Khairat

9K 707 1
                                    

Ta sake ni ta kama hannuna muka karasa kan kujera, ta zaunar dani sannan ta zauna a kusa dani still tana rike da hannuna, tana min murmushi from ear to ear, na dan sunkuyar da kaina saboda kallon da take min, ta saka hannu ta dago habata, tace "masha Allah, you my dear are very beautiful" naji kunyarta na sunkuyar da kaina. Ta dora hannunta akan cikina tana dariya excitedly, hawayen cikin idonta ya saka idonta yayi maiko irin na Sultan tace "wata nawa?"

Ni dai duk kunya ta ishe ni, na kasa bata amsa, tace tana karkata kai "please kar ki yi min haka mana, talk to me, ki dauke ni kamar kawar ki kinji?" Na gyada mata kai, ta sake dora hannunta akan cikina tace "wata nawa?" Ina murmushi nace "almost four" ga mamaki na kawai sai naji babyn yayi motsi for the first time, itama taji a hannunta, ai kuwa murna kamar me, tace "shima yasan yazo gida" ta sunkuyo da kanta dai dai cikina tace "welcome home my little love"

Ni dai sai taya ta dariyar ta nake yi, sai da ta gama murnarta sannan tace "how is he?" Na san wa take nufi da he din, to amma na kasa sanin ta ina zan fara bawa uwa labarin danta wanda rabonta dashi shekara talatin? Jin bance komai ba yasa tace "ya kamannin sa suke yanzu" na dago kai na kalle ta nace "you just need to look in the mirror, he looks just like you" ta fadada murmushinta tace "but he has his father's built and temper" nace "yes, he do"

Ta sake juyo wa tana kallona tace "har yanzu yana da hot temper kenan? Sanda yana baby in yana son abu na hana shi sai yayi ta buga kansa a jikin bango, in na bashi abin ma daga baya sai ya karba ya jefar wai yayi zuciya" nayi murmushi, ta sake cewa "tell me menene yafi so duk duniya" na san me yafi so duk duniya amma am not going to tell her that, dan haka nace "food"

Ta bude baki da mamaki tace "har yanzu bai daina son abinci ba? Sultan har cikin dare yake tashi yaci abinci, sanda ina feeding dinsa sai da na hada masa da madara saboda tsabar cin sa, da ya fara wayo kuma babban abincin da yake so shine nama, daga nan sai fresh milk" nace mata "har yanzu ma, yana son nama sosai" tace "is he still making troubles? He was a trouble maker as a baby, yana da kiriniya sosai dan sanda ya fara crowling duk abinda nake so sai dai in dora a sama, a saman ma in ya samu abin takawa sai ya dauko, yayi ta faduwa yana jin ciwo amma sai ya koma"

Ina jinta ina ta murmushi a raina ina hango baby Sultan yana ta kiriniya da wannan thick gashin kan nasa, ta sake matse hannayena a cikin nata tace "please tell me all about him, nuna min pictures dinsa in gani" na dauko waya ta na zare sim card din dan kada Sultan ya kira, na kunna na nemo mata wani hoton Sultan wanda yake looking very good and decent, na mika mata, tana karba tasa hannu ta rufe bakinta tace "Ya Allah, he is so grown up and handsome" sai kuma hawaye ya fara zuba a idonta "my son, my darling baby"

Daga hoton dana nuna mata maimakon ta dawo min da waya ta sai ta fara scrolling tana kallon pictures din mu, mostly na Sultan ne da ni, sai na yan gidan mu, in tazo kan wanda bata gane ba sai ta nuna min ta tambaye ni in bata amsa, har yanzu hawaye bai daina zuba a idonta ba, kuka take kuma tana dariya duk ita kadai, ni dai ji nake kamar in karbe waya ta saboda da akwai hotunan da bai kamata ta gani ba, amma ita babu ruwanta, kallo take yi kawai tana dariya, ta dago kai ta kalleni tace "he really loves you, I can already see it in his eyes" na gyada mata kai nace "yes, he does" sai can kuma ta ajiye wayar tace "oh dear, ko ruwa ban baki kin sha ba"

Nayi dariya kawai bance komai ba, hannuna ta kama ta jani har dakin da na fahimci cewa bedroom dinta ne, ni dai kawai kallonta nake yi, she is really beautiful and amazing, in ka ganta daga nesa ba zaka taba tsammanin babba bace ba, sai in kun zauna da ita ka kalle ta sosai sannan zaka ga shekarunta a fuskarta, jikinta kam babu alamar girma a tare dashi.

Anan dakin nayi sallah, ina idarwa sai ga Hafsat tazo kirana in fito muci abinci, sai a lokacin na kalli Hafsat sosai, nace "yanzu Hafsat dama ciki ne dake baki gaya min ba" ta murguda min baki, nace "yanzu Khairat din watanta nawa har zaki yi mata sibling" tace "ke watanki nawa aka haifi Faruk? Ni wata na nawa aka haife ki? Me ya ragu a jikin mu? Ko wani mugun ciwo babu wanda yake dashi a cikin mu, itama Khairat babu abinda zai same ta"

MaimoonWhere stories live. Discover now