The Eclipse

6.9K 583 4
                                    

Na cigaba da kallonsa har ya bace min da gani. Feshin ruwan saman da akeyi yana dukan fuska ta amma sam ban damu dashi ba. Zuciya ta tana kuna amma hawaye yaki zuwa ido na balle inji dadi. Motsin mutun naji a baya na, nasan ko wace dan haka ban juya ba. Sai da ta lulluba min towel sannan nasan duk jiki na ya jike da ruwa. A hankali ta jani muka shiga daki ta rufe kofar balcony din. Na zauna a kan stool ina goge ruwan jikina ita kuma ta zauna a gefen gado tana kallona. Tace "what happened Moon?" Na dago kaina na kalleta da busassun idanu na nace "He is gone" "gone?" "Yes, He was mistreated by our security, He saw Daddy and....... Ya Walid yazo ya gaya masa cewa daddy ne ya samo masa aiki, he then lost it"

Hafsat ta saki hannuna ta rufe bakinta da hannayenta. "Oh my God, me yace kuma" nan na bata labarin duk abinda ya gudana tsakanin mu. Tayi shiru na wani lokaci sannan tace "Moon am so sorry, I really am, amma dama nasan alakar ki dashi ba mai dorewa bace. You are too different from each other. Banbancin da yake tsakanin ku kamar banbancin da yake tsakanin Maiduguri ne da Lagos, ba zasu taba haduwa ba"

Na kalleta da murmushin takaici a fuskata nace "you are wrong my dear sister, we are more alike than we are different. Na farko duk kanin mu mutane ne, sannan kuma Africans, must importantly kuma Muslims. As muslims kuma munsan we are all equal a gurin Allah, babu wanda yafi wani sai wanda yafi tsoron Allah. Banbancin da kuke gani a tsakanin mu banbancin kabila ne. Ni a ganina kabilar mutum ba komai bace illar yarensa da al'adunsa. Yanzu misali ke wacce yare ce?"

Ta kalleni da mamaki tace "fulani mana" nace "eh, babanki fulani ne amma mamanki buzuwa ce, meaning you are not full blood fulani. Yare yana nufin language, yanzu misali ni, ina jin fulatanci, buzanci, turanci, larabci da hausa. To wanne yare ce ni kenan? Yanzu fulani nawa kika sani wadanda suke full blood fulani amma basu iya fulatancin ba? Wani ko zo bai sani da fulatanci ba amma yana ikirarin shi bafulatani ne. It doesn't make sense to me. In nayi maganar al'ada kuma is much worse than yare, dukkan kabilun Nigeria mun aje al'adun mu a gefe mun dauko na wadansu daban munayi. Then how are we different from each other?"

"Yanzu ke da kika ce ke bafulatana ce duk cikin suturar ki babu ta fulani, babu abinda kika sani na daga al'adar fulani, we are even lucky mun iya yaren ma. This all doesn't make sense to me. Yanzu na tabbata idan aka kawo miki wani bafulatanin wanda bai iya fulatanci ba, aka kawo miki Igbo ko yoruba wanda ya iya turanci sai kin fi communicating da igbon ko yoruban akan fulanin"

Duk maganar da nake Hafsat tayi shiru tana kallona da alamar tana fahimta ta. Can ta nisa tace "Ok, yanzu what will you do?" Na kalleta for some seconds nace "That, my dear sister is what I don't know"

Sati guda kenan chif da zuwan Ibrahim amma har yanzu ban ji sassauci a zafin da zuciya ta keyi min ba, kuma har yanzu ban yanke shawarar menene abinyi next ba. Ina kwance main falo akan kujera, Hafsat tana zaune a gaba na, Mommy tana can gefe tana operating system din ta.

Waya ta nayi dialing na saka a kunne na "the number you are trying to call is currently switched off, please try again later, thank you" naji wadannan kalmomin ya kai sau dari a cikin satin nan, amma na kasa hakura in daina trying.

Na ajiye yawar na lumshe ido na. Muryar Ya Habeeb naji ya shigo da sallama, ya gaida Mommy ya zauna kujerar kusa dani. Na dan kalle shi, yayi min murmushi, ban mayar masa ba, na sake mayar da idona na rufe.

Wajan five minutes muna zaune a haka babu wanda yayi magana. Can Ya Habeeb yayi tsaki yace "wai menene yake faruwa a gidan nan ne? Duk komai ya zama so dull kwana biyun nan, ni na gaji gaskiya" Mommy tayi ajiyar zuciya tace "I don't know Habibi, ni kaina abin ya ishe ni wallahi, dazu nake cewa ko da yamma fita zamuyi ne mu dan zaga gari? Duk gidan babu dadi"

Hafsat tace "au wai ku baku san me yake faruwa ba?" Ya Habeeb yace "menene yake faruwa?" tace "we are having a lunar eclipse" Mommy tace "what? Me kike nufi?" Hafsat tace "our Moon is no longer bright" duk suka juyo suka kalleni. Ya Habeeb yace "tabbas, duk ta zama wata iri kwana biyun nan" Mommy tace "ko abincin kirki bata ci fa, kullum na tambayeta ko bata da lafiya sai tace min ita lafiyar ta kalau" duk ina jin abinda suke cewa amma na kasa tanka musu.

MaimoonWhere stories live. Discover now