A Pink Handkerchief

6.8K 642 4
                                    

Har na karasa dakin mu ina tunanin maganganun Amira. Tabbas duk abinda ta fada gaskiya ne. I know my biology and I know I am in adolescent stage. But am I really attracted to Ibrahim? It is not as if we are in love or something amma kuma do I even know what love is? Am I ready for this? Har na kwanta ina ta lissafi a raina.

Soyayya da Ibrahim ba abu ne me yiwuwa ba. Wata tafiya ce mai tsaho. Family na, familyn shi, everyone will be against us. Hatta Hafsat ta saurara masa ne yanzu saboda nace mata ba soyayya tsakani na dashi. But i know what I am feeling. Ba zance ina son shi ba saboda ban san menene son ba. Amma nasan ina son kasancewa tare dashi, yana sani dariya, kuma duk sanda bana tare dashi inajin kamar ina missing wani abu. Is this love 💟?

Ni na san ba zan iya yiwa Hafsat wannan tambayar ba in ba so nake in tsokano tsuliyar dodo ba. Tambayar da nake yiwa kaina itace: if abinda nake ji shine love din, am I willing to take the chance for him? And more important, is he willing to take the chance for me?

Tun daga lokacin sai na samu kaina da yin baya baya da Ibrahim. Bana barin mu hada ido dashi sam, in ya taho zai rako ni kuma na kan jawo Amira ko Hafsat mu tafi tare, ita ma kuma Amiran ba ta ki saboda ta fahimci maganar da tayi min rannan ne ta saka nake gyarawa. Kullum in muna tafiya kuma maganar mu bata wuce ta karatu ko labarin gida.

Muna haka har muka fara exams komai ya koma serious, Amira ma tayi joining karatun mu, kullum tare muke karatu mu uku shi kuma Ibrahim in mun gama sai ya dunga yi mana questions muna amsawa. Ana gobe zamu yi hutu mun fito daga Exam sai Ibrahim yayi kirana, muka tafi ni da Amira. Muna zuwa muka tarar dashi yana waya. Sai da ya gama wayar sannan ya kallemu yace "so you guys are going home tomorrow, right?" Amira tace "yes sir" yayi dariya yace "oh su Amira harda saurin amsawa ko? Wato kin gaji da ganin mu ko? Dadinta dai muma gidan zamu tafi muma mu huta" sai a sannan nayi magana nace "are you going home also" ya kalleni da seriousness yace "yes, I am going tomorrow, there is nothing for me to do here in kun tafi" na hadiye wani kululu da ya tsaya min a wuya na nace a hankali "ok". Mukayi shiru for sometimes sannan yace "I will see you guys tomorrow before you go" Amira ce kawai ta bashi amsa da ok sir. Daganan muka tafi hostel.

Duk jikina a sanyaye nake shirin tafiya, tamkar wacce ta tashi daga jinya haka nake ji na. Washegari tun a assembly ground nake ware ido ko zan ganshi amma babu shi babu alamar sa. Gashi wannan abun da ya tsaya min a makogwaro na har yanzu yaki wucewa. Wajen karfe goma aka bude gate motoci suka fara shigowa. Hafsat sai ware ido take tana neman motar gidan mu ni kuwa addu'a nake yi a raina kar su zo yanzu sai na ganshi. Muna cikin haka na hango motar mu tana shigowa, na lura Hafsat bata ganta ba sai nayi sauri nace mata "Hafsat zan dan je toilet kafin azo daukan mu" batare data kalli inda nake ba tace "ok" na juya da sauri nayi hanyar classes ina ta waige waigen ko zan ganshi, har naje gate din hostel ban banshi ba, kuma na tarar har an rufe get din dan haka na juyo, hawaye naji mai zafi yana tahowa daga kirjina amma naki na barshi ya karaso idona saboda kar a gani a tambayeni dalilinsa.

Ina tafiya kaina a kasa naji an kama hannuna an jani da sauri cikin wani class, da sauri na kwace hannuna ina neman hanyar gudu sannan naji wannan mayataccen kamshin nasa ya ziyarci hancina, na juyo da sauri muka hada ido. Ya saka complete kaki na NYSC a jikin sa, p-cap din ya juya ta tana kallon bayansa, da backpack a goye a bayansa. Fuskarsa babu murmushi. Mun jima muna kallon juna sannan nace "I thought ka tafi" ya hadiye yawu adams apple dinsa ya motsa sannan yace "I am sorry, an kira mu meeting ne tun safe, I was really pissed na dauka bazan same ki ba" naji dadin maganarsa har cikin raina, take naji wannan kululun da ya tsaya min a wuya ya narke yana tafiya.

Nayi murmushi nace "I was afraid ka tafi without saying goodbye" ya matso gaf dani yanda har muna iya jin lumfashin juna, sa saka hannayensa biyu ya ruko fuskata idonsa cikin nawa yace "I will never" a can kasan zuciya ta nake jin tana min warning cewa in kwace fuskata daga hannunsa in matsa daga kusa dashi amma jikina yaki yayi responding, na kasa koda dauke ido na daga cikin nasa ballantana in matsa. Mun jima a haka kamar masu haddace fuskokin juna sannan kuma ya sake ni da sauri ya juya bayansa ba tare da ya sake kallona ba yace "go Maimunatu, just go" da sauri na bude kofar class din na fita kirjina yana bugawa da karfi amma kuma ina jin tamkar na bar zuciyata a cikin ajin.

MaimoonWhere stories live. Discover now