Munir

6.3K 607 3
                                    

Ina kallon cdn ya jima yana floating sannan ya nutse. Na dauke kaina na koma hanyar inda na baro su Hafsat. Tun daga nesa na hango alamar abinci suke ci, sun shimfida blanket suna zaune akansa. Na karasa da sauri nace "ina fatan dai baku cinye sandwich din nan ba" Amina ta kalleni da mamaki tace "au da jira kike yi mu rage miki? Kinga na hannuna shi ne na karshe, sai dai kisha fruits" ban yi wata wata ba na kwace na hannunnata na tura shi gabakidaya a baki na, ai kuwa ta taso kaina lallai sai ta kwace, suka hadu ita da Hafsat suka danne ni, Hafsat ta kama yi min chakulkuli ina dariya Amina ta ƙwakwule sandwich din daga bakina, sai kuma ta jefar dashi a kasa tace "ew, duk ta saka yawu a jiki"

Hafsat ta daga ni tana karkade jikinta saboda dan squeezing da kayanta suka yi, na faki idonta na damƙo kasa cikin hannuna na watsa mata ta cikin wuyan rigarta. Tsayawa kawai tayi tana kallona cike da takaici, Hafsat da shegiyar tsafta, kuma na tabbatar kasar ta shiga har cikin brazier ta. Ta ma rasa me zata ce min duk masifar ta. Sai kawai ta juya baya tana karkade rigarta ni kuma na cigaba da kyalkyala mata dariyar mugunta, banyi aune ba kawai sai jin kasa nayi a fuskata, har cikin baki na dana bude ina dariya. Nan take wani fadan ya kuma rinchabewa kowa yana watsawa kowa kasa. Kasa har cikin gashin mu ranar sai da ta shiga.

Sai late evening ranar muka bar beach din gabaki dayan mu munyi kacha kacha. Muna shiga palour Mommy ta mike "what in God's name happened?" Hafsat ta nuna ni tace "ita ce ta fara" Mommy ta juyo da dubanta kaina, kafin tayi magana na yi sauri nace "aga wanda zai fara zuwa toilet" nan muka dau gudu muka yi dakin mu muka bar Mommy a tsaye da sakakken baki.

Tun daga ranar na mayar da hankali na wajan ƙoƙarin ganin na manta Ibrahim, daga naji ya fado min araina sai in fara wani abin da zai dauke hankali na. Addu'ah kuwa kullum sai na yita. Lecturers din mu sunyi marking report din da na rubuta sun turo wa daddy, ya kira ni naje na same shi a zaune shida Mommy ya miko min takardar hannun sa yace "karanta a fili inji" na bude hannuna yana rawa na fara karantawa, As da Bs ne duk, ko C babu, na ajiye takardar na rufe bakina ina dariya, daddy shima dariyar yake yi yace "ashe zaki iya, da wato ganin dama ne bakiyi ba ko?" Mommy tace "Moon ai tamkar mai aljanu take, yau fari gobe baki, ni kaina ban san inda ta sa gabanta ba" Daddy yace "at least she is doing good yanzu" ya juyo ya kalleni yace "Moon, ina so in cigaba da ganin irin wannan result din, bana son wannan mood swings din naki. Kina da kokari, kiyi amfani da brain din ki yanzu da kike da chance" nace "nagode Daddy, insha Allah abinda ya faru a baya ba zai kuma faruwa ba".

Yanzu a makaranta bama tare da Hafsat, dan haka kowa harkar gabansa yake. Amma hakan bai yi affecting dina ba kamar yadda nayi tsammani, na mayar da hankali na sosai akan karatu na, nan da nan na fara sabawa da mutane, lecturers duk sun sanni saboda ni ina da saurin shiga ran mutane. Turawa, blacks da sauran kabilu duk kowa nawa ne, maza da mata. I was very serious akan karatu and was very friendly.

Sai da muka gama second year din mu sannan na samu zuwa Nigeria. Kawai sai naji bana wani murnar zuwa saboda dama wanda nake saka ran zan gani a Nigeria yanzu na tabbatar is no longer mine. Da muka je Nigeria sai muka zama abin kallo a gurin mutane saboda yadda muka zama, ni kaina nasan a cikin wadannan shekaru biyun ba karamin chanji na samu ba, fata ta wani mugun laushi da santsi, nayi yar kiba ta komai ya cika yayi bulbul, ga kuma uwa uba wayewa, daɗin mu daya Mommyn mu is very strict, bata son shigar banza, dan haka koda English wear mu ka saka to sai mun rufe jikin mu, bama taba fita waje da matsatstsun kaya. Samari kuwa tun a makaranta har a gida haka muke ta fama dasu, daga ni har Hafsat har Amina babu wacce take kula samari, dan ni a England zobe na saya na saka a ring finger dina, duk wanda yazo naga yana kokarin ya fara nuna min soyayya sai in nuna masa zoben in ce "am married" duk da dai wadansu suna fahimtar karya nake yi amma dole su hakura tunda babu yadda zasu yi dani.

Muna zuwa Nigeria ma abinda ya faru da mu kenan, dan ma samarin nan suna dan jin tsoron tunkarar mu amma duk da haka da akwai masu courage, in sunzo nakan tsaya in basu hakuri ince anyi mana miji, Hafsat kuwa ko kwallon inda suke bata yi balle ta kulasu. Rannan Amina tace "ni kam Hafsat zan ga saurayin ki a duniyar nan" nace "gaskiya kam, duk wanda Hafsat ta bude baki tace tana so to ya kamata azo kallonsa" bata kulamu ba saboda in miskilancin Hafsat ya tashi mu din ma bamu ishe ta kallo ba.

Satin mu biyu a Abuja muka tafi 'yalleman. Murna a gurin su inna ba'a magana. Tana ganin mu tace "lah, England din ce haka? Anya ba za abar karatun nan ba kuwa? Kar kuzo wata rana mu kasa gane ku saboda kun zama irin 'yan can" na rungume ta nace "we miss you too innarmu, in mun tashi tafiya next time tare zamu tafi dake saboda kullum kike ganin mu dan karki manta mu" ta rungume ni itama tana cewa "na ki wayon, salon mu tafi da Baffa ki kwace min shi da wannan kyan ka kike yi kullum bayan ni tsofewa nake yi" Amina tace "kai Inna, ai kamar ku daya ke da Moon"

Naji dadin zuwan mu 'yalleman dan ba karamin missing din su nayi ba. Nan da nan fara bin 'yan'uwan mu gida gida ina gaishe su kuma kowa sai na kai masa kayan tsaraba, har kayan da na siyo musu suka kare na fara diban kayan mu ina rabarwa. Nan take samari kuwa su kace dawa Allah ya hada su ba da ni ba, babu shiri na koma daki kusa da Hafsat na zauna na daina fita, amma duk da haka ban tsira ba saboda har gida ake aiko wa wai ana sallama da Maimunatu, Hafsat tana ta yi min dariya wai wa ya aike ni fita yawo a garinnnan.

Rannan muna zaune a compound din gidan sai Daddy ya shigo zai gaishe da mutan gidan kamar yadda ya saba. Inna ta aika ni na dauko masa carpet a cikin gida aka shimfida masa, duk ya gaishe su mu kuma muka gaishe shi. Sai Hajja tace "ni kuwa Muhammadu ina son magana da kai, da Adama naso muyi magana da ita amma sai nayi tunanin kar ta ce bakin ciki nake yi wa jikokinta" ina jin haka nasan maganar mu zatayi masa.

Daddy ya gyara zama yace "to Hajja ina jinki" tace "anya Muhammadu yaran nan ba za ayi masu aure haka ba? Yanzu ka ɗebi yara mata ka tafi dasu kasar waje wai da sunan karatu? Wanne karatu mace zatayi wanda ya wuce na dakin aure? Ni dai a shawara ta ka dawo dasu nan, ga 'yan'uwansu nan sai a hada su auren zumunci, ga Nuraddeen nan shima in karatun ne ai yayi, ya gama degree dinsa a BUK, ga Balarabe, ga Manniru duk babu abinda suka rasa. Ni tsoro yaran nan suke bani musamman wannan tsagerar" ta fada tana nuna Hafsat, "yanzu ma tana mana kallon wulakanci ballantana nan gaba in tafi haka? Ai cewa zata yi bata taba ganin mu ba"

Daddy yayi ajiyar zuciya yace "to Hajja, ni ban taba tunanin hana su aure ba, ko yau suka fito da miji aure zanyi musu" Hajja tayi sauri tace "yo ai indai wadannan ne ba zasu fito da miji ba, ai indai ana so ayi wa wadannan aure to sai dai a fito musu da miji" Daddy ya sake cewa "shikenan Hajja, yanzu abinda za'ayi ki kira su samarin ki ce su zo suyi magana da su Hafsat din, indai sun fahimci juna a tsakanin su to na miki alkawarin baza mu bar garin nan ba sai da auren su aka".

MaimoonWhere stories live. Discover now