The Shadow 2

8.2K 642 11
                                    


Tunda muka shiga gida Amira take min bala'i. Ni dai kawai dariya nake mata. "Yanzu kinsan kuwa duk wanda ya ganki a motar Sultan irin kallon da zaiyi miki? Kin san ma kuwa waye Sultan? Mutumin nan ko magana bai kamata ace ta hada ku dashi ba ballantana har ki shiga motar sa. Yanzu ma tukunna, ina kukaje da kuka dade haka baku karaso ba?"

Na harare ta nace "Sannu Mommy. To gidan sa ya kaini. Ina ruwanki da inda muka je?"

Muka shiga dakin mamanta na gaisheta muka danyi hirar bikin Hafsat sannan muka koma dakin Amira. Nan fa ta saka ni a gaba da nasiha tana hadawa da ayoyin Alqur'ani da hadisai, ita lallai gani take shiga motar Sultan din da nayi tamkar wani katon zunubi na aikata. Tace "Yanzu Allah ne kadai yasan irin maganganun da ya gaya miki, duk sai yaje ya hure miki kunne anzo an kasa gane kanki. Ke kina ganin abin kamar wasa bayan ita halayya naso take yi kafin ki ankara kin fara biye masa. Ki rufa mana asiri Moon ki rabu da Sultan dinnan"

Na daga kafada kamar tun farko banji duk abinda take cewa ba nace "Saboda me? Saboda me zan rabu dashi?" Tace "saboda me? Yanzu har tambaya kike yi saboda me? Just look at him zaki gane saboda me. He is a criminal for God's sake. He is spoilt rotten no good human being. A gangster. A rogue. A drunk. Duk wadannan dalilan basu ishe ki ba?"

Murmushi kawai nake yi ina kallon yadda ta dage tana ta bayani. Nace "yanzu in tambayeki, ya akayi kika san Sultan is a drunk?" Tace "duk garinnan waye bai san dan giya bane? sau nawa ana ganinsa yana yawo a gari a buge, yara suyi masa ihu? Sau nawa ana kama shi da giyar ma gaba dayanta" nace "yanzu misali ke kin taba ganinsa yana shan giya? Ko kuma wani ne ya gani ya fada wa wani shima ya fada wa wata ita kuma ta fada miki?" Tace "ni ban taba ganin sa ba amma.. " na daga mata hannu nace "amma me? Annabi da kansa ya hana yaɗa jita jita, ita ake kira da shaidar zur, wato abinda baka tabbatar ba kuma kake gaya wa mutane musamman akan alfasha. Yanzu idan Sultan ya kaiki kara sai an daure ki saboda kinyi masa kazafi"

Amira ta saki baki tana kallona kamar zata yi kuka tace "are you truly depending him Moon?" Nace "ba wai goyon bayan Sultan nake yi ba, ina goyon bayan gaskiya ne" ta sake matsowa kusa dani ta dafa kafaduna desperately tace "yanzu ki duba kiga irin abokansa, ki kalli wannan shegen Amir din da suke yawo tare ki gani. Idan kana son ka san halayyar mutumto ka kalli mutanen da yake tareda su, haka Annabi yace. Kin san kuwa sunan gang dinsu? Gang Bang they call themselves. Gang din 'ya'yan manya ne wadanda suka fi karfin iyayensu suka kuma fi kargin hukuma. Abuja, Kano, Kaduna, Lagos da duk sauran manyan states na Nigeria an sansu, Sultan da Amir sune 'yan Abuja. Moon duk wanda yake cikin gang dinnan is a known criminal kawai dai dan babu yadda za'ayi dasu ne shi yasa. Kinsan kuwa kwanan baya suka yi gang raping wata yarinya a Nassarawa state?"

Ji nayi tamkar ta chaka min mashi a kirjina, amma na daure nace "ke a ina kikaji wannan labarin?" Ta daga kafada tace "a radio, a television, a social media, a newspaper ko ina zancen akeyi" nace "ita yarinyarce tace su su kayi raping dinta" tace "eh mana, anyi hira da ita har a gidan radio" na sake cewa "ita yarinyar ce tace da wane da wane da Sultan suka yi raping dinta?" Ta sake girgiza ni kamar mai son farkar da ni daga bacci Tace "just because his name wasn't mentioned doesn't mean he didn't do it"

Na girgiza kai na kawai ina kallonta, tace "Moon kar ki bari son da kika fara yi masa ya rufe miki ido ki kasa ganin gaskiya har kuma ki bari son yayi nisan da koda kin fahimci gaskiyar zaki danne ta. Dududu yaushe kika sanshi da har zaki tunanin kinsan shi fiye da sauran jama'a? Duk abinda nake gaya miki kamar yana shiga ta wannan kunnen ne yana fita ta wancan. Already har ya riga ya hure miki kunne"

Ta mike a ranta a bace ta dauko laptop dinta ta ajiye min agaba na tace "in baki yarda dani ba check for yourself, ki duba internet zaki fahimci waye Sultan" daga nan ta fice ta barni a dakin.

Na jima ina kallon laptop din ina jimamin abinda bincike na zai gano min. Can na dauka na kunna direct na shiga goggle, nayi typing sultan sai naga amsoshi da yawa wadanda ba sa dangantaka da abinda nake nema. Na goge nayi typing Sultan Abuja prince. Nan da nan kuwa naga an watso min hotunan Sultan, wadansu a kasarnan wasu a kasar waje. Duk hotunan babu ko guda daya da yake da manyan kaya a jikin sa, babu kuma ko guda daya da yake tare da babansa. Nayi typing criminal record dinsa, nan ma naga rubutu da hotuna da yawa, can ya daki wancan, nan yayi trashing wancan shagon, yayi causing traffic jam, duk dai labarin daya ne. Nayi shiru ina karanta labaran daya bayan daya, sai wani tunani yazo min, duk cikin labaran banji ance yayi sata ba, banji fashi da makami ba, banji kisan kai ba kuma banji labarin yarinyar ta Amira ta fada ba, asali ma duk hotu an nasa babu inda na ganshi da mace, duk tare da maza ne masu shiga irin tasa. Wani hotonsa ne ya dauki hankali na nayi zooming, Sultan ne fuskarsa dauke da murmushi, rike a hannunsa kwalbar giya ce ya daga ta alamar cheers. Na runtse idona ina jin zafi a kirjina. So it's true, yana shan giya.

MaimoonWhere stories live. Discover now