Missed You

8.8K 644 5
                                    

Na lumshe idona ina addu'ar Allah yasa shi din ne na gani ba wai gizo yake yi min ba, dan ganin nasa ya taba min wani guri a zuciya ta wanda bansan yadda zanyi ba idan ba shi bane. Muna zuwa airport muka fito, Mommy ce ta fara shigewa jirgi, Daddy ya tsaya suna sallama da mutane, sai lokacin na samu damar ganawa da yaya Walid dan a mota tsoron Mommy ya hana ni magana, na rungume shi sosai tare da cewa "I missed you" ya rabani da jikinsa yace "I missed you too sweetie pie" ta gefen idona na hango Sultan yana tahowa gurin da muke, kara kankame yaya Walid nayi ina runtse idona, 'Oh Allah, give me the strength kar inje inji kunya a gaban mutane' na kasa kallon inda yake dan nasan zan iya loosing control shima in rungume shi kamar yadda na rungume yaya Walid, muryarsa naji yana cewa "to cika ta haka, ai an gama oyoyon" shi dinne dai, dan muryar sa ce wannan.

Ya walid ya dafa kafaduna da hannayensa duk biyun yace "anki din, sai ka bari in an daura muku aure sai kayi min iko akanta amma yanzu tawa ce. Ni ban taba ganin ma suruki marar kunya irin kaba Sultan, babban wa ai uba ne, ni ne fa madaurin auren ta, inna ga dama sai ince bazan bayar ba" yaushe Sultan suka fara wasa da Ya Walid? Last time I checked ya Walid ya mari Sultan.

Wata dariya Sultan yayi yace "kayi kadan yaro, ni iya kacin sani na na girme ka, dan haka kai ya kamata ka ke yi min biyayya" ya Walid ya kama hannuna muka tafi jirgi, har yanzu na kasa kallon Sultan, sai da muka fara hawa steps din sannan na juyo ina tunanin kar mu tafi mu barshi, ina juyo wa muka hada ido, nayi sauri na dauke kaina.

Chamber biyu ne da jirgin sai gurin pilots, Daddy da Mommy suna chamber din farko, mu kuma mu uku muna chamber ta biyu. Tunda na zauna har jirgin ya tashi ban daga kaina ba, duk jina nake a takure saboda idanuwan da Sultan ya dora a kaina ko kiftawa baya yi. Ji nayi kallon yayi yawa na dan daga kaina kadan sai naga ashe ido hudu ne a kaina ba biyu ba, yau naga ta kaina zasu chinye ni danya.

Ya walid yace "kin ganki kuwa? Wannan ai kece ifritu minal jinni. Wannan irin rama haka? Me Aunty Zaliha tayi miki?" Ni dai bance komai ba na rufe fuskata da hijab dina. Ina jin Sultan yana ce masa ya tashi ya koma gurin su Daddy, ya Walid yace "saboda me? Duk abinda zaka gaya mata ka gaya mata a gabana. Suma wadancan din couple ne, gwara ma ku ba aure ne da ku ba, babu wani abu da zakuyi wanda ba zan iya gani ba" su kayi ta maganganun su ina jinsu bance musu komai ba, shi Sultan yana ta insisting sai Walid ya tashi ya bamu guri shi kuma yaki.

Nadan bude fuskata kadan na kallesu naga basa kallona sai na gyara zamana na bude fuskata sosai. A hankali nace ina kallon Sultan "how is your leg?" Duk suka jiyo suna kallona da mamaki Sultan yace "What?" Na sake maimaitawa ina kallon kafarsa. Still bai gane mai nake nufi ba, nace "kafarka da kaji ciwo rannan, how is it?" Dariya yayi sosai, da alama yama manta da cewa yaji ciwon, yace "ta warke ai, tun tuni. Abinda ya kamata ki tambayeni shine how is my heart, ita ce take ciwo yanzu" ya Walid ya harare shi, ni kuma nayi murmushi ina sunkuyar da kai na kasa.

Har muka sauka a Nigeria bamu samu munyi wata magana da Sultan ba, muna sauka muka tarar da motoci suna jiran mu, muka shiga sai gida. Tunda na fito daga mota nake jin idanuwan Sultan a kaina amma naki kallon inda yake da sauri na shige cikin gida. Ina shiga palo na tarar da yaran gida kowa sai murnar dawowa ta suke, nan na sha runguma har sai da jikina ya fara ciwo, da wayo na gudu na hau sama na shiga dakina, a gyare na tarar da dakin sai kamshi yake yi, na fada kan gado tare da lumshe idona, home sweet home, da sauri kuma na mike naje na bude window ina leken waje ko zan ganshi amma naga bayanan, to ko ya tafi gidan su? Toilet na shiga na kunna ruwa a tub na hada kumfa sosai, when was the last time I had a real bath? Na cire kayana na shiga ina sauke ajjiyar zuciya.

Na lissafo irin wahalar da nasha, kuma duk akan Sultan amma yanzu wai gani gashi na kasa yi masa kwakwkwarar magana. Sai kuma na fara yiwa kaina tambayoyin me ya faru da bana nan? Ya akayi har su Daddy suka karbi Sultan har ya saba dasu sosai? Jin ana kiran sallar isha yasa na tuna ko magrib banyi ba, na dauraye jikina na fito, na bude kayana naga sunanan yadda na tafi na barsu sai dai daga alama an dan karkade su an sake gyaramin, na saka wasu riga da skirt ga mamaki na sai naga wuyan rigar yayi min yawa skirt din kuma yana zamewa, chafdi, gaskiya na rame da yawa, dole na saka doguwar riga nayi rolling mayafi na fita. Ina saukowa daga sama na tsaya da mamaki, Sultan again, dare dare a kan kujera a palo suna ta zabga musu da ya Habeeb, a tare suka juyo suka kalle ni, dif Sultan ya dauke wuta ya daina magana, ya Habeeb kuma ya taso da sauri gurina yana cewa "welcome home, my parrot" nayi murmushi na karasa gurinsa, sai kuma ya rike hannuna yana kallon fuskata, dariya yayi yace "kinga yadda kika yi baki kuwa?" Na juya idona nace "tubarkallah, wannan yace da rame wannan yace nayi baki in ba so kuke ku chinye ni ba ai ya kamata ku kyaleni haka"

MaimoonWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu