The Visitors

8.8K 781 5
                                    

Ina dan bubbuga bayansa kadan nace "Nothing Sultan, You did nothing" yace "me yasa ya tsane ni to? Me yasa basu zubar da cikina ba tunda sun san basa sona?" Nace "Suna sonka Sultan, kawai dai basa nuna maka ne, amma deep down suna sonka sosai, maybe more than yadda nake son ka ma" ya sakeni yana kallon fuskata yace "don't say that, in kina son kwantar min da hankali na say something else amma ba wannan ba, cos nasan basa sona, tun kafin in san menene so nasan basa sona. They hate me and I don't know why, wannan shi yafi komai bata min rai, why do they hate me so?"

Bance masa komai ba saboda bansan me zance masa din ba. Ya zauna akan kujera ya zaunar dani a kusa dashi yace "tunda ya fara wannan maganar ba zai bar ta ba har sai yaga ya raba mu, I know him, zan shirya mana barin kasar nan, shine kadai hanyar da zamu bi mu tsira daga gare shi"

Na girgiza kaina nace "Sultan barin kasa ba shine mafita ba, iyayen mu ne, we are nothing without them and we can't runaway from them. Mafita shine mu zauna muyi facing din su mu yi duk abinda suka ce mu bar duk abinda suka hana mu. In mukayi haka to Takawa will have no reason da zai sa ya takura mana ko yayi tunanin raba mu. Amma in dai muka ce zamuyi retaliating ko kuma zamu bar kasar to anan ne zamu bashi damar yi mana duk abinda yake so"

Ya girgiza kansa yace "baki san halinsa ba, he will not stop, baya bukatar reasons, in dai yana son yayi min abu to tabbas zai yi min ne ko nayi laifi ko banyi laifi ba, ballantana yanzu yana ganin yana da dalili a hannunsa. Yanzu nasan Daddy zai kira ya nuna masa picture dinki da bindiga ya kuma gaya masa cewa nace nine na baki. The next thing you will know Daddy zai zo yace ki fito ku tafi an gama auren kenan"

Nace "then you don't really know Daddy. Daddy ba zai taba yanke hukunci ba tare da bincike ba, ni kuma in ya tambaye ni zan san yadda nayi nayi masa bayani yadda zai gane, kuma nasan zai gane din ma. Yanzu abinda nake so muyi magana akai shine; wa kake tunanin ya kaiwa Takawa pictures din nan?"

Wani murmushin takaici yayi yace "tunani? Am sure it was Abbas, ba yau ya fara ba ai, but this will be the last time da zai shiga harkata, dan wallahi sai jikin sa ya gaya masa. He shouldn't have touch you" yadda ransa yake a bace na tabbatar idan ya kama Abbas sai dai wani bashi ba. Na kama hannunsa ina shafa gashin hannun a hankali nace "wannan shine exactly abinda Abbas yake so kayi, so yake ka taba shi yadda Takawa zai sake samun karin dalilin raba ka dani. He got your weak point, me. Yasan cewa you will react exactly like this, yasan cewa in Takawa yayi maka magana zakace zaka dauke ni mubar musu kasar, yasan kuma Takawa zai ce ba zaka tafi dani ba. Ya lissafa cewa duk abinda ya faru shine mai riba, in ka tafi kabar kasar dani shikenan he got rid of you, in kuma bamu tafi ba zaku yi ta rigima da Takawa shima nan shine da riba"

He seems calmer now, yana sauraro na sosai, yayi ajjiyar zuciya yace "yanzu mai kike ganin zamuyi?" Nace "kar mu bawa Abbas abinda yake nema. Kar muce zamu je ko'ina. Kuma kar kace zaka dauki fansa akan Abbas, just let him be, duk abinda zai yi kar ka kula shi. Sai kuma muyi taka tsantsan, kar mu yarda muyi wani abinda muka san Takawa baya so. You already got your job, ka cigaba da abin ka, duk sanda kake bukatar fatherly care ko wata shawara, go to Daddy. The last and the most important thing shine mu dage da addu'ah. I believe Allah yana tare damu kuma yana ganin duk abinda yake faruwa kuma ba zai taba barin mu ba as long as muma bamu barshi ba. Yadda ba zamu bar Allah ba kuma shine ta hanyar ibada da addu'a. Kuma ka saka a ranka cewa I will never leave you, Ever. Duk ma wani abinda zai faru, we will face it together"

Na dago hannunsa na kai baki na nayi kissing, nace a hankali "I love you" ga mamaki na sai naga yayi murmushi, genuine murmushi, yace "I love you too".

A ranar Asma'u tazo, da gudu naje na rungume ta ina murna, itama murnar take yi, tace "me sunan Daada in dai girki kike so ki koya to ina tabbatar miki kin samu, dan bazan bar gidan nan ba sai na tabbatar babu wani abincin da baki iya ba"

MaimoonWhere stories live. Discover now