Riyadh

10.2K 744 0
                                    

Sai da naji daukewar numfashinta ta cikin wayar, sai kuma ta fara maganar da sauri cikin rawar murya kamar mai shirin yin kuka "what? What did you just said? Sultan is your husband? Yana ina ? Yana kusa dake?"

Nace "yana jin duk abinda kike fada Ummee" ta sake cewa "what? Sultan? Kana jina? My son are you there?" Sultan ya taso da sauri ya taho inda nake zaune ya kwace wayar daga hannuna, ban ankara ba sai gani nayi ya buga ta da jikin bangon dakin, a take ta tarwatse a kasa, ya tsaya yana kallona yana numfashi sama sama tamkar wanda yayi gudu, sannan kuma ba tare daya sake cewa komai ba ya juya ya shiga kofar corridon da zata kaika bedroom dinsa, yana shiga ya bugo kofar da karfi har sai da dakin yayi motsi.

Na mike tsaye ina kallon kofar, dama nasan sai munyi drama da sultan akan ummeen sa, amma na shirya damarar sai na daidaita su, so help me God. Na karasa inda pieces din wayata suke na durkusa na tsince, wannan wayar ta gama yawo sai dai kuma wata ba ita ba, na zare sim card dina da memory card na tattara sauran na zuba a wastebasket, na kashe kayan wutar dakin na rufe koina na bishi dakinsa, ina shiga na tarar dashi a kwance a kan gado ko kayan jikinsa bai cire ba, idonsa a rufe kuma nasan ba bacci yake ba, na shiga toilet nayi shirin kwanciya nazo na saka wata T-shirt dinsa babba wacce tazo min har chinya ta, har yanzu yana nan a yadda yake, na kashe fitilar dakin na hau gadon nayi addu'ah sannan na jawo pillow na can nesa dashi na kwanta na juya masa baya.

Ko minti biyu banyi da kwanciya ba na jishi ya mirgino ya dawo jikina, ya saka hannuwanshi ya zagayo ni ta baya, bance masa komai ba, mun jima a haka sannan naji yace "why did you call her bayan na gaya miki I want nothing to do with her?" Nace "bani na kirata ba ai, ita ta kirani" yace "amma ai ke kika saka har ta kira ki din, kina sane ai" nace "afuwan, ayi hakuri" yace "please don't call her again" nace "I don't even have her number ta yaya zan kirata? Besides, ka fasa min wayar ma" yace "I will get you another one tomorrow. Ko ta kuma kiranki kar ki dauka, am doing perfectly fine without her"

Na juyo ina kallonsa na bata rai duk da nasan duhu ne ba gani zaiyi ba, nace "why are you blaming her wai? Bayan kasan bata da laifi" yace "she left me, shine laifinta" nace "she didn't, a gaba na Takawa ya gaya maka a ka aka dauke ta aka fita da ita, what is her fault in that?" Yace "she should have come back for me, why didn't she look for me all these years?"

Nace "bansani ba Sultan, amma nasan dole tana da dalilin ta, uwa tafi gaban komai a duniyar nan. Ba zaka san dalilin da yasa bata dawo ta neme ka ba har sai ka bata chance, har sai kayi magana da ita, idan kunyi maganar kaji cewa hujjarta is not good enough nayi maka alkawarin ba zan sake yi maka maganar ta ba" na daure shi da jijiyoyin jikinsa, bashi da amsar da zai bani sai cewa yayi "maganar ta isa haka. Let's sleep".

Washegari na daura niyar fara abinda zan yiwa Sultan, dan haka dana hada mana breakfast sai naci nawa a kitchen na kawo masa nasa great room dinsa, nayi tafiyata dakina. Ina zaune a palo ya shigo, naji kamshin turarensa amma ban dago na kalleshi ba, yace "me yasa baki zo munci abinci tare ba?" Na bawa iska ajjiyarsa, ya karasa shigo wa dakin ya tsaya a gaba na, ya shirya alamar office zai fita, kallo daya nayi masa na dauke kaina, yace "magana fa nake miki Moon" na yamutsa fuska nace "naji ai, nafi son cin abincin ni kadai ne shi yasa" ya saka hannu ya juyo da fuskata yace "wai duk akan maganar wayar ne? Yanzu kafin inje office ma zan siya miki wata" bance masa komai ba kuma ban kalle shi ba.

Ya dora lips dinsa akan nawa yana kissing, na kwace fuskata na mike na bar gurin ina juya masa bombom, ina shiga daki na bugo kofa ta da karfi irin yadda yayi min jiya.

Ranar Amir ne yazo daukar musu abinci, yana zuwa ya miko min waya yace "gashi inji oga kwata kwata, yace yayi miki charge, kuma ki kirasa yanzu" na karba nace "to nagode" yace "ki kirashi fa, dan tun safe yana can ya kasa zana komai, yace rashin jin muryarki ne" na kirkiro murmushi nace "zan kira ai" Amir yana fita na jefar da wayar akan kujera nayi tafiya ta daki.

MaimoonWhere stories live. Discover now