For You, Only You

8.7K 669 2
                                    

Washegari da sassafe Sultan ya kira ni yace min ya tafi office, yana da meeting very early, dan haka nima ban tashi da wuri ba, ina jin Mommy kusan shigowarta uku tana dubani, sai kusan karfe 12 na tashi, shima kuma yunwa ce ta tashe ni, nayi wanka na shirya cikin wasu riga da skirt english wears tunda duk kayana sunyi min yawa yanzu, nayi packing gashina a tsakiyar kai na sauko kasa, a kitchen na samu su Mommy already suna aikin abincin lunch, na gaishe da Mommy ta amsa tana kallon kayan da na saka, na jawo kujera na zauna nace "Ma'u ki kawo min taimako, yunwa na ke ji" da sauri Asma'u ta ajiye aikin da take yi ta fara hado min tea, na karba na fara sha sannan ta zubo min farfesun naman ragon da suka gama hadawa ta hado min da bread, na karba ina ci ina santi, Mommy tace "aikin kenan, amma in akace kiyi garki ba zaki yi ba sai dai a girka ki ci, ni ban taba ganin macen da bata son girki ba irin ki Moon"

Furaira ta karba "kuma gashi gwanin nata gwanin abinci ne ba" a tare muka watsa mata harara ni da Mommy, tayi sauri taja bakinta tayi shiru, can Mommy tace "ke Furaira ya akayi kikasan saurayinta ne?" Furaira tace "nima Mommy wallahi a gurin 'yan waje nake ji, shi yake gaya musu" a raina nace "zai aikata"

Asma'u tace "kar ki damu mai sunan Daada, duk sanda akayi bikin ki gidan ki zan koma inyi ta dafa muku abinci ke da mijin ki" nan itama ta karbi nata rabon hararar daga Mommy. Sai da na gama cin abinci na sannan Mommy tace "ku bata suyar friend rice din nan tayi" na fara yarfe hannu ina kallon Mommy kaman zanyi kuka "Mommy wallahi kone wa zanyi, ni kuba ni in yanka muku wani abu, ni zafin wutar ne bana so" Asma'u ta biye min "dama wannan jikin naki haka babu tsoka ina zaki iya juya shinkafa? Bara dai in baki ki hada fruit salad" nan na kama murna na zauna dishen a kasa na nade kafa, Maryam tace "so take fa ta gudu, ai tana zuwa kitchen zata ce a bata yanka, daga nan zata yanke hannu sai kuma ta tashi ta fita shikenan ba zaki kara ganin taba sai akan dining table" duk suka saka dariya, na bata rai nace "ke Maryam har zaki nuna min aiki da wuka? Da likita fa kike magana" daga nan sai na fara basu labarin yaddda muke buda kan mutum mu bude kwakwalwarsa mu yi masa aiki sannan mu mayar mu rufe, ban ankara ba ina ta surutu sai gani nayi ana juye fruit salad din a bowl, har an gama hadawa, na dauko cup aka zuba min na koma gefe na fara sha ina cigaba da labari na.

Tsayuwar mota muka ji a waje, Mommy ta kalleni tace "madam ki je ki chanza wadannan kayan na jikin ki, dan wannan tsageran yaron bashi da linzami a gidan nan, har kitchen din nan zai iya shigowa" nace "Mommy kaya na duk sunyi min yawa ne wallahi" tace "to sai ki saka wadanda suka fi wadannan girma ko kuma ki saka dogon hijab" nace "yes Mommy" har zata fita tace "kar ki yarda fa inzo dining in tarar dake da kayan nan sai ranki ya baci" da sauri na mike na riga ta hawa saman.

Sai da nayi alwala na saka dogon hijab dina nayi sallah sannan na dan gyara fuskata na sauka kasa, ya Habeeb na tarar a palo, na zauna muka fara hira sai da ga Daddy, ya Walid da Sultan sun dawo, daga gani daga masjid suke. Ko kallon inda Sultan yake banyi ba na gaishe da Daddy, duk da ina jin idanuwansa a kaina. Daddy ya fara yi mana zancen convocation din mu da za'a yi next week, kuma duk tare za'ayi har dasu Faruk. Nan muka kama murna. Saukowar Mommy ce ta katse mana hayaniyar mu, gaba daya muka juya muna kallonta, tasha ado tun daga sama har kasa, tayi kyau sosai dan bazaka kalleta ba kace ta haife ni ma ballantana ya Walid daya doshi 30 years. Tana zuwa ta gaishe da Daddy, su kuma duk suka gaishe ta har Sultan, ta amsa ba tare da ta kalle shi ba, sannan tace "ga abinci nan a dining" ta mike ta tafi, muma duk muka bi bayanta. Muna zama na tashi na fara zubawa kowa abinci, sakwara ce da miyar vegetables, fried rice da hadin salad sai farfesun naman rago, sai kuma fruit salad. Kowa farfesu na fara zuba masa sannan kuma sai in tambaye ka me kake so a cikin sakwara da shinkafa sai in zuba maka, amma da nazo kan Sultan ban tambaye shi ba na xuba masa fried rice da salad da yawa amma na ciccire tumatir din cikin salad din, duk abinda nake yi idon kowa akaina yake, ina gamawa yace min "thank you" ban amsa masa ba na koma na zauna.

Ya Habeeb ne ya kasa shiru yace "shi Sultan mai yasa ba'a tambaye shi abinda yake so ba? Idan kuma ransa yafi son sakwarar kuma fa?" A hankali nace "baya cin sakwara ai" ya Walid yace "wow, yanzu kai zama kayi kai ta lissafa mata abincin da kake so da wanda baka so?" Daddy yayi gyaran murya duk kowa yayi shiru.

MaimoonWhere stories live. Discover now