His Everything

11.7K 738 2
                                    

A hankali na bude ido na ina ji a jiki na kamar assuba tayi ko kuma ma ta wuce. Dakin naga da duhu kamar cikin dare amma jikina yana bani assuba ce. Abinda ya faru da daddare ne ya fara dawo min a raina, sai a lokacin na lura cewa a jikin mutun nake a kwance. Wata muguwar kunya naji ta kamani kamar in tsaga gadon in shige cikinsa, gani nake kamar a mafarki amma kuma nasan ba mafarkin bane. Na daga jikina a hankali da niyyar sauka daga jikinsa, wata 'yar karamar kara na saki na koma na kwanta, gaba daya kafafuwana sunyi tsami, jikina gaba daya ciwo yake yi, na sake gwada kokarin tashi amma shima sai wani karin ciwon ma kamar dadamin ake yi. Na koma na kwanta ina kwalla silently.

Motsin Sultan naji alamar ya farka amma na kasa dago kaina saboda bana jin zan iya hada ido dashi yanzu, ya sa hannu a hankali yana kokarin dago fuskata amma naki yarda na kara cusa ta a cikin wuyansa, ya rabu dani yace "menene kuma? Sai kin kara wa kanki wani ciwon da kukan nan ko?" Banbashi amsa ba naci gaba da kukana, kokarin daga ni daga jikinsa ya fara yi, ai kuwa na saka masa kara ina dada kankame shi, ya cika ni yace "ciwon ne dai?" Na gyada kaina, ya fara shafa bayana a hankali yana noticing temperature dina data fara hawa, yace "am sorry Love, bara muyi sallah sai muga ya za'ayi da ciwon nan"

Cikin kuka nace "ni ka kaini gida gurin Mommy" da sauri yace "what? So kike Mommy ta tsire ni a kasuwa? In na kaiki gida a haka ai kamar na nuna am not responsible. Ki bari inyi sallah sai in duba ciwon in gani, in naga yana bukatar doctor da akwai doctor din gidan nan sai inyi masa magana ya samo mana gynecologist mace sai tazo ta dubaki" na makale kafada, yayi ajjiyar zuciya yace "OK, to ke ki rubutamin magungunan da kike ganin zasu yi miki amfani sai inje in siyo miki" na sake makale kafada, yace "to fada min me kike so, banda zuwa gida" nace "ni dai ka kira min Hafsat" yace "kinsan dai Hafsat tayi fushi ko na kirata ba zata dauka ba" nace "ni ka bani wayata, in na kira ta zata dauka" yace "to daga  ni in dauko miki wayar" na sake makale kafada, yayi 'yar dariya yace "wannan dai ba ciwon bane kadai har da shagwaba ko?" Nayi shiru bance komai ba yace "bara inyi maganin shagwabar"

Juyi daya yayi ya mayar dani kasa, na bude baki zanyi kara ya rufe min bakin da nasa, sai da ya tsotse duk shagwabar da nake ji da ita tas sannan ya sakeni, still yana kaina amma ya rage nauyin sa da hannayensa, na rufe bakina da hannuna nace "banyi brush ba fa" yayi murmushi yace "nima haka"

Daga haka ya mike ya shiga toilet, ya fito da alwala, sai da yayi sallah sannan ya dawo inda still nake kwance ba tare daya ce min komai ba ya dauke ni ya kai toilet, da gaske ciwon nake ji ba wai shagwaba bace, dan kafafuwana jinsu nake kamar lagwani, da nayi alwalar ya dawo dani daki ya sakamin doguwar riga ta da hijab dina ya zaunar dani akan sallaya nayi sallah, ina idarwa ya shigo da tea a hannunsa ya zauna ya fara bani, naki sha sai da yace min inna shanye zai kira Hafsat, na sha kamar rabi nace na koshi, kan gado ya sake mayar dani ya lullubeni. Ya dauko min wayata ya dawo kusa dani ya kwanta yace "to kira Hafsan, tunda kince ita kike so" na duba time naga 6:30, na kira number din Hafsat, ringing biyu ta dauka, sai kuma na rasa me zance mata, tace "I know you will call me dama, check your messages, na bar miki sako" daga nan ta kashe.

Sultan yace "me tace?" Na gaya masa, ina duba wa kuwa naga message daga Hafsat
"you once asked me what it feels like, yanzu nasan kin sani. Was Sultan gentle? If he wasn't please knock his big head for me. I left something a bedside drawer dinki and I also left you farfesu a cikin fridge, for you alone, kar ki bashi ko loma daya"

Ina gama karantawa na tattaro dan sauran karfin daya rage min na rankwashi Sultan aka, ya rike gurin yace "ouch, me nayi kuma?" na nuna masa message din Hafsat nace "sako ne inji Hafsat" ya shagwabe fuska "was I not gentle?" Nace "you weren't" yace "to ai ba laifi na bane ni kadai, why do you have to be so damn good. I always thought it will be good but did not expect it to be this good" nace "so it is my fault kenan ko?" Yayi dariya bai amsa ba ya mike yace "let me get sakon nata".

MaimoonWhere stories live. Discover now