The Prince

9.1K 866 10
                                    

Sultan gaba daya ya rikice min, wai shi lallai sai na fada a gida cewa aure nake so, kaji mutum, kuma shi in nace masa ya fada sai yaki. Dole yanzu na fara rage doguwar hira dashi, a waya ma kuma sakin layi yake. Gaba daya ni yanzu lamarin sa tsoro yake bani, kuma gashi Daddy ko mentioning zancen mu baya yi, ballantana Mommy da ko maganar ma bata so ayi. Da yaga na fara gudunsa sai ya tsiyo da zancen driving lesson, Daddy ya gayawa, daddy kuma yace muke yi da yamma in ya taso daga office.

Ni dai nasan ba wani abin arziki za'a koya min ba amma dai haka nake binsa muna fita, in muka je rabi lesson rabi hira. Rannan nace masa "to wai kai me yasa ba zaka je ka tambayi Daddyn ba? Ai kun fi kusa dashi, ko kasa yaya Walid ya tambayar maka" yayi shiru yana kallona sannan yace "Daddy has done so much to me ne bana so inyi disappointing dinsa, bana so yaga gazawa ta ko kuma yayi tunanin dama abinda nake after kenan kawai. Nafi so ace shi yayi min magana da kansa. Amma gaskiya na gaji da jira, I don't know how long zai taking kafin yayi min maganar" ya dan bata fuska yana kallona "ke ko ajikin ki ma wallahi, hankalinki kwance ke ko shekara za'ayi a haka babu ruwanki ko?" Nace "wa ya gaya maka haka?" Yace "to ai bakya nuna wa. At least kema ki dan ringa nuna min kina so mana, at least sai in san cewa the feeling is mutual ba wai ni kadai na ke abuna ba"

Nace "Sultan komai fa da lokacin sa, musamman aure, in kaga anyi to lokaci ne yayi ba wai nuna ina so ko rashin nuna inaso bane zai sa ayi. Kai dai kayi ta addu'ah sai kaga komai yazo da sauki"

Sosai muke ta shirye shiryen haihuwar Hafsat, takanas Mommy ta dauko wata midwife suke kwana tare saboda in case ko haihuwar zata zo da daddare. Hafsat kam duk tayi laushi, bata da aiki sai cin abinci sai da yamma inna tafi driving lesson dina ita kuma ta tafi strolling. Kaya kam har dai da aka ware daki guda ake zubawa dan kullum sai an siyo wani abu na baby an ajiye, abinka da basaban ba tunda rabon mu da baby a gidan tun Faruk, Faruk kuwa yanzu in aka ce min yana da budurwa ba zanyi mamaki ba. In dare yayi kuwa Hafsat bata zaman palour tana daki makale da zayed a waya har sai tayi bacci. Ni kuma kullum da daddare bayan an gama dinner zamu zauna hira da Sultan, Mommy ta hana mu hira a part din maza tace muke zama a compound in da mutane za suke ganin mu, shima Sultan dana gaya masa abinda Mommy tace sai cewa yayi "yauwa, ai gwara ma muke zama inda Daddy zai ke ganin mu yana tunawa da maganar mu"

Rannan ina gyaran kayana a daki kawai sai naga katin da Musbahu ya bani a agadaz, shaf na manta dashi ma ni, dan adam kenan. Na dauka na saka number din nayi saving as 'musbahu ngr', sai bayan da nagama aikina kaf sai na dauko wayar na kira number dinsa, nayi masa sallama ya amsa yace "sai yau kika tuna dani ko Moon?" Nace "lah ya akayi ka gane nice?" Yayi dariya yace "naga number din Nigeria kuma naji muryar mace, I have been expecting your call dama kuma shiru har na fitar da rai" nace "wallahi na rasa card dinne sai dazu na ganshi, ya su Mustapha da sauran 'yan gidan?" Yace "lafiya lau. Ina Sultan?" Nace "au baka manta sunan sa ba?" Yace "It is kind of special ne shi yasa ban manta ba" muka dan taba hira na kashe na ajjiye wayar, ni sam ban kawo wani abu a raina ba sai da daddare muna tare da Sultan ya karbi wayata yana kallon pictures din da mukayi dazu wajan koyon mota sai kawai naji an kira ni, na mika hannu ya ban wayata sai naga yanayin fuskarsa ya chanza, ya juyo min screen din na karanta 'musbahu ngr' wayar ta katse aka sake kira har ta sake katsewa bai bani ba kuma bai ce min komai ba.

Can dai yace "why is he calling you?" A ina ma ya samu number dinki da zai kira ki" na bata rai nace "dazu na kira shi muka gaisa. Yace in nazo Nigeria in kira shi, tunda nazo kuma ban kira shi dinba saboda nama manta da maganar sa sai dazu" nan take naga yanayin fuskarsa ya chanza "ina ruwanki dashi to da zaki kira shi, yanzu gashi ya samu number dinki kuma har yana da guts din da zai kira ki yanzu da daddare" nace cikin lallashi "Sultan, gaisawa fa kadai muka yi, har tambayata kai sai da yayi, he means nothing, kuma ya taimakamin wallhi, badan shi ba maybe da har yanzu ina agadaz" Sultan yayi chuckling yace "he is fooling you, kuma zancen taimako ke fa kike gayamin kullum cewa komai yana da lokacinsa, dan haka tunda lokacin dawowar ki gida yayi dole sai kin dawo with or without his help"

MaimoonWhere stories live. Discover now