The Light

11.5K 710 6
                                    

Muka kalli juna ni da Sultan sannan muka kalleta, she was blushing, Sultan ya mike tsaye bacin rai a rubuce a fuskarsa yace "wait, what? Aure? Who did you marry? Kawai dan ki zo Nigeria sai kiyi aure?" Duk kallonsa muke yi daga ni har Ummee, ya fara zagaye palon yana magana "koma waye I will have nothing to do with him. Tunda kin aure shi ya kawo ki Nigeria shikenan mission accomplished, ya sake ki kawai ki dawo gidana ki zauna, in ma ba kya son zama a gidana sai in sai miki wani gidan ki zauna, but I don't want to see any man near you" ni kam dariya kamar zata kwace min ganin yadda ya hakikance yake fada, lallai kishi kumallon maza, lol, tabbas da ace Ummee tayi aure da anyi drama da Sultan.

Ummee tace "Sultan, you shouldn't judge people before you get to know them, give him a chance, yana da kirki sosai, you will like him" da sauri yace "I won't. Kuma ma nasan tunda da gaggawa akayi auren yanzu haka baki gama sanin halinsa ba, he may even be a 419 guy for all we know, ko kuma ma arm robber, Nigerians are not like Arabs, ba'a saurin trusting mutane anan Ummee".

She was calm duk wannan fadan da yake yi ni kuma dariya kawai nake boyewa tace "Sultan, I know him tun kafin musan zamu haife ka, zan iya cewa I knew him more than anyone a wancan lokacin, kuma har yanzu ma he hasn't change a bit" ya tsaya da zagayen da yake yana kallonta, sai a lokacin dariya ta kwace min, ya juyo yana kallona fuska a daure yace "menene abin dariya kuma?" Na tsaya da dariyar da nake nace "Sultan, Ummee is trying to tell you cewa sun mayar da auren su ita da Takawa" ya dan jima yana kallona inayi masa murmushi, sai kuma ya juya ya kalli Ummee, ta gyada masa kai, a hankali kuma kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki sai ya dawo ya zauna a kusa da ita.

Ta saka hannu tana shafa gashin kansa, tace "you look so much like your father when you are angry" yace "amma Ummee me ya faru? Ji nake fada kuke yi da Takawa" ta danyi dariya tace "dama can kullum fada muke yi dashi, he is so stubborn and hot headed like you" ya kwantar da kansa a kafadar ta ya zagaye ta da hannayensa yace "I love you, Ummee" na mike a hankali na koma cikin gida, ina jin dadin auren Takawa da Ummee a raina amma deeply kuma ina alhinin rashin Baffa.

Washe gari da wuri Takawa yazo, da jiniya da hakimai da dogarai da komai yazo, Allah bai yi zasu gaisa da Baffa ba. Kofar gidan Baffa kuwa ya cika taf da mutane sunzo ganin sarkin Abuja. Ya jima a gurin su Daddy sannan ya aiko aka kira ni, muka tafi tare da mata da yawa muka gaishe shi yayi mana gaisuwa sannan muka dawo cikin gida.

Bayan azahar aka aiko su Ummee su fito zasu tafi, Ummee dama ta shirya amma muka nemi Huda muka rasa, gashi kuma ta bar handbag dinta da wayarta a ciki ballantana a kira ta, ni da Amina muka fita daki by daki muna nemanta amma shiru, gashi ana ta jiransu a waje, na zagaya bayan dakin Hajja inda take 'yan shuke shuken ta kawai sai na hango hijab din Huda a bayan katanga, na kara sauri sai na hango tare suke da wani namiji, gaba na ya fadi, na shiga yi uku ni Maimunatu, kar dai Munir ne ya ja 'yar mutane bayan gida zai lalata musu yarinya inzo inji kunya.

Ga mamaki na ina zuwa sai na ga Faruk, na tsaya ina kallonsu duk basu san ma nazo gurin ba, Faruk ya karkace a jikin gini yana ta zuba mata tsari ita kuma ta sunkuyar da kai kasa tana ta murmushi, nayi gyaran murya, suka juyo a tare suna kallona, da sauri ta ja hijab dinta ta rufe fuskarta shi kuma ya juya baya yana shafa keya, nace "ki zo ana jiranki zaku tafi" sumi sumi tazo ta wuce ni, bance masa komai ba na juya zan tafi, ya biyo ni da sauri, "ammm...... dama wai bata san kayan lambu ba shine nake nuna mata" ba tare dana kalleshi ba nace "to" a raina nace 'maida karuwa 'yar iska' wai dan karamin Faruk din nan ne har ya girma shima zai fara tsara 'yammata, sai kuma na tuno cewa yanzu fa service yake yi, dan haka ya girma kenan da gaske. Duniya kenan.

Muka fita rakasu Sultan yana ta bacin ran Takawa yace tare zasu koma, ni kuma sai anyi sadakar bakwai sai mu taho tare da su Mommy. Na san dan dai babu yadda zaiyi ne, gashi ko wata sallamar kirki bamu yi ba. Motar Takawa suka shiga, shi yana gaba kusa da driver, Takawa da Ummee suna baya a tare. Sai kawai na samu kaina da murmushin jin dadi. Suka shiga motocinsu suka tafi mu kuma muka koma gida.

MaimoonWhere stories live. Discover now