskare a bakin kofa, he looked exactly like yadda yake a cikin mafarkinsa, older, thirty years older, ya karasa gaban madubin yana taba fuskarsa, shi din ne dai kuma tabbas wannan ba mafarki bane ba.

"Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun"

Yanzu duk abinda ya faru da gaske ya faru kenan? Yanzu shekararsa talatin rabonsa da Khairat? Tana ina yanzu, shin tana da rai ko akasin haka? And Little Love, poor innocent Little Love. A toilet din ya durkushe yana rusar kukan dashi kansa bai san ya iya irinsa ba.

30 years back
Tabbas, Prince Sadiq Abdallah yayi soyayya da Khairat Faysal Abdallah a Oxford, England. Khairat full blood balarabiya ce kuma she too is of royal blood, born and raised in Riyadh, Saudi Arabia. Soyayya suka yi mai tsanani wadda har suke ganin cewa kamar they share the same soul but different bodies. Amma duk wannan soyayyar da suke yi iyayensu basu da masaniya a cikin al'amarin, wannan kuma ya faru ne kasancewar Khairat balarabiya dan larabawa da wahala su dauki 'yar su su bada ita aure ga bakar fata, bahaushe.

Khairat bata taba ganin anyi haka a familyn su ba, in fact a familyn su ma mostly auren dangi ake musu, dan already ma ita da akwai wanda aka riga aka ajiye mata zata aura in ta gama makaranta. Wannan shi yasa duk nacin da Sadiq yake yi mata akan ta barshi yaje gidansu taki yarda. Lalube kawai suke yi a cikin duhu. Sadiq yasan da irin kalubalen da yake gabansu amma shi bashi da tsoro sam, kuma ya riga ya saka a ransa cewa Khairat tasa ce ko da kuwa sama da kasa zata hadu babu wanda ya isa ya raba shi da ita.

A haka har suka gama makaranta, iyayen Khairat suka zo suka dauke ta suka mayar da ita gida. Wannan ba karamin tayar da hankalin Sadiq yayi ba dan ya san da maganar wancan hadin da ake so ayi mata a gida. Babu shiri shima ya tattaro ya dawo Nigeria gurin sarki Abdallah, ya shigar da maganar yana son sarki Abdallah yaje can Riyadh ya nemo masa auren Khairat. Sarki Abdallah yasan abinda dan nasa yake nema is close to impossible, ba zasu bashi auren Khairat ba, musammam tunda an riga an yi mata miji, ba zasu karya alkawari ba, hakan yasa yayi kokarin tausar zuciyar dan nasa akan ya hakura da auren ya dawo gida ya nemi auren ko wacece a Nigeria zai nema masa aurenta, amma Sadiq was as hard as stone, dan haka ya tubure shi lallai ita yake so kuma ita zai aura.

Da Sadiq ya fahimci cewa baban nasa bashi da niyyar honoring wish dinsa ga kuma time yana kurewa dan yasan a koda yaushe za'a iya daura wa Khairat aure, dan a halin yanzu ma tayo masa waya tana kuka cewa maganar auren ta tashi kuma ta fadawa babanta cewa ita bata son wanda za'a aura mata kuma shi sadiq din take so, tana fadar haka baban ta ya saka aka kaita daki aka rufeta yace ko palour kar a barta ta ta kuma fitowa.

MaimoonOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz