The Storm

7.1K 603 4
                                    

A daidai kofar gidan su Moon, Yaya Walid yana kokarin shiga bayan ya dawo daga masallacin sallar ishai sai yaga wani saurayi yana kokarin yi masa magana, kallo daya yayi masa ya gane shi saboda hasken fatarsa da ya sha banban da na mafi yawan mutane, ya tuna yana ganin sa da tare da Moon a london, da ya dauka ma soyayya suke yi dan har gidan su yakan je gurinta sai daga baya kuma ya daina ganin su tare.

Ya karbi hannun da yake mika masa suka gaisa da sakakkiyar fuska sai kuma saurayin ya tsaya yana shafa kai yana murmushi. "Bismillah" Yaya Walid ya ce masa yana nuna masa kofarmma sai saurayin ya girgiza kai yace "nagode, amma ba na jin zan shiga. Bani da number dinka ne dama da waya ma kawai zan yi maka. Wata magana ce nake so muyi. Sunanan Mahdi, munyi karatu tare da kanwarka Maimoon a Oxford"

Ya Walid ya gyada kai yace "na gane ka ai, sunan ne dai ban sani ba amma na gane fuskar" Mahdi ya gyara tsayuwar sa, he seemed disturb, kamar abinda zai fada ne yake disturbing dinsa. "Ina jinka" yaya Walid yayi encouraging dinsa, ya bude baki ya rufe, ya sake budewa sannan yace "akan Maimoon ne, I feel ya kamata in gaya muku ku kara saka ido a kanta" sai kuma yayi sauri yace "ba wai ina nufin ba kwa saka ido ba, amma nasan halin mu mu matasan yanzu, zamu iya boye abinda muke aikata wa a waje yadda ba za'a sani a gida ba".

Yaya Walid ya cigaba da kallon sa fuskarsa cike da confusion, sai kuma yace "menene Maimoon din take aikatawa wanda kake tunanin ba mu sani ba?" Mahdi yayi shiru yana tunanin, he hated seeing that boy destroying that innocent girl's life, amma kuma still baya son ya hada ta da iyayen ta, but he knows a ransa cewa ya kamata yayi something akai, and that something is what he was doing.

Yace cikin yanayi na tsintar kalmomi "akwai wani da suke tare da shi mai suna Sultan, ban sani ba ko a gida an san da shi?" Walid yayi shiru yana juya sunan Sultan a ransa sannan yace "Sultan?" Mahdi yace "eh, ban san shi ba but naji ance ɗan Sarkin garin nan ne"

Nan take yanayin fuskar yaya Walid ya chanja, ya sake maimaita sunan cikin mamaki "Sultan? Menene hadin Maimoon da Sultan?" Mahdi ya sake jin babu dadi amma kuma yana da tabbas din abinda yayi dai dai ne dan yanayin fuskar Walid ya tabbatar masa a gida ba'a san Maimoon tana tare da Sultan ba, yace "ba wai wani abu ne naga ita Maimoon din tayi ba, kawai dai naga......." Sai kuma ya kasa cewa komai, Maimoon tana da wani kaso mai tsoka a zuciyarsa. Yaya Walid ya sake miƙa masa hannu yana gyada kai yace "I understand, and I am really greatful that you come forward with this information, and I promise you your name will not be mentioned".

Daga haka ya juya cikin sauri ya shiga gida, a ransa yana fatan abinda yaji ba gaskiya bane ba amma kuma wani part din zuciyarsa already har ya yarda da maganar dan Mahdi bai yi masa kama da makaryaci ba. "Moon will have a lot of explaining to do"

Yana shiga yaji an bude gate motar Mommy ta shigo, dan haka sai da ya tsaya ta fito sannan ya gaishe ta suka shiga cikin gidan tare, baya son gaya mata komai sai yayi confirming daga Maimoon tukunna kuma ya saurari uzirinta. A palour suka tarar da Habib, daga dukkan alama shima daga sallah yake, Mommy ta zauna akan kujera cike da gajiya shi kuma Walid ya wuce saman Moon, so yake yaji daga gare ta kafin ya san matakin dauka akan maganar da yaji yanzu.

Yayi knocking kofar dakin ta ya jira, shiru babu amsa sai ya sake yi sannan ya tura kofar tare da sallama. Bata nan. Ya sake sallama da ɗan karfi shima shiru dan haka ya juyo ya sauko yana kokarin kiran ta a waya. Sai kuma ya dakata at the foot of the stairs yana kallon Habib da yake yiwa Mommy wani bayanin wanda daga dukkan alama ya dauki hankalin ta sosai, sai dai shi abinda ya dauki hankalin sa shine sunan Sultan da yaji an ambata, sai kuma yaga Mommy ta mike da sauri hankalinta a tashe sannan ta fara kwalla kiran Maimoon tana kallon hanyar dakinta.

Asma'u da taji kiran da ake wa Maimoon ta fito daga kitchen tana cewa "Mommy mai sunan Daada bata jin dadi, tace zata kwanta a dakin ta kanta yana ciwo" Walid ya kalle ta sannan ya kalli Mommy yace "bata can, bata dakin ta"

MaimoonWhere stories live. Discover now