When Destiny Calls

7.9K 747 7
                                    

Daddy ya tashi ya shige daki. Yana shiga Hafsat ta mike ta fada cinyar Mommy ita kuma ta rungume ta suna dariya, nima dariyar nake yi amma ta yaqe ce, maganar Daddy ce take yi min yawo aka, tabbas nasan Munnir bashi da niyyar hakura, kuma nasan in har na gama school bani da wani sauran excuse, ballantana yanzu idan iyayen Zayed suka je neman auren Hafsat kowa kuma hankalinsa dawo wa kaina zaiyi.

Ina cikin wannan lissafin naji maganar Mommy wacce ta sake daga min hankali "ai naji yace ma indai har su Baffan sun amince acikin hutun nan naku yake so ayi komai a gama, in yaso kya karasa project dinki a gidan sa, kinga nan da baifi wata biyar ko shida ba za'a gama komai"

Hafsat ta boye fuskar ta a cinyar Mommy wai ita kunya, su yaya Habeeb suna ta tsokanarta da amarya, ni kuwa, shock din maganar ne ya daskarar dani a inda nake zaune, Mommy ta kara da cewa "ni dai kam ni aka tasa a tsaye, lokacin yayi min kadan gaskiya, saboda ni plan dina shine nan da kamar shekara biyu masu zuwa, so nayi yadda kuka taso tare ke da Moon in hada ku rana daya in aurar daku shikenan"

I have heard enough, na mike zuciya ta tayi min nauyi na kama hanyar fita, ina jiyo su suna ta making plans, Mommy ta kira Daada a waya tana gaya mata. Ina fita part dinmu na shiga, sai kuma na rasa me zan dauka, sai kawai na dauki hijab dina na saka na kama hanyar gate. Ni kaina bansan inda zani ba, I just want to get away for a while. Baifi saura wata biyu ya rage mana muyi hutu ba, muna yin hutu zamu tafi Nigeria. Allah ne kadai yasan irin abinda zan fuskanta a can. Dan jiki na yana bani Baffa zai iya cewa a hada aure na dana Hafsat, da zarar nace bani da saurayi kuwa za'a ce ai ga munnir nan yana ta zaman jira. Allah ya gani bazan iya auran munnir ba. I despise him. To ko Mahdi zan lallaba ne? But I don't love him and I will end up hurting him. Ya Ilahi.

Ina fita gate na hango motar Zayed a gurin da yake tsayawa in yazo gurin Hafsat. Na juya na fara tafiya in opposite direction, ina jinsa yana horn kuma nasan dani yake amma naki juyowa. Ban ankara ba sai ganin mota nayi a gaba na, yayi winding glass din motar ya kalle ni da murmushi a fuskar sa "beautiful one ina zaki je ne haka ke kadai kuma a kafa?" Nayi niyyar inyi banza in rabu dashi tunda duk shi ya ja min daya dauko maganar auren Hafsat amma kuma sai na kasa, it is not in my nature wulakanta mutane. Na karasa kusa da motar sa nace "nan baya zan je ba nisa" daga yadda yake kallona nasan bai yarda da maganata ba, ya bude kofar motar yace "shigo in kai ki" na danyi jim sai kuma na shiga. Ina zama yace "What is wrong" kawai sai jin hawaye nayi yana zubo min, nayi sauri na rufe fuskata da hannuna na fara kuka. Ya gyara packing din motar ya zauna, bai ce min komai ba, bai kuma rarrasheni ba, sai da nayi kuka na me isa ta sannan na buɗe fuskata ina goge idona da hannuna, ya miko min box din klenex, sannan ya sake tambayata "what's wrong?" Nan take na fara bashi labarin tun farkon haduwar mu da Ibrahim, aikin da na saka Daddy ya samo masa, graduation din mu, yadda ta kasance ranar da yazo gidan mu da tafiyarsa, dawowarmu England da labarin aurensa, na kara da cewa "har yau babu shi babu labarinsa, he might be dead for all I know. Amma na kasa chire shi daga raina, na rage tunaninsa amma na kasa mantawa dashi, and now I realized that I can't fall in love again" sannan sai na bashi labarin Munnir, na kuma bashi labarin Mahdi. Na kara da cewa "yanzu muna zuwa Nigeria aka fara maganar ku da Hafsat, shikenan hankalin kowa zai dawo kaina, ko dai in fito da miji, which I don't have, ko kuma a aura min Munnir, who I don't love".

Nayi shiru idona a lumshe ina sauraren yadda zuciyata take bugawa. Zayed yayi gyaran murya yace "do you want the truth? Or you want something that will make you feel better?" Ba tare da na kalle shi ba nace "the truth" A hankali yace "He is not coming back"

Na juyo da sauri na kalleshi ya gyada min kai tare da maimaitawa "he is not coming back" na dauke kaina na daina kallonsa, ya cigaba da cewa "he left because he is weak and unsure of himself, yes, sanda ya tafi maybe yana da niyyar dawowa sanda yaji he is strong enough, auren sa ya kara rage chances dinsa of coming back to you saboda matarsa zata yi iya kokarinta wajan janye hankalinsa daga kanki, da zarar ta haihu kuma shikenan hankalinsa zai kara karkata kan 'ya'yansa. After almost five years kuwa the chance of him coming back to you is zero percent. Dole ki saka a zuciyarki kuma ki yadda da fact that he is not coming back. Abu na farko kenan. Abu na biyu shine, dole kiyi opening heart dinki for another man. Love at first sight is very rare dan haka idan guy yace yana sonki kamata yayi ki bashi chance, get to know him sannan zaki san cewa you can love him or not. You are very young and very beautiful Moon, your life is just starting, kar ki bar wani can da maybe ya manta dake yayi ruining happiness dinki. Open your heart to both Munnir and Mahdi and whoever else comes your way. Kina jina Moon?"

MaimoonWhere stories live. Discover now