The New Bride

9.9K 746 5
                                    

Ya rike fuskata a hannunsa yana kallon cikin idona yace "kinsan dai da rayuwa da mutuwa duk na Allah ne ko? Kinsan babu wanda ya isa ya raya wani idan har Allah ya rubuta cewa kwanansa ya kare ko? Kuma kinsan babu wanda ya isa ya kashe wani in har kwanansa bai kare ba ko? Iyaye, 'yan uwa, miji ko mata, 'ya'ya dukka Allah ne yake bamu su kuma shi yake karbar su a lokacin da yaga ya dace. Duk lokacin da muka rasa wani abinda ya kamata muyi shine mu gode wa Allah daya bamu su tun farko, har muka rayu dasu muka ji dadinsu suma suka ji namu, dan daga mu harsu na Allah ne. Idan mutum ya riga ya mutu babban abinda yake bukata daga gare mu shine addu'ah, mu nema masa rahamar ubangiji tare damu baki daya, mu kuma yi fatan Allah ya sada mu dashi a aljannah inda zamuyi rayuwa ta har abada ba tare da tsufa ko mutuwa ba. Maimunatu Allah yayi wa Baffa rasuwa jiya da daddare, yau da safe akayi jana'izarsa aka kaishi gidansa na gaskiya."

Wani sabon kuka ne ya taso min, yayi sauri ya hade bakinsa da nawa, sai da yaji na tsayar da kukan sannan ya sake ni, na ture shi da sauri na fara kokarin mike wa, ina jin kaina yana juyawa, wayyo Allah Baffa na, wai Baffa ya tafi ya bar mu shikenan ba zamu sake ganin sa ba? Na runtse idona ina hango kyakykyawar fuskarsa ta fulani mai cike da kwarjini da fara'a, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Sultan naji ya sake rike ni yana kokarin zaunar dani "Moon zaki fadi fa, menene hakan wai? Shi yasa tunda aka kaishi asibiti aka ce kar a gaya miki saboda an san halinki"

Na juyo da sauri ina kallonsa bibbiyu, nace "asibiti? Au dama bashi da lafiya amma baka gaya min ba? Daya mutum ma har sai da aka binne shi sannan za'a gaya min" ya sake kokarin rike ni na ture shi, yace "to inda an gaya mikin ma menene zaki yi masa? Za ki cire masa ciwon ne ko kuma zaki hana shi mutuwa?"

Da karfi nace "I could have been there for him, I could have hold his hands and say goodbye to him" yace "and what difference will that make?" Nace cikin fada "It would have made me feel better".

Na rufe fuskata da hannayena na fara kuka a hankali mai shiga zuciya. Duniya kenan, ina nan ina enjoying rayuwata ashe Baffa yana can yana sallama da duniyar gabaki daya. Sultan ya zo ya durkusa a gaba na, har yanzu swimsuit din jikinsa a jike take yace "ya salam, Moon da kinsan yadda nake jin kukan ki a raina da kin daina, da ina da dama da ba zaki taba kuka a rayuwar ki ba, amma ba zan iya dawo miki da Baffa ba, dan Allah ki tausaya min ki daina kukan nan haka"

Ni haushi ma naji yana bani, daga shi har sauran 'yan gidan mu duk haushi suke bani, tunda duk muna waya dasu kuma duk sun san Baffa yana asibiti amma babu wanda ya gaya min. Ya dora hannunsa akan cinya ta na ture hannun na juya baya na na cigaba da kuka na.

Ina jin shi ya mike ya shiga toilet, naji alamar shower sai kuma ya fito ya shirya, har lokacin ina zaune ina kuka na, yazo ya zauna kusa dani, na matsa. Yace "am sorry Love, nasan bashi da lafiya amma kinga yanayin da kike ciki, ga problem din bp dinki, wannan yasa aka ce kar wanda ya gaya miki, babu wanda yasan mutuwa zaiyi saboda babu wanda yasan gawar fari sai Allah. Am sorry" yayi kokarin juyo dani in kalle shi amma naki yarda, ya rabu dani yace "zan je airport yanzu in gani ko da akwai flight zuwa Nigeria yau ko gobe. Please dan Allah promise me you will stop crying" ya zagayo ta side din da fuska ta take, ya saka hannu ya bude fuskata dana rufe da hannuna, fuskarsa tayi abin tausayi, ya goge min hawayen fuskata.

Yace "kinji abinda na gaya miki? Ina so inje in samo mana tickets amma bana son in barki kina kuka kuma, please ki daina sai in tafi. In baki daina ba kinga ba zanje in sama mana flight ba ballantana mu tafi Nigeria"

Na goge fuskata ina kallonsa nace "na daina to" yace "promise" nace "I promise" sai da yaga na tsaida hawayena sannan ya fita, yana fita na hau kan gado na kwanta na cigaba da kuka na.

Wajan karfe daya ya dawo, inajin shigowarsa na rufe idona kamar  bacci nake yi. Ya dan jima a tsaye yana kallona sannan ya hawo gadon ya dan taba jikina, yace "my God, kukan ki ka cigaba kenan ko? Bayan kinyi min alkawarin ba zakiyi ba" bance masa komai ba, naji ya sauka daga kan gadon, na bude idona ina kallonsa naga ya dauko first aid box din mu ya dauko min magunguna na, ya dauko bottle water ya bude ya hawo gadon ya mikar dani zaune ya bani nasha.

MaimoonWhere stories live. Discover now