The Goodbye

6.7K 619 4
                                    

Hafsat ta tsaya saroro tana kallona. Sannan ta sunkuyo saitin fuskata tace "yanzu ke Moon kina ganin har kinyi girman da zaki fara soyayya? Har kina ganin kin isa ki yanke wa kanki hukunci? Har kina ganin kin san menene dai dai menene ba dai dai ba?" I was ready for her dan haka ko gezau banyi ba nace "7 years ago, sanda nace inna girma ina so in zama neorosurgeon murna kuka yi ta tayani kuna cewa nayi making right decision, ta yaya kuma yanzu zaki ce min ban isa in making decisions ba? I know what I am doing I just need you to support me please" Tayi min wani kallon wulakanci tace "lallai yau na tabbatar baki da hankali Moon" tayi tafiyar ta ta zauna. Nayi shiru ina tunani, lallai Hafsat bata gama sanina ba har yau.

Mutane da yawa suna cewa I am a genius, amma ni ban yarda ba, na san dai ina da brains kuma I am going to use it here. Tabbas nasan ina son Ibrahim amma hakan bazai sa in barshi yayi messing with my life ba. I said yes to him saboda bana son ya bar makarantar kamar yadda yayi threatening amma hakan ba yana nufin za muyi soyayya bane ba. In dai har yana sona zai jira ni har in gama secondary school in kara girma sannan we will see what will happen.

Na gama tsara komai yadda nake so ya kasance. Abu na farko shine; ba zan ke bari muna kebewa ni da shi ba alone. Dan haka ana yin break na tashi a class nayi announcing cewa ina gayyatar duk wanda yake da ra'ayi zamu ke karatu tare. Kusan rabin class din suka ce suna so, nan muka zauna muka tsara timetable ta karatu, kullum da akwai subject din da zamu keyi, za muke fara wa 3pm mu gama 6pm. Nayi inviting duk class din ne saboda nasan kullum dole wani zai zo, baza mu kasance daga ni sai Ibrahim ba.

Abu na biyu da nayi shine na fito da duk textbooks dina na jera akan desk dina yadda babu yadda za'ayi mutun ya zauna akai, no more sitting on the desk tactic. Iyakacin sa sai dai ya tsaya a gaban board ya gama abinda zai yi ya fita. The next thing da nayi shine ana tashi a school na tafi gurin HOD na Islamic studies na kai masa complain cewa ina so a chanja min class din islamiyya amayar dani B class, dalilin dana bashi shine ina son raba aji da Hafsat dan tana distracting dina. Da kyar na samu ya amince shima saboda muna mutunci dashi sosai tun jss1.

Nasan in Ibrahim ya fahimci abinda nayi he will be mad but I am ready for him.

Ai kuwa sanda ya fahimci na chanja class a islamiyya he was furious. Muna zaune muna karatu a new class dina sai gashi ya shigo ya bawa yasaiyadin mu hannu suka gaisa sannan yace "I will like to see one of your students please" nasan ni yake nema amma sai naki dago kaina na dukufa ina karatu, ya sayyadin yace masa "kadan yi hakuri in ba emergency bane yanzu muna karatu in mun  gama sai tazo" Ibrahim yayi masa godiya ya fita. Sai da naga saura less than ten minutes mu tashi kuma na riga na biya karatu na sai na tambayi yasayyadi nace zan je toilet, yace min ai it is almost time inna tafi inyi zamana kawai, dama haka nake so dan haka na dauki books dina sai hostel. Hafsat tana zuwa ta fara tuhumata akan menene yasa na chanja class nace mata its none of her business.

Ranar da Ibrahim yazo mana maths yaga na cika gaba na da texbooks, kawai ya tsaya yana kallona ni kuwa na dauke kaina kamar ban san yana yi ba. Duk yadda yaso in kula shi naki yarda har period dinsa ta fita, yazo ya tsaya a gabana yace "see me immediately after school" nace "yes sir" amma ko kadan banyi niyyar zuwa ba. Da yamma muka shirya wajan mu biyar muka fita karatu. Muna zuwa muka yi arranging chairs muka samo wani babban table muka saka, mun fara karatu kenan sai ga wasu ma sunzo, haka muka hadu wajan mu goma, muka shiga library muka karbo aron books da syllabus din term din muna tsara yadda zamu fara karatun sai ga Ibrahim.

Tsayawa yayi yana kallon mu fuskarsa cike da mamaki. Yayi kwalliyarsa da sabuwar shadda sai, kamshi yake yi. Ya jingina da jikin library ya rungume hannayensa a kirjinsa ya zubo min ido, kallo daya nayi masa na dauke kai naci gaba da abinda nake yi. Amira ta taba ni tace "mutumin ki fa ke yake nema" nace mata "I know" na cigaba da karatu na, can ta sake cewa "duk wannan kwalliyar fa ke akayi wa" na sake ce wa "I know" taga dai bani da niyyar kulata ta rabu dani, ita Amira bata san zafin da nakeji a raina ba, I missed him alot amma still I want to be strong, na leka ta saman littafina ina kallon shi naga ya dauko wayar sa yana dannawa, nan na samu damar kare masa kallo. Sabuwar shaddar sa kalar ash mai haske ta sha dinkin tazarce da aiki kalar ash mai duhu, hular sa da takalmin sa duk ash mai duhu ne, fatar sa tayi tas, fuskarsa fes kamar yanzu aka bare shi daga cikin ledar sa.

MaimoonDonde viven las historias. Descúbrelo ahora