Awkward

7.9K 648 2
                                    

Ranar duk ban karasa ta da nishadi ba,  the day was my graduation day, I was supposed to be happy but I wasn't, I felt sad and lonely. Da naje gida ma yaƙe kawai na ringa yi daga baya ma na tafi daki nace na gaji bacci zanyi, a dakin kuma da na kwanta sai na kasa baccin.

"So Sultan thinks he is tough right? He thinks he can just give me up instead of facing me? Lets see how tough he can be. Wato ni nice soft one din shine Amir zai wani zo yace in kira shi ko?"

Na ga dai baccin ba zai yiwu ba na mike na fara abinda na saba duk sanda wani abu ya dameni ko wani al'amari ya shige min duhu, na tashi na fara gaya wa Allah. Nayi adduoi sosai akai na da kan Sultan ina nema mishi guidance na ubangiji.

Sai a lokacin na fara wani tunani, addu'ar iyaye itace addua mafi inganci a gurin 'ya'ya, Sultan baya samun wannan, shi kansa ba lallai ne yana yiwa kansa da kansa addu'ar ba. Duk da dai adan zaman da nai dashi na lura baya barin sallah. Na gama adduoi na na kwanta akan sallayar nayi baccina.

Da assuba na tashi nayi sallah, har na koma zan kwanta naji still raina babu dadi, na dauko waya ta a jaka na kunna na nemo number din Sultan nayi dialing, sai da ta kusa katsewa sannan ya dauka, amma bai ce komai ba, naji takaici ya kamani kamar in rufe kaina da duka, why did I even bother to called? Na katse kiran kaman zanyi kuka. Ina ajjiye wayar kiransa yana shigowa. I let it rang. Ya sake kira naki dagawa. Message ya shigo.

"Answer the call please"
nayi reply "why didn't you call me sai da na kira ka?"
"Am sorry, please pick up the phone"

Wani kiran ya shigo, it had been a month rabona da Sultan, rabon da inji muryarsa. Na dauka tare da sallama. Ajjiyar zuciya naji ya sauke and then an awkward silent followed. Nace "look, idan ba zaka yi magana ba zan ajjiye wayar" a hankali yace "how are you?" sai da naji muryarsa sannan na fahimci how much I had missed him. Nayi shiru kuma na kasa magana sai daga baya nima cikin rawar murya Nace "I missed you" ya dan jima sannan yace "I have more than missed you, I have no words for what I am feeling" Nace "amma me yasa baka kira ni ba? It hurts me sosai, how can you give me up just like that?" A nutse ya fara magana "you have no idea how much I love you, do you? Bawai nayi giving up on you bane, I am a bad person Moon, You are good, more than good, bana son in bata miki rayuwarki. Ina sonki son da zan iya rabuwa dake even if it kills me, in dai har zaki samu kyakykyawar rayuwa" na katse shi da muryar kuka nace "and who says I want a good life? Huhh? All I want is a life with you. Just tell me idan har kai ka daina sona ne kawai ka gayamin ka daina min wani boye2. You keep saying you are a bad boy, you can never be good in dai har kana tunanin you are bad" yadda na rufe shi da fada ne yasa yayi shiru ya kasa magana. Nima dana gama fada na nayi shiru. Sannan nace "when are you going back to Nigeria?" Yace "I have nothing to go back to Nigeria for"  nace a hankali "you can come to England you know? you have me here, right? Besides, ina son kazo ka gaishe da Daddy"

Ya danyi jim sannan yace "are you sure?" Nace "yes, am sure. Kai na zaba a matsayin mijina, whether you are good or bad, kai nake so, all of you, the good side and the bad side gabakidaya"

Sosai magana ta ta taba zuciyar Sultan dan har a muryarsa naji, shi abinda ya cigaba da insisting shine wai I was too good for him, baya so ya sake letting dina down, baya son ya sake hurting dina ya saka ni kuka. Daga karshe dai na gaya masa cewa nan da about a month or so zamu koma Nigeria kuma muna zuwa aure za'a yi min da Munir, who I despise, dan haka zabi ya rage nasa, is either ya zauna a America ya cigaba da playing bad boy role dinsa ni kuma a aura min Munir ko kuma ya dawo yayi facing Daddy ya karbi aurena.

Ina fadin haka na katse wayar, ko minti daya ba'a yi ba ya kira, na katse kiran na kashe wayar gaba daya. Na san na kunna masa wuta. Dole ya dawo cikin sense dinsa yasan abinyi.

Ranar da yamma naje na samu Mommy a dakin Daddy tana gyara masa kaya. Na zauna a kusa da ita nace "Mommy wannan da kuke zance ke da yaya Walid rannan, sunansa Abbakar, dan garin Abuja ne, he is an architecture, iyayensa manyan mutane ne sosai a garin Abuja. Ina son kiyi wa Daddy maganar sa idan kun amince zai zo England ya gaishe da ku" Mommy ta kalleni fuskarta kamar gonar auduga tace "kai Alhamdulillah, he is your final choice kenan ko?" Na gyada kai tace "Allah ya kawo shi lafiya" nace "Amin" har na mike sai kuma tace "Moon, kash, kinga har naso in manta, Daddyn ku jibi zai yi tafiya, president ne ya tura shi wani summit a South Korea kuma zasu dan jima a can, dan yace ma maybe sai dai mu hadu a Nigeria tunda mu zamu tafi da wuri kinsan maganar bikin Nuraddeen ya tashi"

MaimoonWhere stories live. Discover now